Chapter 68
Chapter 68
ka fad'amin kaji" Yanda ta langwab'ar dakai ta sake basa tausayi, ya d'agata zaune ya mik'e tare da kama hannunta "I promise uh indai kikaci abinci zan fad'a miki" Ba musu ta mik'e tana turo baki suka haura sama, kan dinning suka samu Ummyn tana jiransu, Mabrookah na ganinta ta sake mak'ale Jamal d'in sai wani zumb'ure zumb'ure take, yaja mata kujera ta zauna sannan shima ya zauna yana kallan Wife d'insa dake ta murmushi wanda ita kad'ai tasan dalilinsa "Wife serve us please" Ba musu ta mik'e tayi serving d'insu soyaiyar d'ankali da plantain da kuma kwai, shi ya had'a ma Mabrookahn tea. Itadai Ummy binsu kawai take da ido, Lipton kawai ta had'a dan shi kad'ai yanzu take iya sha. Mabrookah sai kaud'i take tana wani shagwab'a, Ummy sai kallanta take tana murmushi, tana gamawa ta mik'e tabar Falon ya bita da ido ganin yanda fuskanta ya sauya. Daru sukayi sosai shida Mabrookah dan k'in fad'a mata yayi wai sai anjima, nan ta tasashi a gaba tanata rera masa kuka. Ya dafe kansa cike da tashin hankali, ga Ummy daga gani Ranta ya b'aci, ga Mabrookah ta tasa shi gaba tana kuka. A ransa yace "Kai auren mata biyu beyi bah" A chan police station kuwa Ba'a sha wahala dasu Mami wajan tambaya bah, sun fad'i gaskiya kamar yanda aka buk'ata. Hakan yama Mifzal da Ram dad'i ganin bazasu wahalar da shara'a bah. Yanma lis Ram yazo gidan, a haraban gidan yayi parking ya aika masu gadi su Kira Jamal d'in dan wayansa na hannun 'yan sanda. A tare suka fito shida mai gadin, Jamal ya mik'a masa hannu suka gaisa sannan suka d'unguma zuwa ciki. Mabrookah ya kira sannan ya shiga d'aki ya kira Ummy suka fito tare. Suna zama Mifzal shima ya shigo, duka suka tattaru a falon su Biyar. Jamal ya mik'e ya shiga d'akinsa ya d'auko diaryn Abba ya fito dashi ya mik'ama Ram. Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 8:20 AM] +234 706 272 2689: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 85 n 86 Jamal ya mik'e ya shiga d'akinsa ya d'auko diaryn Abba ya fito ya mik'ama Ram "Inaso ka karanta kowa yaji" Ya nuna Mabrookah da Ummy yace "Yakamata su sani a matsayinsu na iyalai na, sannan kuma ku sani dan bani da aminai kamar ku" Jikin Ram yayi sanyi dajin maganan abokin nasa, a hankali ya bud'e diaryn ya k'urama rubutun ido sannan ya soma karantawa a natse. Dukansu saida sukayi mamaki dajin Labarin dake k'unshe cikin diaryn, Ummy ko kuka ta dunga yi na tausayin mijin nata, lallai yanzu take k'ara godema Allah dan duk halin da ta shiga itada iyayenta bai kai wanda Jamal ya fuskanta bah. Mifzal ya dubi Jamal har lokacin fuskansa d'auke da alamar tambaya "Nayi mamaki sosai dajin wannan labarin, Abba da Mami dama basu suka haifeka bah" Ya gyad'a kai idanunsa cike da kwalla, yace "No Wonder ita da Yayarta suke san kasheka dan suci dukiyarka" Mabrookah ta kalli Mifzal da alamar tambaya "Bangane me kake nufi bah" Mifzal ya juya ya kalleta dakyau dan dama haushinta yakeji "Da uwarki da k'anwanta Mami suka had'a baki suka kashe Abba, sannan...." "What!" Ta mik'e dasauri ko ina na jikinta na rawa, ta fashe da kuka tare da juyawa tana kallan Jamal "Ya Jamal kanajin abinda yake fad'a? Tayaya Mummy na da Mami zasu kashe Abba me yayi musu" Ta kuma fashewa da kuka, Ram ya d'anyi gyaran murya yace "Abinda Mifzal ya fad'a gaskiya neh" Ta d'ago dasauri ta kallesa ya gyad'a mata kai "Yanzu haka suna police station a tsare kuma gobe za'a shiga court" Basu ankara ba ta sulale k'asa ta sume, Ummy ta rarrafa dasauri inda take tana kuka, Jamal ya k'araso wajan gaba d'aya hankalinsa a tashe. Ram yace "Ummy samo ruwa yi sauri" Ta mik'e ta shiga kicin dasauri ta d'auko ruwa, Tallafo ta Jamal yayi ya d'aurata a cinyarsa Ram ya yayyafa mata ruwa, ta sauke ajiyar zuciya a hankali, wani kukan ta kuma fashewa dashi tana girgiza kai "Mummy na da Mami bazasu tab'a iya kashe Abba bah" Ta bud'e ido a hankali ta rik'e hannun Jamal "Dan Allah Ya Jamal kace min Mafarki nake" Rungumeta yayi yana shafa kanta duk da shima hankalinsa a tashen yake "Its ok, ya isa kibar kukan." Ya mik'ar da ita tsaye ya kama hannunta tana kuka suka sauka k'asa, d'akinta ya kaita ya kwantar da ita tare da lallasheta. Bai fito d'akin ba saida tayi shiru anma zuciyarta cike yake da bak'in ciki da takaicin abinda taji daga bakin Mifzal. Koda ya koma Falon yanda ya barsu haka ya dawo ya samesu, sai Ummy dake gefe tanata jan majina tana sharan k'walla jefi jefi. Ya k'arasa ya xauna kusa da ita tare da rik'o hannunta yana murzawa a hankali. Ram yace "Menene Abinyi yanzu? Akwai abubuwa sosai a gabanmu, na d'aya Court d'in da zamu shiga gobe, na biyu neman Parent d'inka" Jamal yayi shiru baice komai bah, Mifzal yace "Gaskiya ne wannan, anma a bari sai an gama case d'in nan sannan sai mu soma binciken real parent d'inka" Cikin sanyin murya Ram yace "Kayi hak'uri Friend, kad'au duk abinda ya faru a matsayin Jarabawa, Haka Allah yaso, Haka yaso ka kasance. Allah ya baka ikon cin wannan Jarabawar" Ya amsa da Ameen Hawaye na gangara daga idonsa "Har gobe Inasan Mami banasan wani abu ya sameta, ko ba komai Uwace min dan bata rageni wajan Tarbiya da neman Ilimi bah" Mifzal yayi ajiyar zuciya yace "Hakaneh, babban tashin hankalina ma shine idan aka shiga court, Allah kad'ai yasan hukuncin da za'a yanke musu. Kasan sharri'a sab'anin hankali ce" Kuka Ummy keyi sosai daga zaunen datake, wani amai ya taso mata ta mik'e dasauri tayi d'akinta, Jamal ma ya mik'e zaibi bayanta, Mifzal na ganin haka ya mik'e yana gyara rigan jikinsa "Mu zamu wuce, Pls gobe k'arfe Tara na safe za'a shiga Court, make sure kin iso kamin lokacin" Kai kawai ya iya gyad'a musu ta bi bayanta dasauri. Amai sosai ya sameta tanayi, duk abinda tashi saida ya fito, kuka take sosai tana maida numfashi ya k'arasa ya rungumeta ta baya yana mata sannu. Saida ta gama sannan ya saketa ya d'auraye mata baki ya maidota d'aki. Ya d'aurata kan gado ya k'ara rungumeta tare da lumshe ido. Bashi da wani gata yanzu daya wuce Wife d'insa, duk sanda suke tare sai yaji damuwarsa ya yaye, Maraicinsa ya gushe. Ya k'ara mak'alkaleta itama ta rungumesa murya chan ciki ciki tace "Ya Jamal rayuwarka darasi ne da kuma ishara ga duk wanda ya jita, nasha wahala sosai a rayuwa ni da Iyayena tunda Mahaifina ya soma rashin lafiya, danaga Rayuwarka na kuma ji labarinka sai nake ganin namu ba komai baneh. Tabbas Rayuwar daka tsinta kanka a ciki Jarabawa ce daga ubangiji, kayi hak'uri sannan ka maida lamuranka ga Allah" Ta k'ara rungumesa tace "Kada ka k'ara tunanin bakada kowa, Am here for you, zan zame maka Uwa, uba dangin daka rasa" Ya fashe da kuka yana rungume da ita "Thank uh Jaleelah, Allah ya miki Albarka" Janye jikinta tayi daga nasa ta d'ago fuskanshi dake ta zubar da k'walla
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82