Chapter 52
Chapter 52
fito da ita, idanunta a lumshe duk jikinta yayi yaushi ko hannunta bata iya d'agawa. Rigan bacci ya saka mata mara nauyi yanata mata sannu. Yana gama shiryata ya kwantar da ita ta koma chan gefe ta k'udundune waje d'aya. Wutan d'akin ya kashe ya cire jallabiyan jikinsa ya haura kan gadon, janyota yayi jikinsa tako lefe. K'anshin turaren jikinsa ne ya daki hancinta tad'an turesa a hankali ta matsa gefe "Sannu Wife!" Shiru batace komai ba sai sheshek'an kukanta dayake ta jiyowa daga gefensa "I'm so sorry, gobe sai muje Hospital da safe koh" Wani amai ne ya sake taso mata ta mik'e dasauri tana ganin jiri, side lamp ya kunna ya mik'e yabi bayanta, bakin k'ofan bayin ta durk'ushe tana ta amai wanda yake zallan ruwa dan ba komai cikinta. Gaba d'aya jikinta rawa yake tana aman tana kuka, tsugunnawa yayi bayanta ya rik'eta shima yana hawaye harta gama. Haka suka kwana babu wanda ya runtsa cikinsu. Tausayinta ne ya cika Jamal, ji yayi dama ciwon ya dawo jikinsa ta huta. Ana fitowa sallahn asubah ya dawo, lokacin tasamu bacci yad'an d'auketa. Bai tasheta ba ya zauna kusada ita yana kallan kyakkyawan fuskanta, daga nan shima baccin ya d'aukesa daga zaune. Kakarin amanta ne ya tashesa, a rud'e ya mik'e ya shiga bayin ya sameta durk'ushe tana kuka. D'aukanta yayi ya k'arasa da ita cikin bayin ya mata wanka ya fito da ita. Kaya ya chanza mata ya saka mata hijab ya sake d'aukota suka sauko k'asa. Lafewa tayi a jikinsa dan bata jin k'arfi ko kad'an. A falon Mabrookah suka had'u da Aunty Faty da itama Mabrookahn, ko kallansu baiyi ba balle susa ran zai ce musu wani abu. Shi gaba d'aya hankalinshi nakan Wife d'insa, mota ya sakata ya tada suka bar gidan. ABUTH ya nufa kai tsaye, suna zuwa aka amsheta tare da bata taimakon gaggawa. Yana nan tsaye bakin k'ofan d'akin sai safa da marwa yake, chan likitan ya fito, Jamal yayi saurin taransa yana tambayansa halin datake ciki. Kafad'ansa likitan yad'an bubbuga, "She wl be alryt, dont uh worry" Ya mik'a masa wani takarda "Tests d'in da za'a mata yanzu ne" Amsa yayi ya masa godiya, likitan yace zai iya shiga ya ganta. Da saurinsa ya shiga ya sameta kwance kan gadon marasa lafiya, da drip a hannunta. Kurri ya mata ko k'iftawa bayayi, tsakanin Jiya zuwa yau har tayi rama sai wani fari data k'ara da k'irjinta da suka ciciko. Ajiyar zuciya ya sauke ya k'arasa ya mata kiss ya mata a goshi ya d'ago yana kallan fuskanta "Speedy recovery Swthrt" Kud'in test d'in yaje ya biya ya dawo, da kansu sukazo suka d'iba jininta suka kuma basa wani roba idan ta tashi tayi fitsari a ciki. Amsa yayi suka fita. Bata wani dad'e dayin baccin ba ta farka, sai lokacin ya tuna ko breakfast basuyi bah, Mifzal ya kira dan baiso Mami ta sani hankalinta ya tashi, ba dad'ewa sai gashi da kayan tea da sauran abubuwan da za'ayi anfani dasu. Yana gaisheta ya koma dan yanada wani case dayake handling.. Taimaka mata yayi ta shiga toilet tayi fitsari a roban, tea ya had'a mata mai kauri tayi saurin kauda kai tana yatsine fuska "Pls Swthrt kisha, i know kina jin yunwa" Sake kauda kai tayi tana yatsine fuska "Banaso!! Amai zanyi" "No bazakiyi bah, daure kisha kinji Wife" Dakyar ya lallamata tasha kad'an ta kauda fuska. Nan da nan Amai ya taso mata ya tara mata abu tayi tanata maida numfashi yana mata sannu. Sai wajan rana sannan result ya fito, Dr Amina ce ta musu Albishir da cewa tana d'auke da juna biyu na wata biyu. Murna wajan Jamal ba'a magana, ji yayi kamar ya maida Ummyn ciki saboda farinciki. Zama yayi kusada ita ya d'ago kanta tareda rik'e hannuwanta yana murmushi "Kin biyani Wife, kinmin komai a rayuwa. I love uh so much" Kuka ya fashe dashi ta d'ago dasauri tana kallansa "I wish Dad was here, da shi zan fara fad'ama wah" Ya rungumota jikinsa yana cigaba da kukan, hannu tasa cikin suman kanshi tana yamutsawa cikin salo. Saida yayi mai isarsa sannan bacci ya d'aukesa a jikinta. Kallansa take cike da tausaya wa, har mamakin irin shak'uwan dake tsakaninsa da Abban take. A ranar aka sallamesu da yanma bayan an rubuta mata magungunan da zata rink'a sha. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* IWA (Onward Together) Dedicated to My *Late Siblings* Page 60 n 61 A ranar aka sallamesu da yanma bayan an rubuta mata magungunan da zata rink'a sha. A haraban gidan yayi parking ya fito dasauri ya bud'e mata k'ofa ta fito. Hannunta ya rik'e "Ko na d'aukeki neh Wife" Ta girgiza kai alamar A'a, tana turo baki. Hannunta ya kama suka shiga ciki har zuwa d'akinsa. Kan gado ya kwantar da ita yana mata sannu ya fita ya moma ya kwaso kayan da suka dawo dasu ya shigo. Har tsawon kwana biyun kwanan ta kula yake bata na musamman, har lokacin bata daina Aman bah. Sosai take galabaita idan tayi aman, tun Mabrookah bata gane ba har ta gane. Ranar da kuka ta shiga side d'in Mami ta fad'a jikin Aunty Faty tana cigaba da kuka "Mummy Ummy ciki gareta" Mami dake gefe ta dafe k'irji tace "Ciki!" Fargaba ne sosai a fuskan Aunty Faty, ta d'ago Mabrookah tana zare idanu "Ke Mabrookah bansan wasa, kin tabbatar da abinda kike fad'a?" Cikin kuka tace "Ciki ne kullum batada lafiya kuma tana amai, hanzu kuma na gama jin yana waya da doctor" Hankalin Aunty Faty da Mami ya tashi sosai, Mami tace "Harga Allah banasan d'ana ya samu zuri'a da yarinyan nan. Bana santa ko kad'an a raina" Shiru Aunty Faty tayi tana sak'e sak'e a ranta, Mabrookah ko kuka ta cigaba kamar Aunty Fatyn ce ta mutu. Bayan sallan Magrib, Jamal na rungume da Ummy yana mata sannu bayan ta gama amai, kuka take sosai tana jujuya fuska a k'irjinshi. Sannu ya cigaba da mata hankalinsa a tashe. "Sannu Wife, fad'amin meh kikeso na miki kiji dad'i" Idanunsa taf da hawaye na tausayinta, cikin shagwab'a tace "Ni ka kaini gida wajan Mama" Jim yayi sannan ya d'agata da kansa ya shiryata, ya saka mata hijab tareda rik'o hannunta suka fito. Side d'in Mami suka shiga, a falo suka sameta zaune itada Aunty Faty, duk da yanda yake jin jikinta hakan bai hanata durk'usawa har k'asa ta gaidasu bah. Mami ce kawai ta amsa itama d'in a dak'ile. Jamal dake kan kujera d'are d'are yace "Mami zamu d'an fita neh, anma ba dad'ewa zamuyi bah" Hararansa tayi sannan tace "Adawo lafiya" Bako kunya ya mik'e ya rik'e hannun Ummy tana ta k'okarin k'wacewa yak'i har suka bar falon. Bud'e mata gaban mota yayi ta shiga sannan shima ya shiga suka bar gidan. Pz ya tsaya yayi siyaiyan Fruits dayawa ya dawo motan suka d'au hanya. A k'ofar gidan yayi parking ta fito dasauri ta shiga ciki. Ya bita da ido yana murmushi tare da girgiza kai. Fruits d'in ya d'auka ya bita cikin gidan. Ko sallama batayi ba ta shiga cikin falon tareda fad'awa jikin Mama ta fashe da kuka. A rud'e ta d'agota "Lapia Ummy, meya faru?" Sallaman Jamal
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82