Chapter 77
Chapter 77
sai na saida gidan nan na sayi wani a chan Abujan" Sai a lokacin Abba yace "Gaskiya nayi matuk'ar mamakin kalaman yarinyan nan, yarinya k'arama kamar wannan da irin wad'an nan maganganun" "Ba abin mamaki baneh ai Alhaji, ka manta gado?" Ya sauke ajiyar zuciya yace "Na aminta da maganar taka bama saika saida gidan bah, chan is ok for us ai" Ammi ta saki lallausan murmushi "Allah ya k'ara rufa mana asiri ya kuma karemu daga sharin mak'iya" Duka suka amsa da Ameen. Nan Ammi tayi serving musu breakfast sannan ta haura sama wajansu Areefah. Ganin Ummy kwance yasa ta k'arasa dasauri bakin gadon "Ummy lafiya?" Ta d'agota taji jikinta da zafi, gaba d'aya Ammin ta rud'e ta soma neman magani. Dakyar ta samu tad'anci wani abu sannan ta bata magani, kan kace komai ta amayar dashi. Koda lokacin tafiya yayi Ammi tace su tafi ita zata zauna da Ummyn, hankalin Jamal gaba d'aya yana kan Wife d'insa hakanan badan ransa yaso ba suka tafi Court d'in dasu Abba harda Areefah. A chan suka samu su Ram da Mifzal, bayan alk'ali ya zauna aka gabatar dasu Mami, kallo d'aya zaka musu duk su baka tausayi sunbi sun rame sunyi bak'i kamar basu bah. Idanun Mami na kan Jamal tana hawaye tana kallansa. Bayan an karanto shar'ia aka yanke musu hukuncin d'aurin rai da rai. Ba shiri Jamal ya fashe da kuka a Court d'in, Areef ya fito dashi waje yana lallashinsa. Mami sai kuka take itada Aunty Faty, haka aka fito dasu Aunty Faty na tafiya da k'afafunta while Mami na kan Wheel chair ana turata. Jamal na ganinsu ya fizge daga rik'on da Areef ya masa ya nufesu Mami ta fashe da kuka "Ka yafemin Jamaludeen, ka yafemin" Yana aniyan k'arasawa akayi saurin sakasu a mota aka tafi dasu. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 91 Yana aniyan k'arasawa akayi saurin sakasu a mota aka tafi dasu. Guiyawu biyu yasa a k'asa yana bin motan da kallo hawaye na cigaba da zuba daga idanunsa, Areef ne yayi saurin k'arasowa ya d'agosa daga k'asan tare da rungumesa yana hawayen tausayin yayan nasa. Mifzal wanda fitowansa kenan daga court d'in ya tab'e baki cike da takaici, sosai abin Jamal ke basa mamaki. Abba shima ya k'araso ya rik'e masa hannu yana lallashinsa, mota suka sakashi suka d'au hanyan gida. Maganganu Masu dad'i Abba ya dunga ma Jamal na kwantar da hankali har ya samu yad'an saki ransa kafin su isa gida. Uffan Areefah batace ba sai bin Jamal d'in datake da kallo. Koda suka isa gida bai shiga side d'in dasu Ammi suke bah, d'akinsa ya wuce ya kwanta yana sauke Ajiyar zuciya, gaba d'aya jinsa yake wani iri ga zuciyarsa dake masa suya. Areef ne yaba Ammi labarin hukuncin da aka yanke masu Mamin, hamdala tayi na godiya ga Allah, Areef tace "Ammi ina Aunty Ummy" "Ta samu bacci" cewar Ammin tana k'okarin shiga kitchen dan kawo musu abinci. Koda Ummyn ta farka Alhmdullh jikin nata da sauki sosai, sai zuciyarta dake cigaba da tashi anma Aman yak'i zuwa. Areefa ne ta had'a mata ruwa tayi wanka sanan ta gabatar mata da abincin da Ammi ta mata. Sosai taci dan ya mata dad'i ga kuma yunwa dake damunta. Kulla da gata Ummy tasha shi ranar, koda Jamal ya fito sallan Azahar a masallacin ya zauna bai shigo ba har akayi sallan La'asar. Ana idarwa Abba ya kama hannunsa suka shiga cikin gidan, kan dinning ya zaunar dashi yasa Areefah ta zuba masa abinci. Ya yatsine fuska yana kallan Abincin "Abba na k'oshi" Abban ya zauna kan kujeran dake kusa dashi yana kallansa cike da tausayawa "Nasan yanda kakeji a halin yanzu Jamaludeen, anma hak'uri da Addu'a shine abin abinda yafi dacewa. I knw its hard ka manta dasu, mutanen da suka rik'eka duk da ita bata maka rik'on daya dace bah" Hawayen daya gani sun gangaro ma Jamal d'in ne yasa ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa "Addu'ar neman gafara shi ne kad'ai soyaiyar da zaka nuna musu a halin yanzu" Ya daga kafad'arsa yana cewa "Kasa ranka a inuwa, bansan ganinka cikin damuwa" Jamal ya gyad'a kai tare da share hawayen idanunsa "Nagode Abbana" Abba yayi murmushi ya janyo plate d'in Abincin ya diba a spoon ya kai bakinsa "Eat my son" Yayi murmushi tare da bud'e bakin kad'an Abba ya saka masa yana cigaba da masa kalamai masu dadi. Daga Ammi har Areefa da Ummy wacce ta sauko yanzu sun matuk'ar burgesu bama kamar Ummy, hawaye suka taru mata a ido ta k'arasa kan kujera ta zauna, Tana matuk'ar kewar Mamanta, kawaici kawai take dan bataso ta damesa musamman ganin halin da ake ciki yanzu. Bayan ya gama ci Abba ya basa ruwa yasha, Sannan ya rik'o hannunsa suka dawo falon, Ummy tayi saurin zamewa daga kan kujeran ta gaida Abban ya amsa tare da tambayanta jikinta. Satan kallanta Jamal keta yi ta kauda kai gefe dan fushi take dashi. Abba yace "Wai ina Areef ne tunda muka dawo ban gansa bah" Ammi ta tab'e baki tace "Kasan Areef da d'an banzan yawo, ba ya soma sanin gari bah" Jamal yad'anyi murmushi yace "Abba inaso muje mu gaida Umman Ummy idan ba damuwa nida su Ammi" Ammi tayi saurin cewa "Wallahi kamar ka shiga raina, ina zuci zuci na maka magana ka rigani" Ummy ji tayi kamar an sakata a aljanna, badan su Ammi ba babu abinda zai hanata rungumansa dan farinciki, Abba yace "Hakan nada kyau, mezai hana kuje yau dan gobe insha Allahu zamu koma" Ya turo baki "Pls Abba ku bari kud'an kwana biyu sai mu tafi tare" Abba yayi murmushi yace "Nabar abubuwa da dama achan kuma rashina zai iya saka damuwa" Shiru Jamal yayi fitan da Abba keyi da dare kamar yanda suka gani rannan ya fad'o masa, baice komai bah na d'an lokaci, Ammi tace "Aa gobe insha Allahu zamu koma, kuma da 'yata zan tafi dan harga Allah ina tsoron Abinda zaije ya dawo musamman wannan yarinyar Mabrookah" Ya tura baki ya mik'e ya fita yana gungunai, Areefah ta doka tsale ta rungume Ummy tana farinciki, itako Jikinta ne yayi sanyi, tunani ta soma a haka ma bata samu taga Mahaifiyarta balle kuma idan ta k'ara nisa. Ammi ta dakama Areefah tsawa "Karki buge min 'ya dallah saketa" Ta tura baki ta matsa gefe, Ammi ta rik'o hannun Ummyn suka haura sama. K'arfe bakwai bayan Sallahn Magriba suka je gidan Mama, sosai tayi farinciki da zuwansu, bata wani yi mamaki ba dan Bilal ya bata labarin duk abinda ya faru. Murna wajan Ummy ba'a magana, Abinci Mama ta gabatar musu, babu wani k'yankyami Ammi da Areefah suka ci tare dayin santi dan Mama ba baya bace wajan iya girki. A nan Ammi ke shaida ma Maman tafiyar Ummy Abuja, Jikinta yayi sanyi anma ba yanda ta iya hakanan tad'anyi murmushi tare da musu fatan Alheri. Hira sosai Ammi da Mama sukayi kamar sun dad'e da sanin juna. Tare sukayi sallan Isha'i, suna nan Jamal da Areef suka shigo suka gaida Maman cike da girmamawa. Sun shiga gidansu Bilal, Umman Bilal tayi farinciki da ganinsu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82