Chapter 40
Chapter 40
da Jamal taga yayi kini kini darai, ya mik'e yana ma Mama sallama yace yana waje. A tare suka fito da ita, a cikin zaure ya kamo hannunta yana cewa "Badan Mama tace kije ba da bazan yarda bah" "Babu fa komai Ya Jamal, Innansa ce zan gaishar idan kuma baka gamsu ba muje tare" Ga mamakinta sai ji tayi yace "To muje" Dariya suka sa duka, saida ya tsaya zauren Innan ta shiga ta fad'a mata sannan ya shiga, sun gaida sosai ta musu nasiha mai ratsa jiki, Sannan suka fito bayan ta dire mata bandir d'in yan d'ari biyu ta amsa dakyar. Shi mamaki yake yanda Innan Bilal take ba ruwanta da kuma san mutane, cikin gida Ummy ta koma shi kuma Jamal ya koma mota ya zauna, message d'in Bilal ne ya shigo wanda ya zama ka'ida kullum saiya turo masa, bud'ewa yayi ya karanta kamar haka _Bazan fasa fad'ama baka isa ka mallaki abinda nakeso na kuma dad'e ina muradi bah. Ina gaf dana kwace muradina daga hannunka, na kuma maka tabon da har ka mutu bazaka manta bah. Saboda kaso abinda nakeso_ Murmushi yayi bayan ya gama karantawa, shi messages d'in Bilal dariya ma suke bashi. Ummy dakyar ta banbaro daga jikin Mama ta fito suka tafi badan ranta yaso bah. Koda sukaje gida har lokacin Mabrookah na falon ta cika tayi fam. Wuceta Ummy ta sakeyi ta haura sama, chan saiga shi shima ya shigo "Sannu da zuwa" tace fuska ba walwala "Yauwa sannu" ya haura sama abinsa. Wanka ya sakeyi ya sauya kayan jikinsa zuwa jallabiya saida ya fara shiga d'akin Ummy ya mata sallama sai turo baki take kamar zatayi kuka. Shi kansa baisan rabuwa da Baebyn saidai ba yanda ya iya, lallashinta yayi har bacci ya d'auketa sannan ya sauko k'asa. Kan dinning ya zauna, ya taho tana karairaya ta d'an dafa kafad'arsa "Honey mai za'a zubama" "Koma menene" yace atakaice. Fried rice ta zuba masa da farfesun kaza ta tura masa gabansa tareda janyo kujera ta zauna kusa dashi "Ko nabaka a baki neh Honey" Ya girgiza mata kai alamar Aa, spoon ya d'auka ya d'ibo tareda bismillah ya kai bakinsa, taunawa ya soma yi yana yatsine fuska. Dakyar ya iya had'iyewa ya juyo yace "Waya girka abincin nan" Ta langwab'ar dakai tace "Ni ce, ko beyi dad'i baneh" Cike da takaici yace "Yayi sosai" Tayi murmushi ta sakala hannunta a wuyansa. Spoon uku ya k'ara dakyar ya ture yace ya k'oshi. Sama ya haura ta koma d'akinta ta sauya zuwa wani fitinanen night gown ta haura saman zuwa d'akinsa. Koda ta shiga dind'in ta samu d'akin ya kashe fitila da alama ya kwanta neh. A hankali ta k'arasa ta kwanta a bayanshi, shiko takaici ne ya cika shi, ta dunga matsowa har ta cin masa, ta rungumesa tana shagwaba "Honey shine ka juya min baya" Yi yayi kamar bai jita bah, k'ara mak'ale shi tayi tana mai waiwayi a k'irji. Saurin rik'e hannunta yayi a harzuk'e yace "Wai meye haka Mabrookah ki kyaleni bacci nakeji" "Haba Ya Jamal ni fa wallahi...." Kasa k'arasa maganan tayi jin ya turata gefen. Ba shiri ta fashe masa da kuka. Dogon tsaki yaja ya mik'e yad'au filo ya koma falo. (Wayyo Jamalu baka kyauta bah) Haka sukayi ta rigima har kwana bakwai, har mamakin rashin kunyan Mabrookah yake yanda ta nuna masa k'irki k'iri sex takeso, abinda shi ko a labari bai tab'aji ba ga Amarya bah. A ranar daya cika sati d'aya a d'akinta ya raba musu kwana. Sannan yace kowa ta rink'a girkinta dan yasan matuk'ar za'ace duk wacce takeda girki ita zata rink'a yi to za'a fuskanci tashin hankali musamman wajan Mabrookah. Ummy Abduol✍🏻 [3/29, 8:36 AM] +234 701 141 1639: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 44 A ranar daya cika sati d'aya a d'akinta ya raba musu kwana. Sannan yace kowa ta rink'a girkinta dan yasan matuk'ar za'ace duk wacce takeda girki ita zata rink'a yi to za'a fuskanci tashin hankali musamman wajan Mabrookah. ***** *Bayan wata biyu* Abubuwa dayawa sun faru, ciki harda fara karatun Ummy a demostration dake cikin ABU, dan tana k'okari sosai. Dakyar malaman suka yarda aka sakata a SS1 kuma ba laifi tana fahimta. Yanzu tana iya karatu saidai idan kalma babba ce bata iya karantawa. Duk da saida aka kai ruwa rana tsakanin Mami da Jamal, dakyar suka samu ta amince. Tayi farinciki sosai da fara zuwanta makaranta. Yanzu sam batada lokaci, tana dawowa k'arfe biyu zatayi sallah ta jira lesson teachernta. Yau saturday ba aiki, tun safe Jamal ke d'akinsa yana bacci. K'arfe sha d'aya da rabi Ummy ta shiga d'akin, kan gado ta hangoshi yana sharan bacci abinsa hankali kwance. A hankali sad'af sad'af ta k'arasa ta zauna kusa dashi ta soma mai tafiyar tsuntsu a k'irji. Tunda ta shigo ya farka, lamo yayi yana sauraran abinda zatayi, salon datazo masa dashi yasa yad'anyi tsam duk da bai bud'e ido ba balle ya motsa. Ita kuwa cigaba tayi tana 'yar murmushi ita a dole tana masa mugunta. Tun yana daurewa har ya hankalinsa ya soma tashi, bata ankara ba taji ya janyota ta fad'a kan gadon, yayi saurin danneta ya mata runfa da jikinshi "Wife ke koh" Baki ta chuno gaba, "To ba kai baneh tun d'azu ina jiranka" Ya d'an sauke lallausan murmushi "Zaki bani sugarn ki neh?" Jin haka yasa ta soma kici kicin zamewa, ya saki 'yar dariya "Ai baki isa ba yarinya, tunda har kika zo sai na sha zuman nan" Ido ta runtse dasauri jin maganan dayake, mamaki ne a ranta yanda yau yake gaya mata maganan bako kunya. Shafata ya soma tayi saurin rik'e hannusa "Yaaa Jamal dan Allah ka bari" Bakinsa yakai saitin kunnenta ya rad'a mata "Ina wahala sosai Wife, ki bari nasamu natsuwa. Ba wani wahala zan baki ba indai zaki saki jikinki" Ta sake matse jikinta hawaye na gangara a idonta "Haba Wife ni neh fah" Bai jira mai zatace ba ya cusa bakinsa cikin nata. Wasa da ita ya soma, ina juyawa na hango 'yan Jamaludeen Fans grp sunata lek'e ta window. Zahra, Hafcycy, Xaboorah, Aunty Nurse, Zeenart, Maman sadeek sune 'yan gaba gaba. Lol Sun d'au mintina a haka, Ummy ba abinda take sai kuka, shiko baima san tanayi bah. Saida ya jagwal gwalata sannan ya fad'a gefe yana mayar da numfashi dakyar. Tana ganin haka tayi saurin mayar da zip d'in riganta ta fita daga d'akin dasauri tana cigaba da hawaye. Ya dad'e a haka sannan ya mik'e dakyar ya shiga toilet. Wanka yayi ya sa kaya, Top Blue da Brown trouser. Sosai yayi kyau sai baza k'anshi yake. Kasancewar ranar girkin Ummy ne d'akinta ya shiga, kan gado ya sameta kwance tayi samo. Murmushi yayi mai sauti ya k'arasa ya zauna kan gadon kusada ita, a tsorace ta mik'e ta zauna tareda duk'ar dakanta. "Yaya dai Wife, ko karatun mu na d'azu bai isheki baneh a cigaba" Ba shiri ta mik'e tana turo baki tareda girgiza kai "Ni dai banasan wannan karatun" 'Kai Wife! Fad'a gaskiya. Bayan gashi har kinyi wanka kin chanza kaya bayan kuma nasan d'azu kinyi" Kunya ne ya kamata kamar ta nutse k'asa haka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82