Skip to content

Chapter 59

Chapter 59

Jamaluddeen Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

d'auka ya kara a kunnensa "Gobe k'arfe hud'u na yanma muke san kud'in nan sannan in cash mukeso" Hankalinsa tashe yace "Ina matata? Dan Allah ku bani ita zanyi magana da ita" Yayi wani dariya mai sauti yace "Matarka a nan cikin k'oshin lafiya a halin yanzu, idan har kanasan ran matarka sai ka kiyaye sharud'an da zamu gindaya maka" "Wani irin sharud'u nayi alkawari zan kiyaye matuk'ar zaku bani matata" Ya sake yin dariya yace "Ka kwantar da hankalinka, na d'aya bamaso ka saka 'yan sanda a wannan tafiyar, sannan kada ka sanar da kowa akan maganar daga mu sai kai. Kud'in da kuma zaka kawo kamar yanda na fad'a maka a baya in cash mukeso a cikin ghana must go. Gobe zamu kira mu fad'a maka inda zaka aje kud'in da kuma inda zaka d'auki matarka" Basu jira mai zaice ba suka kashe kiran, k'ara kira yayi jikinsa na rawa anma a kashe. Wani sabon kuka ya fashe dashi na tashin hankali musamman na tuna irin mak'udan kud'in da akeso wanda baida halinsu. Kuka ya dage yanayi bil hak'i da gaskiya ga wani irin yunwa dake cinsa. Ganin kukan bazai fishe shi ba yasa ya mik'e dakyar ya shiga toilet yayo alwala ya tada sallah. A police station kuwa, secret room aka kai Alhaji Ameenu, duk tambayan da Mifzal ya masa k'in amsawa yayi wai sai anzo da lawyernsa. Ganin zai b'ata musu lokaci yasa aka fita dashi aka kawo Bilal. Da wani kallan rainin wayo Bilal ke bin Mifzal yar ya zauna. Mifzal yayi folding hannuwansa yace "Bilal Tukur! Me ka sani game da kisan Alhaji Surajo" Bilal ya b'ata fuska yace "Waye kuma Alhaji Surajo" Kyakkyawan mari Mifzal ya d'aukesa dashi sannan ya chakume sa "Baka sanshi bah kuma ka aika yaranka suka kashe shi" "What the hell are you talking about" cewar Bilal ransa b'ace "Ranar Ashirin ga watan January da daddare an shiga gidan Alhaji Surajo an kashe sa, mai zakace game da wannan" Bilal ya sake had'e rai "Oho!" Mifzal ya saki murmushi mai sauti ya danna wani alarm sai ga wasu 'yan sanda guda biyu manya sun shigo, Mifzal ya sake kallan Bilal a karo na uku "Meyasa ka aika aka kashe Alhaji Surajo bayan bashi da masaniya akan Hatsaniyar dake tsakaninka da d'ansa" Yaja dogon tsaki rai b'ace "Ni bansan abinda kake magana akai bah" Tafi Mifzal yayi, 'yan sandan da suka shigo suka soma dukan Bilal da kulki iya k'arfinsu, Ihu da kururuwa babu wanda Bilal beyi bah, Mifzal ya dakatar dasu ya sake matsowa inda Bilal d'in ke zaune kan kujera, wayan da sukayi ranan bayan rasuwan Abba ya saka masa yaji yace "Me zakace game da sak'on nin da kake tura ma Jamal da kuwa wannan wayan da kukayi dashi ran nan" Cikin Kuka Bilal yace "Bani da wata masaniya akan kashe mahaifin Jamal" "Shi kuma wad'an nan sak'onnin da waya fah" Ya sake fashewa da kuka "Wallahi duk barazana ce kawai nake masa dan ya rabu da Ummy, tun fil azal ni nake san Ummy kuma munyi alk'awarin aure a tsakanin mu" Mifzal ya katseshi da cewa "Shine dakaga yak'i sakinta ka tura aka kashe mahaifinsa" "A'a Wallahi bani na tura aka kashe Mahaifinsa bah" Mifzal yayi murmushi ya sake bada oder aka cigaba da dukansa, sannan yace su tsaya. "Kana wahalar da kanka sannan muma kana wahalar damu, idan har kanasan kanka da arziki, ka tsaya kayi mana bayani" Iya rud'ewa Bilal ya rud'e duk jikinshi a farfashe sai share kwalla dayake "Iya gaskiyata na fad'a muku." Mifzal yace "Menene Alak'ar ka da Alhaji Ameenu" "Shekara d'aya da rabi da suka wuce ya tab'a tsinta na a hanya lokacin munyi hatsari, kasancewar ba mazaunin Nigeria baneh yasa ya tafi dani chan k'asar dayake da zama. A chan ya mini magani har na warke ina zaune a gidansa" Mifzal ya gyada kai yace "Good!" Ya kalli 'yan sandan dake tsaye yace "Lets all it a day, ku saka shi a Ceil, gobe ma cigaba daga inda muka tsaya" Ya fita daga d'akin ya koma inda Alhaji Ameenu ke tsare, "Alhaji Ameenu kasancewar ka babban mutum yasa bama san mu wahalar dakai sannan bama san duniya tasan halin dakake ciki" Rai b'ace Alhaji Ameenu yace "I told uh bazan tab'a yin magana dakai without my lawyer bah" Mifzal yayi murmushi ya bada umarni aka d'auko wayan Alhajin ya mik'a masa "Gashi ka kira Lawyern naka, muna jiransa gobe by 7:am" Ba tare da b'ata lokaci ba ya amsa wayan ya nemi layin Lawyern ya sanar dashi abinda ke faruwa. *** Kuka kam Ummy tasha har ta gode Allah, An kawo mata abinci ta kasa ci sai ma amai daya taso mata ta rasa yanda zatayi hakanan tayi a wajan rabi duk a jikinta. Tuni zazzab'i da matsanan cin ciwon kai ya rufeta har bata gani sosai, har lokacin tana nan a kulle kamar yanda take d'azu sai hawaye dake fita daga idonta. Wani matashi ne ya shigo d'akin datake ya aje mata abincin dare, sannan ya kwance mata baki da hannu ya tura mata abincin gabanta. Cikin kuka ta kalleshi "Dan Allah ku kaini gida, ban muku komai bah" Ogan ne ya shigo, saurayin ya mik'e ya fita dasauri, ya k'araso inda take yana murmushin mugunta "Gaskiya mijinki na sanki sosai, saidai idan har yayi yunk'urin b'ata mana budget ko yayi jinkirin kawo kud'in da mukace" Ya matso inda take zaune saitin fuskanta "Sunanki keda shi Gawa, dan an bamu umarnin mu kashe ku" Ta fashe da kuka tana girgiza masa kai dakyar "Dan Allah karku kashe shi, ni na yarda ku kashe ni a madadin sa dan Allah" Ta k'are maganan da matsanancin kuka. Ya saki wani irin dariya yace "Mu umarnin da aka bamu kenan mu kashe ku duka ke dashi koda an bada kud'in" Ya sake sakin dariya ya mik'e ya fita. Ta bisa da kallo tana kuka tare da kiran sunan Allah. •••••• Jamal ko ya dad'e yana kai kukansa wajan Ubangiji yana kuka yana rok'on Allah ya kawo masa d'auki akan abinda ke faruwa dashi har zuwa goshin asubah sannan ya mik'e dakyar dan shima kanshi ne ke wani irin sarawa ya fito daga side d'in ko tsoron dare bayayi. Side d'inshi ya shiga ya haura zuwa d'akinsa, Diary d'in nan yaci karo dashi a kan gado ya k'arasa ya d'auka ya bud'e page d'in daya tsaya ya cigaba da karantawa _Watan gaririya muka soma cikin anguwan da muke gashi dare nata yi bamu samu wajan saka hak'arkarin mu bah. Kwatsam munzo wucewa ta wani bola mukayi muka soma jiyo kukan Jariri a cikin bolan, cikin tsoro muka matsa, Jamila matata ya rik'o hannuna tace_ " _Gaske ne wanna kukan mutum neh_ " _Duk da ina cikin tsoro hakan bai hanani k'arasawa wajan bah, nan muka same KA cikin wani akwati kana ta tsaya ku....._ Cikin wani irin k'ara ya rufe diaryn ya fashe da kuka. *Toh Fah!* Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 10:54 AM] Ayshaaaaaa: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ _Salam Masoyana, kuyi min Afuwa jina shiru kwana biyu. Uzuri ne a gabana dts why, anma insha Allahu zan cigaba da posting kamar

Table of Contents

Chapters

82 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82