Chapter 72
Chapter 72
jiranshi, tana ganinsu tare taja tsaki yad'anyi murmushi daidai sanda suka k'arasa saukowa falon k'asan, Hannun Mabrookahn ya rik'e suka fito su duka. Bai sake hannayen nasu ba saida suka kai k'ofar falon Abba, ya shiga da sallama suma suka bi bayansa, Chak Ummy ta tsaya ganin Bilal a falon, Jamal ya janyo hannunta suka k'arasa cikin falon sosai, dukansu a k'asa kan Carpet suka zauna, Cike da girmamawa Ummy ta gaishe su, ganin haka yasa itama Mabrookah gaidasu tana yatsine fuska. Jamal ya nuna Abba da Ammi "Alhamdulillah ku tayani murna naga Parents d'ina" Ummy ta d'ago dasauri cike da fara'a "Dagaske?" Ya gyad'a mata kai yana nuna Abba "Wannan shine Abbana" Ya nuna Ammi sannan ya nuna Areef yana cewa "Wannan kuma k'anina Areef" Kallo d'aya zakama Ummy ka gane tana cikin farinciki, Mabrookah ko sai yatsine yatsine take daga gefe. Ya d'an duk'ar dakai yana sosa k'eya "Ummmm Abba wad'an nan Ummmm Ma..Matana neh" Ammi ta rik'e baki da mamaki "Duka matanka?" Ya sake duk'ar da kai yana murmushi, Albarka Abba ya saka musu sannan yace "Baka fad'a mana meya faru ba bayan rabuwan mu dakai" Nan ya gyara zama ya zaiyane musu komai har zuwa ranar, Ammi kuka take sosai na tausayin d'an nata, Jin gagarumar gudunmawar da Ummy taba d'an nata yasa taji ta shiga ranta sosai. Kallanta kawai take tana zubar da kwalla. Ganin yanda Ammin ke kuka sosai yasa Jamal ya rarrafa ya rungumeta yana shafa bayanta "Its ok Ammina, yau ranar farinciki ne garemu duka" Ta d'ago kanta tana mai zubar da kwalla tana shafa fuskansa "We are so sor..." Yayi saurin sa hannu ya rufe mata baki yana girgiza mata kai, sosai Suka burge duka mutanen dake falon. Areef dake gefe yayi murmushi yace "Abba Lil sis fah na gida" Abba yace "Hakane" Ya juya ga Jamal yace "Areef nada k'anwa sunanta Areefa" Jamal ya saki lallausan murmushi cike da faribciki yace "Woaw ashe inada k'anni dayawa" Duka falon sukasa dariya, waya Abba ya d'auka ya kira Areefan tana d'auka ta fashe da kuka tana shagwab'an barinta da akayi ita kad'ai, Abba ya soma lallashinta sannan yace gobe tasa driver ya kawota zaria idan suka iso sai ta kirasa. Cikin wani irin ihun murna ta amsa tare da kashe kiran. Har lokacin Ammi bata daina kallan Ummy bah wacce kanta ke k'asa tana ta murmushi, Ram yace "Bilal kayi hak'uri akan abinda ya faru, rashin sani neh" Bilal yayi saurin girgiza kai yana 'yar murmushi "Babu damuwa, rashin sani ne ai" Jamal ya sake bashi hak'uri, nan ma ya nuna babu damuwa. Sannan ya mik'e ya musu sallama dan zaije gida, driver Jamal yasa ya d'aukesa ya kaisa gidan bayan ya masa kyautar kud'i yaki karba. Gaba d'aya Jamal jinsa yake cikin wani irin farinciki, ji yake kamar an d'auke masa kaya. Mifzal da Ram suka musu sallama suma suka tafi, Jamal ya kalli Areef yace "Bro zo ka tayani wani aiki" Ba musu Areef ya mik'e yabi bayansa, Mabrookah na ganin sun fita ta mik'e tana wani cin magani tabar Falon, Ammi ta kalli Ummy tace "Tashi kije abinki Ummy Allah ya miki albarka" Cikin jin kunya ta amsa ta mik'e ta musu sallama cike da girmamawa. Ammi ta kalli Abba bayan Ummyn ta fita tace "Yau na fara ganin yarinyan nan, anma wallhi ta shiga raina sosai" Abba yace "Nima haka wallahi, kum daga gani tanada natsuwa da kamun kai" Ammi ta gyad'a kai tana murmushi. Mabrookah na fita taga Jamal da Areef sun shiga side d'in Mami, harta juya zata koma nasu side d'in sai kuma ta juyo tabi bayansu. Suna shiga Jamal yace "Wannan side d'in Mami ce itada wicked Sistern tah. Inaso ka tayani mu fitarda komai na ciki inaso Ammina ta dawo nan" Karaf a kunnen Mabrookah wacce take k'ofar falon tana kallansu fuska a had'e, ta k'araso ciki dasauri tana huci "Wallahi bazai yuwu ba Ya Jamal, me kake nufi a fitar da kayan Iyayena asa wani" Ya juyo ya kalleta rai b'ace "Saboda masu gidan wanda suke da iko da komai na gidan zasu dawo nan da zama" Areef ya haura sama abinsa yana tab'e baki dan kallo d'aya yama Mabrookah d'azu yaji sam bata masa bah, "Babu wanda ya isa ya fito min da kayan iyayena, kaje ka aro iyaye ka kawo to wallahi bazai yuwu bah, wad'an nan mutanen basu isa su..." Lafiyaiyan mari taji a fuskanta ta d'ago idanunta da sukayi ja tana kallansa da b'acin rai tana nuna kanta da hannu "Ya Jamal ni ka mara akan wad'an nan banz..." Wani marin ya sake d'auketa dashi ta fashe da kuka tana gagaya masa bak'aken maganganu, Areef ne ya sauko d'auke da Manyan Trolleys guda biyu yana jansu da kyar, ta k'arasa ta sauri ta rike akwatunan "Ina zaka kaisu, wallahi karka sake ka fita dasu" Jamal ya kira sunanta cikin kakkausan murya "Ki shiga taitayinki Mabrookah, ina raga miki ne kawai saboda Alk'awarin dana d'aukan ma Abba bazan rabu dake bah. Karki sake ki kaini bango" Areef iyayen k'eta ya d'anyi dariya ya fisge Akwatin yayi waje, ta k'arasa inda Jamal d'in ke tsaye tana kallansa hawaye na fita daga idanunta "Ka cika butulu Jamaludeen, kai butulu neh, ko me Mami da Mommy suka maka bai kamata ka sakamusu da haka bah, Kai butulu ne" "Karki k'ara kirana da butulu" "Na fad'a kai Butul..." Wani irin shak'a yakai mata dan gaba d'aya takaisa bango ta saki k'ara a wahalce idanunta gaba d'aya sun fito, Areef ya shigowa yaga abinda ke faruwa ya fita dasauri zuwa inda su Abba suke ya shaida musu, a tare suka taho dukansu da sauri. Har lokacin Jamal na shake da ita idanunta duk sun bulluk'o tana kakari kamar zata shid'e "Ban kira Mami da Aunty Faty butulu ba saini zaki kira da butulu, sun kashe min Abbana, sunyi k'okarin kashe min Matata dani kaina, duk wad'an nan ba butulci baneh, bariiii" Abba ya shigo falon tare da kiran sunan Jamal da k'arfi "Jamal! Ka saketa karka kashe musu 'ya" Ya sake mak'ureta idanunsa sai lumshewa take tana cigaba da kakari "Barin kasheki sai ki kirani da butulun da huja" Luuuu tayi zata fad'i Ammi ta k'arasa ta rik'e hannunsa tana hawaye "Ka saketa Jamaludeen, kar zuciya tasa kayi abinda zaka dawo kana danasani" K'in saketa yayi, Abba gaba d'aya ransa ya gama b'aci "Ashe Bamu isa mu hanaka abu ka hanu bako" Ya juya baya fuskansa ba walwala "Hakan ya nuna mana bamu da iko akanka" Sakinta yayi ta fad'i Luuu ta sume a wajan, baga d'aya fuskansa da idanunsa sun koma ja, Ammi ta rik'o hannunsa tana hawaye "Kome ta maka bai kamata kayi mata haka bah" Taja hannunsa ta zaunar dashi sai huci yake kamar zaki "Areef samo masa ruwa" Ruwa ya d'ibo a dispensern dake falon ya mik'a mata ta ba Jamal d'in, ba musu ya kafa baki ya shanye tas yana sauke ajiyar zuciya Abba ya k'arasa inda Mabrookah ke kwance ya yayyafa mata ruwa ta sauke ajiyar zuciya a wahalce tana kakari, dakyar ta mik'e tana rik'e da wuyanta ta fita daga side d'in dasauri. Ammi tace "Areef wai meya faru neh" Nan ya karkace ya labarta musu duk
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82