Chapter 15
Chapter 15
yana cewa "Mungode sosai, and idan ta tashi zamu kawota insha Allah" Mabrookah na daga gefe tana b'ata fuska cikeda takaici. Abba ya k'arasa falon k'asa ya zauna su Mami suka bishi suma suka zazzauna yace "Munga ikon Allah koh? Mukaita magani ashe cuta bata asibiti baneh" Ya kalli Ramadan yana cewa "Babu abinda zance maka Ramadan sai Allah ya saka da alkhairi, lallai kai aboki ne na gari" Murmushi Ramadan d'in yayi yana d'an girgiza kai "Abba bani yakamata ka gode mawa ba sai yarinyan nan, ita yafi chanchanta da'a godema wah dan ni k'arashe nayi kawai" Mami ta gyad'a kai tana cewa "Allah saki Ummy, yarinyan nan mutum ce, ban tab'a samun mai aiki wacce takeda gaskiya da rik'on amana kamarta bah, Lallai ta chanchanci yabo" Abba ya sauke nannauyan ajiyan zuciya yace "Gaskiya neh, shiyasa nad'au wani alkawari a raina. Insha Allahu zan kyautatama yarinyan nan, zan inganta rayuwarta insha Allahu" Mabrookah ta saki d'an guntun tsaki tana cewa "Duk ba wannan yakamata ayi magana akai bah, Ya Jamal yakamata a san abinyi dan ba'asan menene ma'anar baccin dayake bah" Mami ta zafga mata harara, Ramadan ya mik'e ya haura d'akin Jamal d'in. Bacci yake sosai Lafiyar Allah, wani murmushi Ramadan din yayi yana kallansa dan tunda ya fara rashin lafiyan nan bai tab'a ganin yayi bacci irin nayau bah. Zama yayi d'akin yana gadinsa har dare, Jamal d'in bai farka ba sai k'arfe takwas da rabi, tashinshi yayi daidai da tashin Ummy. Kansa ya rik'e idanunsa a rufe, a hankali ya bud'e ido, ganin d'akin yayi yana juya masa yayi saurin rufe idon yana cigaba da rik'e kansa. Ramadan ya mik'e ya k'araso bakin gadon yana kallansa da farinciki "Jamal! Jamal kana jina" Jin muryan Aminin nasa yasa ya sake bud'e ido ya zubasu kan abokin nasa "Say something Jamal, yi magana ko zanj dad'i" Mami da Abba a tare suka shigo d'akin Mabrookah na binsu a baya Abba ya karaso bakin gadon yana cewa "Ramadan yaya?" Saurin bud'e ido Jamal d'in yayi ya zubasu kan Abbansa yana kallansa da d'an murmushi, daga Abban har Mami da Mabrookah mutuwar tsaye sukayi suna kallansa, kok'arin mik'ewa zaune yake yana yatsine fuska, Ramadan yayi saurin rik'eshi yana cewa "You have to rest, i knw jikinki ba dad'i yanzu" Girgiza kai yayi cikin sanyaiyar murya yace "No I'm alryt" Da taimakon Ramadan d'in ya zauna, Mabrookah tako a hankali ta zauna gefen gadon ta fashe da kuka tareda rik'e hannunsa. D'ago kanshi yayi yana kallan Iyayen nasa da tuhuma ganin suna hawayen neh ke fita daga idanunsu "Mami, Abba Lapia? Meya faru kuke kuka?" Ya juya yana kallan Ramadan da tuhuma "Ramadan meya faru? I tot ina kaduna wajanka, mekuma nadawo yi yau?" Mami ta k'arasa gabanshi tana shafa suman kanshi "Its a long story, have some rest zamuyi magana anjima" Maganan Mami ba k'aramin d'aure masa kai yayi bah. Zama yayi hankalinsa duk yana kan labarin da Mami tace zata bashi, hira Ramadan keta masa yana bashi amsa jefi jefi. A bangaren Ummy kuwa, koda ta bud'e ido wani irin mugun sarawa taji kanta ya mata, ta saki k'ara kad'an tasa hannunta na dama dafe kan, ga kuma hannunta na hagu dake mata zafi sosai. Laurat ce ta shigo d'akin dan tun dazu hankalinta ke kanta dan sanin halinda take ciki, bakin gadon ta k'arasa tana cewa "Sannu Ummy kin tashi" Batace mata komai ba sai runtsa ido datake tayi hawaye na gangara a idanunta. Fita daga d'akin Laurat d'in tayi dan kiran Mama talatu, Mami ta had'u da ita ta fito daga d'akin tace "Yaya ta farka ne" Ta bata amsa da eh, dakin ta shiga gainta tayi duk ta fita haiyacinta, a rud'e ta haura sama zuwa d'akin Jamal, tana shiga tace a rud'e "Ramadan taso mukai Ummy asibiti ta farka kuma... Ganin ya mik'e yasa ta fasa k'arasa maganan ta fita yana binta baya, Jamal ya bisu da ido kanshi a d'aure. Wai meke faruwa a gidan nan neh? Wacece kuma Ummy? Dakyar ya sauke k'afafunsa k'asa, jin jikinshi yake duk ya masa tsami, mik'ewa yayi tsaye ya koma ya zauna tareda sakan k'ara kad'an. Tsayuwa ne ya gagaresa, dakyar ya sake mik'ewa yana ririntse ido tareda yatsine fuska saboda yanda k'afar ke masa zafi. Bango ya soma dafawa yana takawa a hankali har ya sauko k'asa, daidai nan Ramadan ya fito daga d'akin Ummyn dauke da ita a hannunsa idanunta a lumshe tana numfashi d'ai d'ai. Ya bisu da ido da mamaki har suka bar falon sukayi waje, dakyar ya k'arasa saukowa ko kamin ya fito har Ramadan ya sakata a mota sun fice daga gidan shida Mami. _Zakuyi hak'uri da yanayin typing d'ina nayau, ina busy neh kuma banda chargi_ Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 8:30 PM] Alion Bagari: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 19 Da kyar ya k'arasa saukowa ko kamin ya fito har Ramadan ya sakata a mota sun fice daga gidan shida Mami. Ya koma ciki yana takawa a Hankali har ya isa falon k'asa ya zauna yana cigaba da mamaki. Abba ya sauko da d'an saurinsa yana k'okarin fita, sam bai lura da Jamal d'in ba yaji ya kira sunansa a hankali, ya juya tareda k'arasawa inda Jamal d'in ke zaune ya zauna yana kallansa da murmushi Cikin sanyayar muryarsa yace "Abba wai meke faruwa ne a gidan nan? Jiya na fita natafi kaduna yau kuma na ganni a gida, gashi kuma naga an d'au wata za'a kaita asibiti" Abba ya sauke ajiyar zuciya ya d'ago yana kallanshi yace "Labari ne mai tsawo Jamal, bt tunda ka matsa zan fad'ama anma ka bari naje na samu su Ramadhan a asibiti na dawo" Jamal yayi saurin girgiza fuska ba walwala "Pls Dad ka sanar dani" Jim Abban Yayi sannan yayi gyaran murya ya soma bashi labarin duk abinda ya faru shekara uku da suka wuce. Da mamaki yake kallan Abban baki bud'e, Abba ya cigaba da cewa "Tunda muka dawo daka gida ba wani cigaba sai lokacinda Yarinyan nan tazo" Hawaye suka cika idanun Jamal ya mik'e dakyar yana cewa "Abba muje asibitin tare i want to see her" Abba ya girgiza masa kai tareda rik'esa yana cewa "No ka bari idan ka k'ara jin k'wari sai kaje" Ya girgiza kai yana cewa "No Abba muje yanzu pls naga halinda take ciki tunda am responsible for her Sickness" Abba ya zaunar dashi ya haura sama ya d'auko masa wheel chair ya d'aurasa yana cewa "Muje" Wani switch Jamal d'in ya danna a jikin Wheel chairn ya fara tafiya da kansa, a bakin mota ya tsaya ya mik'e dakyar ya shiga cikin motan Abba ya saka Wheel chairn a booth. Ma'aikatan gidan sai bin Jamal suke da kallo da mamaki, yawancin su hamdala suke ganinshi ya samu lafiya. Shika suka nufa dan Mami ta fad'a masa chan suka kaita, kallo d'aya zakama Jamal ka gane hankalinshi a tashe yake musamman jin shine silan rashin lafiyan nata. Suna isa sukama Ramadan waya ya musu Jagora zuwa d'akinda take, a bakin k'ofa suka had'u da Mami take sanar dasu ana dubata neh. Nan suka tsaya sukayi chirko chirko, Ihunta sukaita ji daga d'akin tana kiran sunan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82