Skip to content

Chapter 72

Chapter 72

Abadan Book One Complete Hausa Novel 1,264 words 0 views Progress saved
Download Book

baku dama ku gaggauta warware harqallar da kuka qulla dani'' ya juya zai wuce adnan yasha gabansa cike da taurin kai da jin shima karansa ya kai tsaiko yana ciccije lebe cikin son nuna shima jan wuya nebayan shi kansa yasan fanko ne lamba daya,kafin yace komai yasa kan wuqar hannunshi ya daki kanshi saiga adnan din a qasa,ihu nene ta saka tayo kansu,da tsinin wuqar ya juna ta ta koma baya tayi luf sai da suka kammala ficewa ta saka kururuwa ta biyo bayansu ko Allah zaisa taci sa'a wani daga cikin security din sun dawo suyi ram da su,saidai ina,babu wanda ta samu bakin get din kamar yadda ta watsa su don gabatar da aikinta πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚ ta kai ta kawo tayi hakan ya kusa sau goma sha biyar,ji take kamar zata hau bori ko hauka kafin ta samu guri ta iya tsugunnawa,ta dubi adnan da kanshi yasha dauri da bandeji da zaharkyya wadda ke zaune tana faman hade fuska,babu wanda take ganin laifi sama da nene,don ita kam ta gaji da wanna jeka ka dawo din,ta riga da ta yanke ma kanta hukuncin abinda zata aikata matuqar wannan karon haqarsu bata cimma ruwa ba kamar sauran lokutan baya ''babu shakka cikin hisham da maryam akwai wanda ya fidda abdallah daga cikin gidan nan,ko kuma daya daga cikinsun ya aikata hakan,kuma nafi zargin wanna shaidaniyar ce marya,tabbas kuwa''ta fada tana guada kai hadesake tabbatarwa kanta ''qwarai kuwa nene,nima na zargi haka tunda kinga fitarsu ana gobe za'a gudanar da aikin,cikinsu akwai wanda yake da hannu kan tsirar abdallah''inji zahariyya,shikam adnan ya kasa magana ta kanahi yake,tsanin ciwo yake masa kamar zai tsage gida biyu har zumbur nene ta miqe tana fadin ''wallahi basu isa ba dukkansu,duk wanda yaci tuwo da ni miya yasha'' πŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒ Tana cikin kitchen tana qoqarin hada masu abincin rana ta jiyo hisham na qwalla mata kira,cike da mamaki ta ajjiye abinda take yi din ta fito don bata taba jin ya mata makamancin irin wanna kiran ba tashin hankali ta gano qarara cikin idanunshi ''dauko duk abinda kika san kina da buqata ki sameni a mota na riga da na kai andallah ciki,babu lokacin bayani na miki shi a hanya'' bata tsaya tambayar ba kuwa,ta koma kitchen din a gurguje ta kashe gas din ta ahiga dakinsu da suka sauka ta dauki iya abinda take jin zata iya buqata ta fito ta taddasu cikin mota Tafiya yayi ta kusan mintina hamsin har suka fara barin ainihin qwaryar birnin kano sanna yayi parking a nutse ya dubeta ''maryam,na samu bayanan sirri daga daya daha cikin security din gidansu abdallah wanda nake biyanshi bayan barinmu yake samin ido kan duk wani motsi da yanayi da gidan ke ciki,don na tsammaci dama lallai wani abu na iya faruwa kan barinmu gidan da abdallah da mukaui,hasashena kuwa ya tabbata ya zama gaske iya,suna na ne ma farko cikin jerin mutanen da nene ke tuhuma,don ta saka amata bincike kan inda nake,yanzu haka mutanen na kan hanyarsu ta zuwa gidana,dalilin barowarmu gidan kenan'' kuka ne ya qwacewa maruam,wannan wace iriyar mace ce nene?me ta dauki rayuwar duniya,baza'a mutu ba?dawwama kowa zaiyi yana abinda yaga dama?,me take nema ne cikin duniyar da dukkanta bata kai qima da darajar fika fikin sauro ba agun Allah,wanne jin dadi ne a ginta ta kashe ran mumini wanda qimatsa tafi ka'aba agun Allah?,tana tsammanin idan ta aikata hakan taci bulus ne ko kuwa,zata taira daga hisabi da zabar Allah ne?dukkan amsar itace a'ah,babu ''a halin da muke ciki maryam kuka babu amfanin da zai mana,ki tsaida kukan mu nemi mafita'' tabbas maganar hisham haka take,ba bata lokaci ta ciro wayarta ta sake kiran mama wadda basu yi awa biyu da yin waya ba,magan sukayi ta kimanin minti talatin da ita kana ta kashe wayar ta dubi hisham kasancewar handsfree ta saka yaji komai kansa ya gyada ''maganar mama gaskiya ce,kuma tsarin nata yayi,nima da mun isa gobe zan wuce katsina hometown namu''ya fada yana mai gamsuwa da bayanin maman yana kuma sawa motar key,ta juya ta sake kallon abdallah har yanzu idanunshi a lumshe yake,babu baki balle ya bayyana abinda ke cin ransa,ta tabbata ba magana daya ke dawainiya da zuciyar abdallah ba,suna da dama,koda bao jude idonsa ba,koda baiyi,magana ba tana ki a jikinta zuciyar abdallan a quntace take,takan tashi kokawa afili da boye duk da shi din tsananin jarumtarsa bai taba barinta taga hawayensa ba Da taimakon bayanin da mama ke masu a waya suka kai ga isa qauyen NI'IMA dake cikin qauyen gaya,tun daga shigowarka garin zaka bawa kanka amsa,tabbas qauyen yaci sunanshi ni'ima,qauye ne da Allah ya wadata su da yawaitar korayen shuke shuke qoramu dabbobi da lullumi ma'ana rashin haske da zafin rana duk da haka sai da sukayi tambaya kafin su kai ga isa ainihin gidan da suke nema,gaya garin kakanninta ne tana zuwa lokaci bayan lokaci saidai qauyen ni'ima din zata iya irga iya adadin zuwanta tunda bata da wani shaqiqin da zata zo gunsa face wannan tsoho qwaya daya da yake qanin kakanta *mrs muhammad ce*πŸ‘‘ πŸ“šπŸ“šπŸ“šβœπŸ½βœπŸ½βœπŸ½ [6:27pm, 9/22/2017] HugumaπŸ‘‘: πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’– 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺 πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’– 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 πŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ πŸ’–πŸŒΊπŸ’– πŸŒΊπŸ’– πŸ’– *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’– πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’– πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ πŸ’–πŸŒΊ πŸ’– Β© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*πŸ’‘ *_home of expert and perfect writers_* β–Ά4⃣5⃣ *_Mazan Allah S A W yace:ku umarci 'ya'yanku da yin sallah suna da shekaru bakwai,sannan ku dakesu saboda ita idan suka kai shekaru goma,kuma ku rarraba musu gurin kwanciya(ma'ana ya zama gurin kwanan maza daban gurin kwanan matan daban yayin da suka cika shekaru goma)_* Gida ne ginin qasa kamar yadda yake kasancewa ginin gidajen qauyuka,saidai wannan ya dan banbanta da nasu damin uasha shafe da ruwan makuba,hakanan ginin sumul sumul yake sakamakon fulastar kar qasa da aka yi masa da kuma makubar da akabi aka shafe ginin da ita. Maryam ce ta fara shiga,kamar yadda muka sani yan uwanmu na karkara basa gini quntatacce hakan ce ta kasance ga wannan gida,babban tsakar gida ne mai girma wanda babu sumunti a qasan sa,turbaya ce saidai ta sha shara fes da ita,ga alamun shatin tsintsoya ne,daga can quryar katangar gidan garkene na dabbobi dake a tsaftace shima,sai rijiya daura da shi wanda lema ce duk a bakinta da tukwanen qasa da aka kikkife da alamu wanke wanke aka gama agun babu jimawa. ta sake yin sallama kin shiru ba'a amsa ba karo na uku,cikin daya daga dakuna hudin dake jere taji muryar matashiya na amsa mata,ta fito sanye da roga da zani na atamfa wadan da suka danyi haske saboda dan jimawar da sukayi a duniya,maryam ta duba itama ta kalleta ''don Allah inna wuro fa?''maryam ta tambaha,sai ta juya ta kalli dakin kana ta kalli maryam ''tana ciki salla take amma yanzu zata....''' ''wake sallama ne mero,a shigo mana'' muryar inna wuro ta katsesu ''inna wuro baqi kikayi'' ''kaddai ace su meramu ne har sun iso haka da wuri''ta fada tana yunqurin fitowa,kasancewar ta san zasu zo din mama ta kirata awaya ta mata bayanin zasu zo din ta wayar mustafa jikan gidan. hannunta dauke da tabarmar kaba sabuwa dal ta fito,dattijuwa ce wadda aqiyasce zata doshi shekaru sittin,tsaf da ita cikin cikin atamfar itama da hijabi ruwan madara,fuskarta ta fadada da fara'ar ganin maryam

Table of Contents

Chapters

138 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138