Skip to content

Chapter 20

Chapter 20

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

Ta sake dubanta tace "Ba ruwanki da Jamal ko Mabrookah, ki tsaya a matsayinki. Banasan shiga sharo ba shannu" Banbara kwayi Ummy taji maganan, ta amsa da to a takaice sannan ta mik'e ta haura sama. Jikinta a sanyaye tayi ayukanta duka ta koma kicin ta had'u da Laurat, sai a sannan ta tuna yau Laurat d'in zataje ganin gida. Nan hankalinta ya sake tashi idanunta suka ciko da kwalla, da taimakon Ummyn Laurat ta had'a kayanta, Ummy ta rik'o mata kayanta suka fito haraban gida. Daidai lokacin da Jamal ya fito daga Falon, Laurat ya hango Ummy na biye da ita tana hawaye. D'aya daga cikin ma'aikatan yasa ya kira mai su, tsayuwa Ummyn tayi tak'i motsi da kyar Laurat taja hannunta suka k'arasa inda yake tsaye. Fuskan Ummyn yaketa kallo yana d'an murmushi ganin yanda ta had'e rai, Laurat ta d'an rusunna ta gaidashi ya amsa yana tambayanta inda zata, ba tareda b'ata lokaci ba ta amsa masa. Kud'i ya ciro a aljihunsa ya mik'a mata tayi godiya sosai, driver yasa ya kaita tasha. Haka Ummy tanaji tana gani Laurat ta shiga mota suka bar gidan tanata d'ago mata hannu. Wani kuka ne yazo mata ta fashe da kuka tayi hanyar Garden a guje. Kan Grass Carpet d'in dake malalle akan Garden d'in ta kwanta tana cigaba da kuka. A haka ya k'araso ya sameta, baice mata komai ba ya zauna kusada ita tareda tank'washe k'afarsa yana kallanta zuciyarsa na masa zafi. Sam bata lura dashi ba saida tayi mai isarta sannan ta mik'e zaune tana goge hawayen idanunta, ganinshi tayi zaune kusada ita har saida ta tsorata tad'an matsa kad'an tana kallansa da idanunta da suka kumbure saboda kuka. "Ummy meyasa kikesan kuka? Kiyi hak'uri ai zata dawo" Batace komai ba ta mik'e tana kakkab'e jikinta, harta juya zata bar wajan ya mik'e dasauri yace "Meyasa kike guduna Jaleelah" Da mamaki ta juyo suka had'a ido dan batayi tunanin yasan sunanta, damuwa ne sosai a fuskansa ya soma takowa zuwa inda take tsaye. "Baki bani amsa ba, meyasa kike guduna yanzu" Ya juya fuska idanunta cikeda kwalla tace "Kayi hak'uri ka daina bina, bansan na rasa aikina dan dashi muka dogara, idan na rasa aikina bansan yanda zanyi bah" Ta matse hawayen daya cika mata ido ta juyo tana kallansa ido cikin ido, abinda bata tab'a yi bah "Gaisuwa kawai ta wadatar a tsakanin mu, ka daina zuwa inda nake dan Allah" Ta had'e hannayenta biyu tana hawaye "I know Mami ce ko Mabrookah suka miki magana koh? ki kyalle maganan su Pls, Allah ne ya had'a mu kuma babu mai rabamu" Ya sauke ajiyar zuciya ya kama hannunta ya zaunar da ita shima ya zauna suna facing juna "Duk abinda Mabrookah ke miki ina sane, harda wanda ta miki baya, ki cigaba da hak'uri kinji" Tayi saurin janye hannunta daga nasa "Yakamata kaso abinda Mahaifiyarka da K'anwarka sukeso, ka rabu dani dan Allah, dan su suna tunanin ko soyaiya mukeyi kuma b..." Yayi saurin katseta yana girgiza kai rai b'ace "Mabrookah ba k'anwata bace..." Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:34 PM] ‪+234 703 981 8283‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 24 "Mabrookah ba k'anwata bace" Ummy ta d'ago ido da mamaki tana kallansa. Ya gyad'a mata kai "Bah k'anwata bace, Sistern Mami ce ta haifeta" Ummy ta jinjina kai cikeda Mamaki, yace "Ni kad'ai Mamina ta haifeni, banida yaya banida k'ani, shiyasa ta d'auko Mabrookah ta zauna tareda ita" Fuska yatsine tareda lumshe ido yana shafa sumar kanshi "Banasan zamanta a gidanan, i hate her" Itadai Ummy ido kawai ta zuba masa tana kallansa, ya d'ago suka had'a ido ta sakar mata murmushi, mik'ewa tayi shima ya mik'e dasauri "Ina zaki?" Baya ta juya masa ta soma tafiya tana cewa "Zanje ne na cigaba da aikina, ni zan chanji Laurat har sanda zata dawo" Bata jira mai zaice ba tabar wajan dasauri ta wuce kicin. Wanka Mabrookah ta sake d'auka ta sanyo wani Bak'in shadda dogon riga wanda yaji aiki Golden, saukowa tayi k'asa ta shiga kicin. Harda ita akayita shirye shiryen tarban bak'in, ranar Ma'aikatan kicin sunsha Masifa bama kamar Ummy har saida tayi kwalla. Cikin lokaci k'alilan aka gama komai aka zuwa a sababbin cooler aka kai dinning d'in sama. Ummy na ganin an gama ta koma d'akinta ta zauna, wuraren k'arfe biyu Mami ta dawo aiki itama ta soma nata shirye shiryen. Jamal na side d'in Abba yana bacci baisan wainar da ake toyawa ba a gidan. K'arfe Hud'u da rabi na yanma aka wangale gate d'in gidan, bak'ar mercedes ce ta shigo tayi parking a k'ofar side d'in Mami, Ummy dake jikin window sai bin motan take da kallo dan ba irin motan gidan baneh. Mabrookah ta fito a guje tana dariya cikeda farinciki. Wata 'yar dattijuwa ce ta fito daga gaban motan, kamansu d'aya da Mabrookahn, ta k'araso ta rungumeta tana dariya. "Oyoyo Mummy! Sannu da zuwa" 'Yan mata ne kyawawa suma suka fito daga bacl seat, kallo d'aya zaka musu ka gane 'yan biyu neh, suna sanye da Pink atampha d'inkin dogon riga, Mabrookah ta saki matar ta k'arasa ta rungumesu "Oyoyo Twins d'in Aunty" Suma suka rungumeta a tare suna mai farinciki, sakinsu tayi ta k'arasa ta rungume d'ayar matar da suke tare itama tana kama da Mami sosai. K'walawa Ummy kira Mabrookah ta fara bayan ta fito da Trolleys d'in dake booth d'in motan. Dasauri ta fito ta gaidasu, ta tura mata kayan tana hararanta "D'auka shi shiga dasu sama" Akwatuna hud'u neh, dakyar ta iya d'aukan Biyu ta haura dasu sama sannan ta dawo ta d'au biyu ta kai tanata haki dan kayan sunada nauyi sosai. Nan falon k'asa suka baje anata hira, sosai Mami da Mabrookah suka yi farincikin zuwansu. Mami ta sake kwallama Ummy kira ta fito dasauri ta k'araso falon, Abincin da aka kai Saman tasa ta sauko musu dashi dan sunce nan zasu zauna. Nan Ummyn ta soma zarya daga falon sama zuwa k'asa tana kwaso abincin. Tana gamawa d'aya daga cikin bak'in tace "Ina kika samo wannan yarinyan, ke haka ake bama mutane abinci bazaki zuba musu bah" Kanta k'asa ta tsugunna ta soma zuba musu d'aya bayan d'aya. Jamal ne ya shigo falon cikin takunsa na k'asaita, turus yayi yana binsu da kallo cikeda mamaki, dan baisan da zuwansu bah, twins d'in suka mik'e cikeda murna suka doso inda yake d'aya na cewa "Ya Jamal Sannu ya jiki" Murmushi ya musu ya kama hannuwansu suka k'arasa falon, mai kama da Mabrookah tace "Dole ka kallemu mana, tun d'azu muke gidan nan ka kasa zuwa ka gaishemu kuma bayan dan kai mukazo" Yayi murmushi ya zauna yana kallansu "Haba Aunty Faty bah haka baneh bansan da zuwanku ba wanda ya gayamin" Wacce aka kira da Aunty Faty tace "Ba wani nan kawai dai kace mulkin kane daka saba ya motsa" Murmushi kawai yayi ya maida dubansa ga d'ayar dake kusada Aunty Fatyn "Sannu Aunty Zainab kunzo lafiya" Tayi murmushi tace "Lapia lau ya jiki? Allah ya k'ara sauk'i" Ya amsa da lapia lau tareda maida dubansa ga Twins "Najma da Najwa kunyi girma fah, yaushe yaushe na ganku" Daidai lokacin Ummy ta gama serving d'insu

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82