Chapter 22
Chapter 22
tana gyaran d'aki su tayana, wani lokacin kuma suna d'akinta suna hira. Ba yanda Aunty Faty batayi ba akan ta hanasu anma sunk'i ji. Ranar Juma'a da safe akayi ma ma'aikatan albashi, bakin Ummy har kunne musamman dataga wannan karan shima dubu d'arin aka biyata. Dak'yar Mami ta yarda ta barta ta tafi gida weekend gida. Hankalin su twins sosai ya tashi ganin Ummyn zata tafi dan saboda ita gidan ke musu dad'i. Har bakin gate suka rakota suka koma cikin gida a sanyaye. Napep ta tara ta shiga, suna karyo kwanan layinsu ta hango gidan su da masu aikin gini kamar gyara yake a gidan. Da mamaki ta shiga tana bin ma'aikatan da kallo, dakunansu taga an had'e an fitar da two bedroom mai kyau, Mama ta fito daga Falor ganin Ummy yasa ta rungumota cikeda murna. "Mama wannan aikin fah" Hannunta Mama ta kama suka shiga cikin Palourn, nan Ummy ta saki baki tana kallan yanda gidan nasu ya koma, had'adden set d'in kujeru ta gani, ga tiles da aka malale falon dashi, sosai falon yayi kyau, tabi Plasman dake jikin bango har lokacin idanunta a warwaje "Mama wannan kayan daga ina" Baba ya fito daga d'aki yana dogara sandarsa yana murmushi "Muryan wa nakeji kamar na Ummyna" Dasauri ta k'arasa ta rungumeshi tana dariya "Baba ni ce" Ya shafa kanta yana cewa "Ba abinda zamuce ma yaron nan sai Allah ya mai albarka" "Baba Ya Bilal ya dawo neh? Dama nasan bai mutu ba zai dawo" Mama tace "Duk wannan abubuwan da kika gani, duk aikin Jamaludeen neh, kuma yace yayi dan Allah ne ba wani abu bah" Yatsine fuska Ummy tayi tace "To an gode" Ta shiga bedroom, nan ma taga an gyara shi tsaf harda sabon funitures, ta tab'e baki ta aje jakanta sannan ta fito. Albashinta ta mik'ama Baba kamar yanda ta saba, Albarka ya saka mata yace "Wannan karan ki adana kud'inki dan munada komai dangane ga kayan abinci" Ummy tayi murmushi tace "Tho Baba, anma yakamata mu sake komawa asibiti ka sake ganin likita" "Hakaneh" cewar Mama "Aa Ummy, nikam Alhamdulillah naji sauk'i, yanzu babban burina bai wuce naga kin daina bauta bah, kin koma makaranta ko kinyi aure" Mama tace "Komai Lokaci ne Mallan, Fatan mu ka samu lapia, komai yazo daga baya" Murmushin takaici kawai Baban yayi baice komai bah. Washe gari lahadi, masu aikin ginin basu zo ba suna hutu, yau D'anwake Ummyn tayi musu dan Baba nasan d'anwake sosai, bayan ta zuba musu nasu ta d'au nata ta fito tsakar gida kan tabarma tana ci. Ta saka loma kenan ta jiyo sallaman su Twins, dakyar ta iya had'iyewa suko mai zasuyi in ba dariya bah. Mik'ewa tayi dasauri ta rungumesu tana dariya "Sannunku da zuwa, ya akayi kukasan gidan mu" "Ya Jamal ne ya kawo mu yana waje" cewar Najma Ciki ta shiga dasu suka gaisa da Baba da Mama, sannan suka dawo waje dan ciki akwai zafi, d'an waken ta zubo musu suka soma ci suna santi, Ummy ko me zatayi inba dariya bah. Mama ta lek'o tareda rik'e hab'a "Oh ikon Allah, ashe ku nan zama kukayi kuka bar Yayan naku a waje" Sai a sannan suka tuna ashe da Jamal suke, Mama tace Ummy ta tashi tace mai ya shigo, turo baki tayi taja hijab a igiya ta fita, cikin mota ta sameshi yana waya, ta k'arasa ta juya fuska gefe tace "Ance ka shigo" Bata jira mai zaice ba ta koma ciki, shi dariya ma abin ya bashi Ummy sai kace mai Juju, wani lokaci ka gansu Lafiya suna shiri, watan kuma a yini ba'a masa magana bah. Da sallama ya shiga ciki, Najma da Najwa na zaune tsakar gidan suna cin abinci "Dama nan kukafi auki, Ci, Ci!" Najma ta b'ata fuska, Najwa ko Dariya tayi ta sake kai loma tana kallansa. Dariya yad'anyi ya girgiza kai ya shiga falon da sallama. Har k'asa ya tsugunna ya gaidasu, Ummy ta had'o mai d'anwaken. Ba ko kunya ya soma ci suna hira da Baba, Ummy sai binsu da kallon mamaki take ganin yanda suke hira kamar wad'anda sukayi shekara da sabo. Waje ta koma suka cigaba da hiransu da Twins, bayan sun gama Jamal yama su Mama sallama yace ma su twins suzo su wuce, Mama ta lek'o tace "Ummy ina ce kema yau zaki koma, kizo ki d'au kayanki mana ki bisu" Baki ta zungure tace "Mama ni sai anjima" Jamal yayi murmushi ya fita, har bakin mota ta rakosu tanata d'agama su Twins hannu, har yayi gaba ya dawo yayi parking ya fito "Wai Twins kad'ai kika gani neh" Ta galla masa harara "Ni su kad'ai na gani" "Koh" Ta kauda kai gefe "Zaki sani neh ai" "Zamu sani zakace" Yayi murmushi yana girgiza kai ya shiga yaja motan yabar anguwan. Sai bayan la'asar Ummy ta shirya tsaf dan komawa bakin aikinta, d'aki ta samu Baba dan masa sallama, ya rik'o hannunta yana cewa "Jamaludeen, Bahar da mahaifiyarsa duka ba abin yarwa baneh. Ki rik'esu Hannu bibiyu kinji" "Insha Allahu Baba" "Ki zama mai hak'uri a duk inda kike, ki kare mutuncin ki, ki zama mai biyaiyya da girmama nagaba dake, ki rik'e addininki, In kikayi haka insha Allahu bazaki tab'a tab'ewa bah. Kin faranta min Ummy, tunda na haifeki baki tab'a min abinda kika b'atamin bah, Allah ya miki albarka Ummy" "Amin Baba, Kai kuma Allah ya baka lafiya" "Ameen!" Ta fito sukayi sallama da Mama ta fita ta tari adaidaita ta hau ta koma gidan aikinta. Tana shiga dasu Twins tayi arba sunata murna, jakan hannunta suka amsa suka shigan mata dashi d'aki. Duk abinda sukeyi Aunty Faty na kallo, ranta sosai ya b'aci ta haura sama zuwa d'akinsu Tana mita. A ranar Aunty Zainab mahaifiyarsu Twins ta koma, su kuma zasu d'an yi hutu, Aunty Faty ko cewa tayi ba yanzu bah. Babban abinda ya d'aurema Ummy kai bai wuce rashin ganin Laurat bah, dan tun sanda zata tafi ta fad'a mata sati d'aya kawai zatayi gashi yau kusan kwana Shad'aya kenan. Da daddaren ranar Mami da Abba suna falon side dinshi, Mami tace "Alhaji magana nazo muyi" Yace "Ina jinki" D'an jim tayi tace "Alhaji har yanzu bakace komaiy kan alkawarin auren Jamal da Mabrookah bah" "Tho mai kikeso nace Maimuna" "Yakamata ace yanzu anyi auren nan, tunda ya samu Lafiya ga kuma aiki ya fara" Abba yad'anyi murmushi "Maimunatu kenan, abinda nakeso ki gane a nan shine, yanzu ba d'ah baneh, yanzu an daina wannan had'in. Gwara a bar yara su zab'i abinda sukeso" "Haba Alhaji yanzu ya za'ayi da alkawarin da aka d'aukan ma Yaya Faty, kuma itama Mabrookahn tana sanshi sosai, shima nasan yana santa" "Sanda kukayi alkawarin ai bana wajan, ba sai daga baya kike gayamin da alkawari bah" Fusata Mami ta fara ta juya fuska gefe "Mafita a nan shine, zan tarasu na tambayesu idan har duka suka amsa suna san juna shiknan" "Anma Alhaj...." "Aa Maimuna, wannan shine magana" Mik'ewa tayi tabar falon ta nufi side d'insu, Aunty Faty ta samu a falo ta sanar da ita yanda sukayi da Alhajin "Maimuna kina bani mamaki, yanzu ke bazak'i iya tank'wara d'anki bah" Shiru Mami tayi ta haura zuwa d'akin Jamal, bata ganshi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82