Chapter 69
Chapter 69
"Shhhh! Ka daina kuka dan Allah, ko kanaso nima nayi?" Ya girgiza mata kai yana kallan kwayan idanunta dake cike da k'walla Ta rik'o hannunsa tasa a maranta tana kallansa "Ni da Babyn mu muna tare dakai" Ta k'are maganan tana kuka a hankali, ya rungumeta tsam a jikinsa yana lallashinta. Ta shagwab'e fuska tace "Pls Ya Jamal inaso inje inga Mama, rabona dana ganta wata d'aya kenan kuma nasan itama tanasan ganina kawaici ne ya hanata zuwa" Ta k'are maganan tana zumb'ura baki, ya ja bakin ta saki k'ara k'adan. Murmushi yayi yace "Ba yanzu bah, ni nama manta jiya danaje tace na gaishe ki" Ta kallesa da mamaki, ya kashe mata ido d'aya ya mik'e ya fita, chan sai gashi da wani bak'in leda ya mik'a mata yace "Tace na baki" Jiki na rawa ta amsa ta bud'e, kayan k'amshi ta gani da sinadaran girki kala kala, sai wani leda kuma dake ciki shima ta bud'e, magunguna ta gani ko ba'a fad'a mata ba tasan na menene, tad'anyi murmushi tana cigaba da kallan cikin ledan. Karo sukayi ta d'ago tana kallansa tare da rufe ledan "Meye kake kallan min sirri" Ta murgud'a baki tana k'ara b'oye ledan a bayanta, yayi dariya ya k'ara matsowa "Idan abin ci ne to a raba aba kowa nasa dan bazan yarda bah" Hararan wasa ta masa "Bayan ka riga ka bud'e ka d'auka" Ya d'aga hannu dasauri kamar criminal "Babu ruwana, yanda ta bani haka na d'auko na aje, duk ke kika mantar dani jiya da nabaki da wuri" Ta sake turo baki "Dan Allah Ya Jamal ka kaini" Ya mak'e kafad'a yana kwaikwayan irin magananta "Aa nak'iya" Takai mai dukan wasa ya rik'e hannun ta saki kukan shagwab'a, kwantar da ita yayi kan gadon ya soma lallubenta, ina ganin haka na tattara nabar musu d'akin. K'arfe takwas da rabi na dare ya fito daga masallaci bayan yayi sallahn isha'i, side d'insu ya shiga dasauri dan so yake ya fita, Mabrookah ya samu a falonta tsaye duk tayi wani laushi, rana d'aya harta fad'a, ya k'arasa kusada ita dan yanzu tausayi take basa ya kama hannunta yad'an matse ta lumshe ido wasu sabin hawaye suka gangaro mata "Haba k'anwata, banace ki daina kukan nan bah" Ta bud'e idanunta a hankali tana kallansa "Bazan iya daina kuka na ya Jamal har sai naje naga Mummy da Mami, dan Allah ka kaini wajansu" Yad'anyi jim yana kallanta, shima chan d'in yakeso yaje kafin gobe a shiga court yaji yanda za'ayi, dan har a zuciyarsa baisan wani abu ya samesu, ko ba komai Mami tamkar mahaifiya take a garesa, sannan Aunty Faty surikarsa ce. Maganan datayi ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi, ya d'ago yana mata murmushi, "Ki bari komai will be fine insha Allah" Ta girgiza masa kai tana cigaba da kuka "Aa pls, dan Allah Ya Jamal" Ya k'are maganan da matsanancin kuka, ya d'ago kanta yana share mata hawaye "Stop crying" "Dan Allah zanje na gansu" Ya sassauta rik'on daya maya mata yace "Jeki shirya" Dasauri ta shiga d'akinta ya bita da kallo tare da sauke ajiyar zuciya. Sama ya haura ya shiga d'akinsa ya sauya zuwa kaftan ya fito ya shiga d'akin Ummy, ta gama shiryawa kenan cikin doguwar rigar Atampha tana murza powder a fuska ya shigo, wajan mirrown ya k'arasa ya sak'ala hannunsa a wuyanta "Kinyi kyau sosai Wife" Tayi murmushi tana kallansa ta mirrown "Ya Jamal ina zaka?" Ya sunkuyo da fuskansa kusada nata yace "Ko kin fasa zuwa wajan Maman neh" Ai dasauri ta mik'e har tana kokarin turesa ta d'auko Hijab sai dariya yake mata, hannunta ya kama suka fito, a falon k'asa suka samu Mabrookah itama ta shirya, Tana ganinsu tare taja guntun tsaki tayi gaba suna binta a baya, tun daga k'ofar falonsu ya danna button d'in security motar ta k'arasa ta bud'e dasauri ta shige gaba. Sam Ummy bata nuna damuwa ba ta bud'e baya ta shiga yaja suka bar cikin gidan. Jefi jefi shida Ummyn suke hira har suka k'arasa kofar gidansu Ummyn, ta bud'e dasauri ta fita, ganin bai fitoba yasa ta juya tana kallansa "Ka shigo mana" Yad'an kalli Mabrookah dake gefensa tana cika tana batsewa yace "Zamu d'an fita ne idan zan biyo na d'aukeki sai na shiga mu gaisa" Batace masa komai ba ta juya ta shiga cikin gidan rai b'ace. Police station d'in suka nufa, sunyi sa'a sun samu Mifzal bai riga ya tafi bah. Jamal na masa bayani ba b'ata lokaci yasa wani daga cikin 'yan sandan ya fito dasu zuwa secret room. Mifzal da kansa ya musu jagora zuwa d'akin, Kallo d'aya Mabrookah ta musu ta fashe da kuka ta k'arasa inda suke zazzaune, Mami nakan wheel chair duk sun rame kamar basu bah. Ta tsugunna gabasu tana kuka tana kallansu "Mummy, Mami meyasa kukayi haka? Meyasa kuka bari shed'an yaci galaba akan ku" Barin musu wajan Mifzal yayi, Jamal na bakin k'ofa yana hawaye, kallan Mami yake tayi ganin yanda k'afanta ke nannad'e da bandage sai zuban ruwa yake yana wani irin k'arni. Daga Mami har Aunty Faty kasa magana sukayi sai bin Mabrookahn suke da kallo, A hankali Jamal ya soma takawa zuwa wajan, Mami da d'ago ad'an tsorace tana kallansa, ya tsugunna guiwa biyu gabanta ya kama k'afarta dabaida ciwo yana kallan fuskanta hawaye na zuba a idanunsa. Tayi saurin kauda fuska ta fashe da kuka, ya d'ago yace "Har gobe Mami ke uwace a gareni, har yanzu matsayinki a rayuwata yana nan bai chanza bah, duk abinda kikamin na yafe miki Mamina" Ta janye k'afanta daya rik'e tana cigaba da kuka "Rud'in duniya da bin zugan shaid'an su suka jamin na shiga wannan halin, ka gafarce ni D..." Yayi saurin sa hannu ya rufe mata baki yana girgiza mata kai. Kasa magana Mabrookah tayi sai kuka datake kamar ranta zai fita. Mifzal ya shigo ya fad'a musu lokaci yayi, hakanan sunaji suna gani suka bar wajan suna kuka suna waiwayen su Mamin. Ransu duk ba dad'i suka shiga mota suka bar station d'in, saida ya tsaya ya d'au Ummy daketa cika tana batsewa sannan suka nufi gida. Daru suka sha daren ranar shida Ummyn dan sosai ranta ya b'aci na barinta dayayi suka wuce. Washe gari ranar da za'a shiga Court, da wuri ya tashi ya shirya saidai Yau Wife d'insa ta tashi da zazzab'i, dole saida ya tsaya ta shirya sannan suka sauko yana rik'e da ita dan jiri take gani, Mabrookah suka samu a falo ta shirya tana zaune tana jiransu lokacin k'arfe takwas da rabi. Shi da kansa ya bud'e ma Ummy mota ta shiga gaba, Mabrookah ta turo baki ta shiga baya suka d'au hanya. Tara daidai duka isa Court d'in, sun samu mutane duk sun hallara, bayan zazzauna aka soma gabatar da k'aran da Areef d'an Alhaji Ameenu ya kawo akan abi ma Mahaifinsa hak'insa, bada umarnin a kawo Alhaji Ameenun Alk'alin yayi, nan wani d'an sanda ya shigo da Alhajin da Bilal, Ummy dake rakub'e jikin Jamal saboda sanyin datake ji ta zaro ido tare da d'agowa tana kallan Bilal wanda duk ya rame kamar bashi bah. Gaban Jamal ya fad'i sanda ya d'ago ya kalli Alhaji Ameenu, Ummy ko Areef ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82