Skip to content

Chapter 96

Chapter 96

Abadan Book One Complete Hausa Novel 1,274 words 0 views Progress saved
Download Book

ta fincike laptop din a hannunshi ba saida ya dago ya zuba mata idanunshi ''me kuma nayi?,ai na daina kallon naki ko?''ya fada a shagwabe kamar qaramin yaro bata kula shi ba saida tayo shutting down fuska a hade cikin zuciyarta a tsinke tace ''saika tsagaita na gama gyara na tukun,baxaiyiwu ina gyaran kaya ana min janye janyen wani shirgin ba''ta fada tana canzawa computer mazauni nesa da shi idan banda jarumtae daya aro ya tabbatar babu abinda zai hanashi fashewa da dariya sai ya wayance da dora hannunsa guda daya kan tattausan sumarshi ''oh Allah na,mami na kin barni gashi ana nan ana gara miki ni'' shi da yayi maganar da ita kanta sai maganar ta soki zuciyarsu,tabbas ba kadan ba sukayi rashi da kewar uwa ta gari irin mamin πŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒ Sosai ta qaranta baccinta don tayi imanin babu masifar da addu'a bata da maganinta,tana samun nutsuwa qwarai da gaske saidai gaba daya hankalinta ya karkata ga abdallah da maryam yammacin ranar lahadi tana gida bayan ta kira baba uwaani,su biyu ne cikin parlour din,a yanzun kam da baya ga 'yan uwanta baaba uwani ce ta biyu wadda take shawara da ita ''amma hajiya tunanin da nayi,ba zamu zauna bamusan inda suke ba,mai zai hana mu nemi gidansu maryam ko suna da labarin inda suke?'' cike da gamsuwa mami ke gyada kai ''qwarai da gaske baaba,wannan shawara ce mai kyau,amma cikin ni da ke babu wanda yasan gidansu maryamu tunda a lokacin bikinta bamu samu damar zuwa ba tunda ya hade da na abdallah'' ''eh hakane hajiya,amma ai da hajiya ruqayya aka kai lefan maryam dinko,ina zaton ki tambayeta zata iya tuna gidan'' ''af,qwarai kuwa,bari nayi kiranta'' Cikin sa'a kuwa ta samu ruqayyan qanwarta ta tabbatar mata zata gane gidan,a nan suka shirya tafiyar nayan sallar la'asar don zata tsaya ta sallami mai gidanta zaiyi tafiya da azahar Su uku ne cikin motar hajiya bintun ruqayya sai baaba uwani,jifa jifa suke tattaunawa kan batun har suka isa unguwarsu maryam din,sukayi parking qofar gidansu kana suka dunguma zuwa cikin gidan Gidan yana nan yadda yake daga soro zuwa tsakar gidan suka fara sallama,inna hadiza dake kan tabarma a tsakar gidan ta amsa musu don babu kowa a tsakar gidan idan ka debe ita da huwaila dake kitchen tana fama da tuwon dare kallo daya tayi musu ta fahimci daga irin gidan da ta fito,don haka jiki na rawa ta miqe tana fadin ''lale marabanku,sannunku da zuwa''mami batasan wace ba amma ruqayya tuni ta tunata saboda diban albarkar data yi danar kawo lefe,sake karkade musu tabarmar da take kai tayi tana fadin ''bismillanku ko zauna,ko daga ciki zamu shiga?'' ruqayya ce ta karbe cikin tabe baki tana girgiza kai ''mama muka zo nema,maman maryam''turus tayi kamar bata ji abinda suke fada din ba,don ita har yau babu abinda ta tsana irin taga wani abu na ci gaba ya samu maman,har yau bata dauki izina ba,rayuwar maman kullum sake inganta take,don hindatu kadai tafi dukkan nin yayan da ita ta haifa wadanda duk suka dawo gabanta,daya ce gidan aure saboda rashin kyakkyawan training na zaman auren,hindatun bata bar maman nasu ta nemi wani abu ta rasa ba,ta sake inganta rayuwarta fiye da da,ta sani rashin adda maryam dinta ne a akusa da ta tabbatar maman ma sai ta fi haka,duk da a yanzun ma ko hasidin iza hasada sai ya daga mata qafa Shirun taci gaba da yi har sai da huwaila ta fito daga kitchen dinsu wanda zuwa yanzu hindatun ta gyara musu shi duk da maman ta bata girki ciki,tayi me saboda babanta da kuma huwailan wadda a yanzu ta saduda,tun ranar da aka gyara kitchen din inna hadiza tabar girki a cikinsa saidai tayi daga waje ''sannunku da zuwa''inji huwaila dake wanke hannunta bakin famfo ''yauwa,don Allah maman maryam tana nan?'' ''eh tana cikin daki ina tsammanin sallah take,ga dakin nata nan ku shiga''ta fada tana musu nuni da shi suka amsa kana suka shige ''an dai ji kunya wlh,an zama 'yar kora da haka za'a qare'' ''ba komai,don ma zama 'yar korar amina ai tafi minke,don qaruwar da nayi da ita banyita da ke ba''ta sa kai ta shige dakinta don tasan halinta idan ta tsaya sai su raba abun fada yanzu ba kunya take ji ba kan abun sallar kuwa suka taddata tana raka'ar qarshe,falon nata qal da shi yanata qamshin turare,koda can ma mai tsafta ce bare yanzu da babu kowa a dakin nata sai ita kadai,suna tsaye har ta sallame,duk da batasan kosu waye ba da fara'arta ta karbesu ''ya zaku tsaya ku zauna mana''ta fada tana miqewa tare da ninke abin sallarta sai data ajjiye musu ruwa da lemo kana ra dawo ta zauna mami nata kallon ta,take ta tuna mata da maryam dinta babu tantama ita tayo,kyau tsafta da kirki Sun taba lemon kana suka gaisa,mami ta dubeta ''nasan baki sanni ba hajiya''murmushi tayi ''gaskiya kam,ban gane fuskar ba'' ''nice mahaifiyar abdallah surukinki'' Sabuwar gaisuwa suka sake yi da mamin cikin mutunta juna kana daga bisani mamin ta gabatar mata da abinda ke tafe da su,sosai mama taji dadi don ko mamin bata fada ba takowar da tayi ta fara neman yaran ya tabbatarwa mama sihirin dake jikinta Allah ya kawo lokacin karyewarshi a nutse mama ta gaya mata inda su maryam din suke,fadar irin dadin da mamin taji bama ita kadai ba harda baaba uwani bata baki ne ''ba shakka gobe zan je na dauko yarana,alhmdlh Allah na gode maka'' a take ta daga waya ta kira baffanta ta sanar masa,cewa yayi ta jinkirta zuwa goben,don bai kamata kai tsaye a dawo da su din ba,akwai abubuwa da ya kamata mafin dawowar tasu,baya ga haka magani yake karba,ta bari nan da wasu yan kwanaki idan ya gama tsara komai zai mata maganar Bata musa din ba saboda tasan baffab akwai hangen nesa,cikin farinciki da zumudi suka baro gidan zuciyoyinsu fal farinciki da godiya ga Allah,ba qaramin qimar mama mami ta sake gani ba data hada diyarta da danta ta kaisu ga mafaka cikin ikon Allah,sosai ta kuma ganin qimarta πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚ Washe gari hisham ya shirya don komawa katsina,yanason duba company din abdallah guda biyu dake can wanda abdallan yace a fidda wa ma'aikatan companies din salary dinsu tunda wata yazo qarshe Kai tsaye ya isa dakin tsoho alhaji wanda dama abdallah na ciki suna tare bayan gama shan rubutunshi wanda ya zama shine ruwan shansa a yanzu,yana duqe gaban tsohon ''banda abunka hisham tafiyar dare ai sam bata da dadi,da ka jinkirta zuwa gobe''cewar tsoho alhaji da yaje yiwa sallama,murmushi yayi kanshi a qasa ''banso komawa ba ma malam,naso naga yadda jikin abdallah zai kaya duk da yanzun ma alhmdlh yana gayamin yana jin canji a jikinsa,tafiyar ce ta zo min haka amma insha Allahu kwana uku kawai zanyi na dawo'' ''to shikenan Allah ya tsare hanya,a gaida manyan'' ''ameen ameen,Allah ya qara girma''ya fada yana miqewa,ya juya ya miqawa abdallah hannu suka yi musabaha,inna wuro ta shigo da jarka biyi daya man shanu ne a ciki daya nono tace ya kaiwa gwaggonshi,godiya ya mata sosai kana suka juya dukka zasu rakashi bakin motarsa hannunta taji an riqe da sauri ta juyo,abdallah ne,ya wani narke yana mata wani krin kallon dake sake

Table of Contents

Chapters

138 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138