Skip to content

Chapter 1

Chapter 1

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,192 words 0 views Progress saved
Download Book

Compiled by Umar Dalha. ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Bismillahir Rahmanir Rahim *Page 1* Mallan Adamu haifafen garin Zaria neh, yana zaune a Unguwar Iya dake cikin zaria city, Yana zaune da matarsa Amina da y'arsu guda d'aya mai suna Jaleelah anma ana ce mata Ummy saboda sunan Mahaifiyar mallan Adamu ne... Jaleelah yarinya ce y'ar shekara goma sha takwas, tanada Ilimin addini daidai misali, Na boko ne bata samu ba dan a primary five ta tsaya kasancewar Mahaifinta baida hali, ga kuma chuta ta Makanta data sameshi lokaci guda.. Hakan ne yasa Ummy da Mama suka kasance cikin wani hali har takai Ummyn ta koma Suyan wara kofar gida dan su samu abin rufawa juna asiri. Ummy yarinya ce Mai tarbiya gata kyakyawa ga diri hakan ne yasa samari ke b'ulb'ulowa tako ina suna santa saida yawancin su da maganan banza suke zuwa hakan ne yasa bata kulasu. Saurayinta d'aya mak'ocin su Sunanshi Bilal, yana matuk'ar tausayama halinda su Ummy suke ciki duk da shima ba wani k'arfi gareshi ba, lebura neh so dayawa yakan sayo d'an kayan abinci daidai gwargwado ya kawo gidansu Ummy, hakan ba b'aramin d'adi yakema Mahaifanta bah. Yau tana shara a tsakar gida ta jiyo tarin Baba gashi Mama ta fita taje mak'ota barka, tsintsiya ta aje dasauri ta k'arkad'e hannunta a jikin k'od'adiyar zanin atamfan dake jikinta, kwance ta sameshi yana tari sosai, idanunshi sun jujuya, tsugunnawa tayu gabanshi ta fashe da kuka "Sannu Baba, Sannu Allah ya baka lapia" Tarin yake ba k'ak'autawa, Kuka take duk ta rud'e dama ita abu kad'an kesata kuka, fitowa daga d'akin tayi dasauri ta ja hijabinta dake igiya tayi waje, a xauren gidan ta had'u da Mama tana ganinta ta k'ara fashewa da sabon kuka "Mama jikin Baba ya tashi" Ai ba shiri Mama ta shiga gidan hankali tashe, d'akin ta shiga ta tarar dashi kwance sai aman jini yakeyi, nan da nan Mama ta fashe da kuka tana tsugunne gabanshi, Ummy ta shigo d'akin dasauri idanunta cikeda kwalla "Mama mu kaishi Asibiti" D'agowa Maman tayi hawaye na bin idanunta "Da wani kud'i zamu kaishi Asibiti Ummy?, kinsan bamuda kud'i" Fita tayi da gudu kamar tab'abba ta fita kofar gida tana waige waige, kuka takeyi sosai lokaci guda tana Addu'a, daky'ar ta samu me napep ta tareshi tace "Mahaifina ne baida lapia dan Allag badan niba ka taimaka min mu fito dashi" Bah musu ya fito daga napeep din suka shiga gidan, har lokacin Mama na zaune gaban Baba tana kuka, ganin Ummy ta shigo da wani yasa ta d'ago dasauri "Mama mu kamashi akaishi Asibiti" Bah musu suka kamashi suka fito dashi, komawa Ummyn tayi ta shiga d'akinta ta d'auko wani k'ullin bak'in leda a hankali ta kwance ledan, kud'i ne yan dari biyar ta rungume kud'in tareda fashewa da kuka, kuka take sosai tana cewa "Kayi hak'uri ya Bilal zanyi anfani da kud'inka" Ta maida kud'in ta kulle ta fito daga gidan dasauri, Asibitin Gambo sawaba suka nufa, suna lsa ta biya mai keke napeep nurses sukayi Emergency dashi, Suna nan tsatsaye wata nurse ta fito tana rik'e da wani paper a hannu "Ku kuka kawo wannan patient din koh" Mama ta matso "Eh mune" Papern ta mik'a mata tana cewa "Magunguna ne da zaku siya, sai kuma zaku biya kud'in gado" Dam! Gaban Mama ya fad'i dan ko sisi bata fido daashi bah, papern tasa hannu ta k'arba, Ummy ta karaso wajan ta karb'i papern a hannun Mama "Na magani neh" Gyada kai Mama tayi dan tama kasa magana "Barinje in amso" Tana juyawa Mama ta k'wala mata kira ta juyo dasauri tareda Amsawa, k'arasowa inda take Mama tayi tana kallan cikin idonta "Ummy ina kika samu kud'i da kike cewa zakije ki siyo" Inda inda ta soma idanunta cikeda kwalla, Mama ta daka mata tsawa "Bah dake nake magana bah" Fashewa da kuka Ummy tayi jikinta ya soma rawa "Wallahi Mama bah abinda kike tunani baneh, Wallahi Ya Bilal ne ya bani ajiyan kud'in" "Saboda kuma bakida hankali shine kika d'au kudin zakiyi anfani dashi" Kamin tayi Magana Sukajiyo Muryan Bilal din daga bayansu yana cewa "Mama yanzu nake zuwa gida Ilyasu mai faci yake cemin kuna asibiti" K'irk'iro murmushi tayi "Wallahi jikin Mallan d'in neh ya tashi" Tunda Ummy taji muryanshi kanta ke k'asa, kallanta yayi ya saki Murmushi, Baice mata komai bah ya janye papern dake hannunta yana dubawa Ya d'ago ya kalleta lokacin Mama ta bar wajan ta koma gefe "Hrt ya jikin Baban" K'anta a k'asa tace "Dasauk'i basu dai bari mun ganshi bah" Lalluba aljihunshi yayi fuskanshi da alamar damuwa, muje muji nawane kud'in maganin. A tare suka jera har zuwa pharmacyn, lissafi aka musu harda kud'in gado dubu goma sha biyar, wani miyau Ummy ta had'iye dakyar tana kallan mutumin, d'agowa tayi ta kalli Bilal din murya chan k'asa tace "Ya Bilal mu d'auki Baban kawai mu koma gida" Girgiza mata kai yayi dasauri yace "Aa Hrt, ko zamu koma gida ne kid'auko kud'in nan" A kunyace tace "Ga kud'in nan" Mik'amai tayi kanta a k'asa, amsa yayi ya irgo dubu goma sha biyar ya biya ya rage dubu biyu, suna dawowa suka samu ana chanza mai d'aki zuwa ward. A Tare suka shiga d'akin, Mama ta mai godiya sosai ganin an sayo maganin da duk abinda ake buk'ata, Itama Ummyn tamai godiya shidai baice komai bah sai Murmushi kawai dayake. Bilal kyakyawan saurayi ne d'an shekara Ashirin da biyar, Bak'i ne shi anma ba wulik ba, yana yanayi da Black americans, Yanada tsayi da fafad'ar kirji, idanunshi dara dara masu kyawun gaske. Mahaifinshi d'an Asalin Garin Yola neh, su biyu iyayenshi suka haifa shida k'aninshi Bahar, Mahaifinsu ya rasu tun yanada shekara Ashirin, Yanzu suna tareda Mahaifiyarsu ne. Mak'ota ne dasu Ummy tun tasowanta Allah ya d'aura mai santa da kuma tausayinta na halinda suke ciki, zan iya cewa shine kusan k'arfin gidansu Ummyn Wannan knan.. Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to my *Late Siblings* *Page 2* Satin Baba d'aya aka sallameshi, duk d'awainiyar su Bilal ya d'au nauyi har aka sallamesu suka dawo gida. Albarka kam Bilal yasha shi wajan Baba da Mama Ummy koh rasa bakin godiya tayi.. Bayan sun dawo Ummy ta koma bakin sana'arta na tuyan wara a k'ofar gida, sam Bilal baya san suyan datakeyi anma ba yanda zeyi haka ya hak'ura duk da zuciyarshi da ke misi suya kullum idan ya dawo aiki ya ganta k'ofar gida.. Yauma kamar kullun tana k'ofar gida tana suya, sam yau ba ciniki duk ta damu gashi yau basuda ko k'wayar hatsi a gidan kuma bataso Bilal ya sani dan d'awainiyar tasu tana ganin yayi yawa, Tana cikin tuya taji Muryan Bilal a bayanta cikin sanyayar Muryansa "Sannu da aiki Hrt" Da d'an murmushi ta juya ta kalleshi, sanye yake da wandan jeans duk ya fatattake daga guiwa, da bak'ar riga itama kod'adiya, fuskanshi da kayan jikinshi duk siminti duk yayi butu butu, da alama daga wajan aiki yake "Sannu da dawowa" "Yauwa sannu Hrt, ya kasuwa" Fuskanta d'auke da murmushi tace "Lapia lau" "Fad'amin damuwarki" Duk'ar da kai tayi tana y'ar fara'a "Babu wata damuwa" "Bai dace dakeba

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82