Chapter 2
Chapter 2
Hrt ki rink'a b'oyemin damuwarki, babu wanda zak'i fad'ama damuwarki duk duniya daga Baba da Mama sai ni. Duk inda nake ko me nake sai nayi tunaninki, ina sanki Ummy bazan iya rayuwa baki bah, a duk sanda kike cikin damuwa ina ganewa saboda tsananin damuwa da nakeyi dake" Hawaye ne suka cik'a mata ido, tabbas abinda Ya Bilal ya fad'a gaskiya ne akan irin sanda yake mata, anma dole ta rink'a b'oye mata damuwan da suke ciki saboda shima ya rink'a hutawa da d'awainiyarsu. Magananshi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi "Hrt fad'amin meke damunki?" Murmushi tayi tana kallanshi "Babu komai Ya Bilal" D'an dutsen dake kusada ita yaja ya zauna ya kafeta da idanunshi "Ashe har akwai ranan da zaki b'oyemin damuwanki Hrt, nayi tunanin a iya zaman mu da soyaiyar dake tsakanin mu da kuma shak'uwa ba abinda zamu b'oyema juna. Ina sanki Ummy kuma bazan fasa fad'a miki zan iya yin komai akan sanda nake miki bah" Kuka ke k'okarin kufce mata anma ta shanye ta dake tana cewa "Ya Bilal ba abinda zance maka saidai Allah ya saka da alheri ya baka lada, ya kuma saka a aljanna. Kayi mana komai nida Iyayena wanda y'an uwanmu basu mana bah. Bansan dame zan saka maka ba Ya Bilal, Ina so n.. " Saurin k'atseta yayi ta hanyar d'aga mata hannu "Ya isa Hrt, bana buk'atar godiyanki. Damuwarki kawai nake san ji" "Ya Bilal yanzu fa ka dawo daga aiki ko gida bakaje bah" Kallanta yayi tareda marairaice fuska "Hrt pls mana fad'amin, bana iya jure ganinki haka" K'arya tamai da cewa kanta ke ciwo, duk da bai yarda ba anma ya bita a hakan dan yaga bataso s fad'amai. Wani yaro ne yazo siyan awaran da kanshi ya iriga ya bashi Ummy nata kallanshi da murmushi, wani sanshi da tausayinshi ne ke k'ara shiga zuciyarta. Mik'ewa yayi yasa hannu a aljihu ya ciro d'ari biyar ya mik'a mata "Hrt ki rik'e wannan idan kuna buk'atar wani abu" Duk da suna da buk'atar kudin anma tayi saurin girgiza kai "Aa bama buk'atar komai" Hannunta ya rik'e ya chusa mata kud'in a tafin hannunta yana kallan fusanta "Hrt bana san musu pls, anjima zanzo muje chemist" Bai jira mai zatace ba yabar wajan ya shiga gida. Binshi tayi da kallo harya shiga gida sannan ta sauke ajiyan zuciya ta cigaba da suyanta. Cikin ikon Allah ta saida waran da wuri ta shiga da kayan gida. Mama ta samu tsakar gida tana hura wuta "Sannu da aiki Mama" "Yauwa sannu Ummy har kin gama?" "Eh Mama ya jikin Baba" "Dasauk'i kinga ma wuta zan hura na d'aura mai ruwan wanka" Kayan ta aje ta amshi aikin a hannun Maman, hura wutan tayi ta d'aura ruwan sannan ta lek'a ta gaida Baban. Albarka ya soma sa mata harda hawaye dan yana matuk'ar tausaya ma Iyalin nashi. Kud'inda Bilal ya bata ta nunama Baba yana gani ya fashe da kuka, Itama Ummyn kukan ta soma tana rarrashin Baban "Allah ya sakama yaron nan da Alheri" Mama dake bakin kofa ta amsa da Ameen. "Ku cigaba da hak'uri Ummy, komai yayi farko zaiyi k'arshe, jarabta ce haka Allah yaso, ku cigaba da min Addua" Mama itama ta fashe da kuka "Allah ya baka lapia Mallan, insha Allahu zaka warke ka cigaba da walwalanka yanda kake da" Ummy ta mik'e ta fita daga d'akin, hijabinta tasa ta fita tayo musu chefanen d'an abinda zasu ci abinci ta dawo gida. Tana shiga ta tarar da Ya Bilal zaune a tsakar gida shida Mama suna hira.. Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to my *Late Siblings* *Page 3* Tana shiga ta tarar da Ya Bilal zaune a tsakar gida shida Mama suna Hira, a suk'wane ta karaso tareda sallama, suka amsa mata ta gaidasu kanta a k'asa, Bilal sai binta da kallo yake, shige da fice ta soma dan d'aura musu abinda zasu ci, tana cikin jajjage taji Bilal na cewa "Mama ki tayani da Addu'a, Ogana ya kirani d'azu yake sheda min gobe zamuje wani aiki a binnin taraiya Abuja, Ginin gidan wani babban d'an siyasa kuma insha Allahu zamu samu alheri sosai" "Aa ina tayaka murna d'an albarka, Allah ya bada sa'a yasa aje lapia a dawo lapia" Ameen yace yana murmushi tareda maida dubanshi ga Ummy wacce tun sanda ya soma maganan ta saki tab'aryan dake hannunta gabanta na fad'uwa, had'a ido sukayi ta soma kuka mara sauti, dasauri tabar wajan dan kada Mama ta gani ta shige kicin tana kuka a hankali. Anya zata iya wuni guda batare da tasa Ya Bilal d'inta a ido bah, balle kuma wannan tafiya da take tunanin zai d'au lokaci, tanaji sukai sallama yabar gidan. A haka ta gama aikinta sukuku ta koma d'aki tayi sallan magrib, tana nan kan sallayan tayi tagumi Mama ta kwalla mata kira daga tsakar gida, dasauri ta fita ta samu Yaro a tsakar gidan "Wai ana sallama dake" Tad'an kalli yaron da mamaki "Wanene" "Wai Bilal" Mama tayi saurin cewa "Kace tana zuwa" Yaron na fita Mama tace "Kije kid'an murza hoda" Bah musu ta juya tashiga d'aki tad'an gogo hoda ta fito ta nufi wajan, tsaye ta sameshi ya jingina da bango yana game a y'ar k'aramar android d'inshi Turo baki tayi kamar zatayi kuka sanan tace "Sannu" Murmushi yayi mai sauti har lokacin idanunshi nakan candy crush d'in daya keyi "Hrt fushin menene" Ai kaman jira take tako fashe da kuka, ya sa wayan a aljihu yana kallanta da damuwa "Hrt kiyi hak'uri kinsan banasan damuwanki, nasan akan maganan tafiyata ne indai bakiso saina fasa" Share hawayenta tayi da bayan hannu tana girgixa mai kai "Aa karka fasa Ya Bilal, kawai dai xanyi kewanka neh, ka sabamin da ganinka kullum kuma gashi zakai nisa dani" Sosai yaji dad'in magananta har saida yayi murmushi "Hrt inaji a jikina wannan tafiyan da zanyi alheri ne, shi zai kawo sauyi a rayuwarmu insha Allahu, babban burina naga kinyi karatu Hrt mai zurfi keda Bahar, inaso naga na samu ayima Baba aiki a idanunsa ya rink'a gani.. Ki daina kuka ki rinka min addu'a kinji" Kai ta gyad'a wani sabon kuka tazo mata "Oh Hrt banasan kukanki, pls ki daina kinji bazan dad'eba just sati biyu zamuyi" Ganin kukanta nasan karya mai k'warin guiwa yasa tayi shiru sai ajiyan zuciya da takeyi "Allah tsareka ya sa kuje lafiya ku dawo lapia" Ameen yace yana murmushi, yasa hannu a aljihu ya ciro wasu kud'i ya mik'a mata "Kuyi managing wannan kafin na dawo kinji" Kallan kud'in take kuka na k'okarin kufce mata, dakyar tasa hannu ta karba tad'an duk'a kad'an tayi godiya. Kallanta kawai yake wani santa mai tsafta na kara shigan shi, ji yake zai iya yin koma menene akanta.. "Ki shiga ciki Hrt dare yayi and kuma akwai sanyi" Godiya ta kara mai sannan tamai addu'oi sosai ta juya zata shiga gida "Hrt" Ya kirata tad'an juyo tana kallanshi, hannu ya k'arasawa a aljuhun shi ya ciro wani zobe mai kyau na azurfa "Kawo hannunki" K'in mik'a hannunta tayi ta kafeshi da ido, yad'anyi murmushi "Oh Come on bani hannun" Bah musu ta mik'a mai hannunta yasa mata zoben yana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82