Chapter 56
Chapter 56
hak'uri, duk abinda zaki kira matata zan jure anma banda ita" Ta mik'e fuuuu yabar falon ya barsu tsaye kamar an dasasu dukansu baki bud'e. Yana fita yabi Ummyn d'akinta, kan gado ya sameta kwance tana kuka a hankali. Janyota yayi jikinsa "I'm very sorry wife, ki k'ara hak'uri kinji. Wata rana sai labari" Kwacewa take k'okarin yi tana cigaba da kuka "Ni na gaji ka kaini gidanmu, bazan zauna bah" Dukansa ta somayi a k'irji, yayi saurin had'a bakinsu waje d'aya. Daina mutsu mutsun tayi cikin 'yan mintina ya rabata da kayan jikinta, ina ganin haka nayo waje na basu waje. Soyaiya sosai Jamal ya nunama Wife d'insa a ranar, ita kanta ta k'ara tabbatar da Jamal mai k'aunarta neh. Yinin ranar suna mak'ale da juna. Bai fita ba sai bayan la'asar. Suna ganin ya fita Aunty Faty ta shigo ta mata kacha kacha harda Mari. Kuka kam Ummy tayi har ta gode Allah. Koda ya dawo tambayan duniya babu wanda bai mata bah anma amsar d'aya cr bakomai. Ranar kwanan zazzab'i tayi sai kuka take jikinsa shiko yana aikin lallashi. Washe gari da wuri ta tashi dan zazzab'in ya saketa, breakfast ta had'a masa mai rai da lafiya sannan tayi wanka ta shirya cikin Uniform d'in makaranta. Tana gama shiri ya farka yana binta da kallo "Wife" Ya kira sunanta ahankali, ta juyo tana kallansa da murmushi. Bud'e mata hannu yayi alamar tazo gareshi, dagudu ta k'arasa ta fad'a jikinsa ya rungumeta sosai kamar za'a kwace masa ita "Wife keda bakida lafiya wani school zaki kuma" Baki ta turo gaba "Yau fa zamu fara exams kuma banasan nayi missing" Yakai mata light kiss a lips d'inta "Nidai da kin hak'ura kawai, banaso kije ki wahala ki kuma wahalar min da baby" Turo baki tayi gama ta tureshi ta mik'e dasauri ta fita, wanka yayi ya fito ya sameta kan dinning, kamar kullum tare sukayi breakfast ya bata taci sosai sannan ta mik'e tana duba agogon hannunta "Nayi latti" Ta sak'ala jakan makarantar ta "Pls Wife karkije, kinga fa baki da lafiya" Kukan shagwab'a ta soma tana doka k'afanta a k'asa, dasauri ya mik'e ya rik'eta "To naji a dawo lafiya kinji" Kiss tamasa a baki ta sauka dasauri tana dariya, da murmushi ya dunga binta da kallo harta fita. Side d'in Mami ta shiga dan ta gaishe su, yauma kamar kullun zageta tas Aunty Faty tayi ta fito a sanyaye ta shiga mota driver yaja suka bar gidan. Duk kewan Ummyn ne ya cika ransa, komawa d'akinsa yayi ya shirya ya fito, baiko lek'a side d'in Mami ba ya shiga motarsa ya fita. Tafiya yake yana keta layukan cikin anguwan, daga nesa ya hango taron jama'a an kashe hanyar fita unguwan, waje ya samu yayi parking ya k'arasawa wajan, ganin motan gidansu yasa gabanshi ya fad'i. Kukkutsawa yayi ya shiga cikin wajan sosai, driver ya gani kwance kansa na fitar da jini, ga Hijab d'in Ummy a k'asa da warin takalminta d'aya. Wani k'ara ya saki da k'arfi ya k'arasa inda Drivern ke kwance. Yana ganinsa cikin k'arfin Hali yace "Ummm.....Umm...Ummy su..sun d'auketa" *Ina Jiran Comment* Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 66 n 67 "Ummm.....Umm...Ummy su..sun d'auketa" Wani irin kuka ya saki, baisan sanda ya kamo kwalan Drivern ba yana jijigashi cikin kuka yace "Ina suka kai min Ummy, waye ya d'auketa" Sumewa Drivern yayi dan ba k'aramin jini ke fita daga kansa bah. Jiniyan 'yansanda ne ya cika wajan, mutanen dake zagaye da wajan suka bud'a hanya 'yan sandan suka k'arasa wajan motan. Har lokacin Jamal na durk'ushe a wajan yana kuka sosai kamar k'aramin yaro. Ambulance ne suka d'au driver, wasu daga cikin yan sandan suka dunga d'aukan motan hoto harda Jamal d'in. Dakyar aka samu ya tashi daga wajan ya shiga motan 'yansandan har lokacin yana kuka hannayensa biyu akai. ```Waiwaye``` Ummy na shiga mota driver yaja suka bar gidan, hawaye ta soma na tausayin rayuwarta a gidan aure. Sunyi tafiya mai nisa dan daga gidan zuwa bakin anguwan akwai tazara, basu ankara ba wata bak'ar jeep tasha gabansu, ba shiri driver yaja burki ya tsaya yana salati. Ummy ko k'walalo ido tayi tana kallan motan gabanta na fad'uwa, wasu mutane ne suka fito ciki, ba shiri ta saki k'ara dan ko tantama babu sune wad'anda suka kashe Abba. Numfashinta ne ya soma barazanar d'aukewa, suka bud'e motan wajan su hud'u dukansu da k'aton bindiga a hannunsu. Ba shiri ta fashe da kuka tana kallansu tare da girgiza kai, d'aya daga cikinsu ya daka ma driver tsawa "Kai! Fito daga motan nan" Ba musu ya fito ko ina na jikinsa na rawa ya d'aga hannu sama, d'aya ya bud'e k'ofan baya inda Ummyn ke ciki ta sake sakin k'ara tana kuka. Fincikota yayi daga cikin motan har saida Hijabinta ya cire, ta soma turjewa tana cigaba da kuka kamar ranta zai fita. Mutanen anguwa na lallab'e suna hango abinda ke faruwa saidai ba halin kawo d'auki saboda manya manyan bindigogin dake hannunsu. Ganin tana neman b'ata musu lokaci yasa suka saka mata wani hankercief a hanci, ba b'ata lokaci ta tafi luuuu xata fad'i daya daga cikinsu ya d'auketa ya sakata a motan. Driver ya d'aura hannu aka ya matso tareda rik'e rigan d'aya daga cikinsu "Ina zaku kaita, dan Allah k.." Saukan kan bindigan dayaji a kansa ne ya hanasa k'arasa maganan dayake, so biyu mutumin na buga masa kan bindigan sannan ya wurgar dashi ya shiga mota suka bar wajan da wani matsiyacin gudu. Tafiya kawai suke da gudu bako birki, har suka soma barin garin zaria. **** Har suka isa Police station Jamal bai daina kuka bah, saima k'ara sautin kukan dayake kamar ana zugashi. Duk yanda 'yan sandan sukaso ya musu k'arin bayani kasawa yayi sai neman guri dayayi ya zauna a k'asa. Haka suka kyallesa dan ya samu zuciyarsa ta sarara. Saida yayi mai isarsa sannan ya d'auko wayansa a aljihu ya soma neman layin Mifzal Bugu d'aya ya d'auka, cikin wani irin murya yace "Ya d'aukemin Ummyna, Ya d'aukemin ita" A razane Mifzal yace "Bangane ba, waya d'auketa." "Anyi kidnapping Ummy da safen nan, pls Mifzal ka taimakeni, ciki ne da ita and ba lafiya gareta bah. Karsu cutarmin da ita pls" Ya sake rushewa da wani kuka, "Kana ina neh" "Ina police station" Dakyar ya masa kwatancen police station d'in dayake. Ganin zaman wajan bazai fishe shi ba yasa ya mik'e dakyar ya fita ya tari adaidaita sahu yahau. A k'ofar gate ya sauka ya biya mai napeep d'in, kallo d'aya zaka masa ka gane hankalinsa a tashe yake matuk'a. Kai tsaye side d'in Mami ya shiga, a falon k'asa ya sameta itada Aunty Faty suna hira. Wani kuka ne ya kub'uce masa suka d'ago a firgice suna kallansa. Jikin Mami ya fad'a ya sake fashewa da kuka, Hankalinta ne ya tashi ta d'ago kansa a rude "Meke Faruwa Jamal! meya sameka" Itama Aunty Faty ta sauko duk hankalinsu a tashe, Mami ta girgizasa idanunta cike da kwalla "Jamal yimin magana mana, meke faruwa" Dakyar cikin kuka yace "Anyi kidnapping Ummy" "What!" Mami ta fad'a da k'arfi tana kallansa Aunty Faty tace "Ba d'azu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82