Chapter 25
Chapter 25
ita,ta tabbatar da cewa rayuwar cikin gidan akwai wani qulli da su su mamin basu san da shi ba,fargabarta daya kada wani abu ya samu abdallah ta sanadinta,idan ta fada wannan shingen wazai fiddata bata da wannan gatan saidai yadda Allah kawai yayi da ita har kusan uku na dare ta kasa runtsawa,sai da wayarta ta buga alarm na qarfe uku da rabi wato dai dai lokacin tashibta sallar dare kenan sanna ta shiga toilet ta daura alwala kusan dadewarta ta yau tana addu'a tafi ta kullum har sai da kiran assalatu ya rusketa,sallar asuba tayi ta dora da azkar zuwa qarfe bakwai ta fita kitchen sam jikinta babu kuzari kamar yadda zuciyarta babu dadi,fuskarta kadai ka kalla ta isheka amsa saboda ja da ta hada da kuma tasawa da idanunta suka danyi,a kasalance take hada musu break din wanda ya kaita har qarfe goma bata kammala ba saboda rashin qwarin jiki goma da minti ashirin da shidda ta ji sallamar mami cikin kitchen din,a hankali ta dago tana amsa mata kafin daga bisani ta rusuna ta gaidata bata damu da amsawa ba ta dora da tambayar maryam din cikin fuskar rashin jin dadi ''maryam,lafiya?,me ya samu fuskarki?,kada kice min kwanan kuka kikayi?,abdallah ne ko?'' zuciyarya ta danyi rauni amma sai ta dake,ta dan murmusa kadan hadi da kada kanta ''ko baki fada ba na sani shine,kiyi haquri kinji maryam na mishi fada kuma insha Allahu haka ba zata sake faruwa ba,ni zan fita,ga wannan albashinki ne na wannan watan''ta fada tana zaro rafar kudin daga jakarta sababbi kar da su hannu biyu ta saka ta amsa sanna ta mata godiya ''nice da godiya maryam,inajin dadin zama dake,kina da kyawawan halaye da mutane da dama suka rasashi a wannan lokacin,fata na Allah ya baki miji na gari maryam wanda zai riqekibisa gaskiya da amana'' kunya maganar ta bawa maryam wanda yana daya dqga cikin halayenta dake burge mami lura tayi da akwai magana a bakin maryam din ''kamar kina son cewa wani abu ko?'' ''dama yau inason inje gida ne'' ''hoo,maryamu,wannan din ne kika kasa fada,banda abunki ai kinyi kara ma wata guda baki gansu ba,babu matsala zan yiwa driver magan ki shirya sai ya kaiki idan zaki dawo ki masa waya yazo ya daukeki,idqn baki dawo da wuri ba ma babu damuwa ni da wuri zan dawo gida yau in yaso sai na mana dinner dinko,ki gaishemin da mutanan gidan da kyau kinji,zan ajjiye miki saqo a parlour idan kin tashi tafiya ki tafi musu da shi'' godiya sosai ta yiwa mamin tare da yaba karamcinta,tana kammala breakfast din ta shirya a gurguje cikin baqar abaya wadda ta sake fidda sirrin kyawunta ta kuma haska farar fatarta wadda ta sake fresh saboda zama gu daya da kuma sanyin a.c,kitchen ta koma ta juye duka patatoes balls din cikin leda bag ta daure ta jefa shi cikon jakarta,sai da ta tabbatar ta qulle duk inda tasan idan an shigo shi za'a iya samun matsala gun abinci ko abunsha da zasuyi amfani da shi sannan ta fita,hatta da breakfast sai data nemi alfarmar baba uwani ta kula da shi kafin abdallan yazo yaci cikin motar ta zaro wayarta ta lalubi number din raliya,har tayi ringing ta katse ba'a daga ba sai da ta sake kira,bugu daya ta daga ''sorry sis,fadil ne ya rudani da kuka na kasa daga kiran''sama sama suka gaisa,tana shirin tsokanarta taji muruarta ba yadda ta saba ji ba sai kawai ta share tambayarta tayi zata iya samun nasir abban fadil a asibiti ko bai fita ba ''tun dazun ya fita,ina tsammanin ma yakai awa uku acan''godiya ta mata ta kashe wayar,kamar ta tambayeta lafiya?sai kuma taga bai kamata ba,idan da buqatar taji maryam ba mai boye mata bane,a mutunce ta cewa driver din zooroad zasu fara zuwa ya amsa mata sanna ya sauya akalar motar *mrs muhammad ce [9/17, 12:52 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺🌺 🌺💖🌺💖🌺 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 🌺💖 💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖 💖🌺💖🌺 🌺💖🌺 🌺💖 🌺 ▶2⃣1⃣ _yar fadakarwa_ _*shin ko kinsan gwalagwalan kwanakin da muke ciki 'yar uwa?,kwanaki ne masu matuqar tsada da daraja har agun Allah madaukaki,kwanaki ne da ayyukan alkhairi suka fi soyuwa agun ubangiji a cikinsu,kwanaki ne mafi daukaka cikin kwanakin shekara,an karbo hadisi daga imamu bukhari r.a,annabi s.a.w yana cewa(babu wasu kwanaki da kyawawan ayyuka sukafi soyuwa agun ubangiji kamar kwanakin goman farko na watan zulhijja,sahabbai suka ce da annabi hatta jihadi saboda Allah?,annabi yace eh har jihadi,saidai mutumin da ya fita jihadi da ranshi da dukiyarshi bai dawo da komai ba),shin me kike aikatawa na neman lada?,kada ki yarda su shude ba tare da kin amfana da komai ba,baki da tabbacin ganin na wata shekarar,Allah ya karbi ibadun mu yasa mu dace ameen*_ 🕋🕋🕋🕋🕋🕋🕋 Minti talatin suka isa asibitin da nasir ke aiki,ta taradda marasa lafiya da suka rigata zuwa,hakan yasa tabi doka itama ta hau kan layi,don ta sani indai tace masa ta zo babu makawa sawa zaiyo ta ahiga kawai ita kuma ba zata so shiga haqqin wani ba ko kafin azo kanta tuni ta qosa,jira ne na tsawon awa guda da rabi kafin ta samu shiga,da mamaki yake dubanta tare da fadin ''yau kuma an tuna da mu kenan'' dan qaramin murmushi tayi kan ta haye kujerar da masu buqatar ganinshi ke zamansa gaisawa sukayi yaso ya dan tsokaneta yadda auka saba sai kuma ya fuskanci yanayonta ba yadda ya saba ganinta bane madaidaiciyar handbag dinta ta zuge ta fidso da leda bag din ta dorata saman table dinshi ''taimako nake buqata daga gurinka nasir ko zaka iya yimin shi?'' ''me zai hana maryam indai ba kaucewa addini ba'' ''abunda ke cikin nan nake da buqatar a duba min ko akwai poising a ciki?'' ido ya dan zuba mata kamar mai buqatar qarin bayani,gganin bata da niyyar qara masa haske yasa ya kauda idonshi kana yace ''ok,ba damuwa,ga kujera can zauna bari na kira lab azo a dauka'' cikin mintina uku kacal wani matashi ya shigo sanye da farar labcoat ya dauki ledar ya fice mintina arba'in din da yayi kafin ya dawo jinsu tayi kamar awa arba'in ne,tuna ni babu kalan wanda bata yishi ba,dawowarahin tayi daidai da kammala ganin patiente da nasir yayi,hakan ne ya bawa matashin damar zama tare da miqawa nasir result din ya ajjiye ledar a qasa yana duban fuskar nasir din nuni ya yiwa maryam din da hannu kan ta taso idanunshi na cikin takardar,a sabule ta iso gaban teburin ta samu kujera daya cikin biyun dake gun ta zauna ''maryama....taya aka samu irin wannan mummunar gubar cikin abinci?,kinsan nau'in guba iri wannan bamu da ita ma sosai cikin qasar nan?,guba ce da ke iya kashe mutum cikin mintunan da basu gaza biyu ba,baya ga haka hatta da gawarka ma bata qyaleta ba sai ta narka duka kayan cikin mutum,dubi yadda ta maida wannan dankalin''ya mata nuni dashi dake cikin ledar da yasa matashin ya bude A hankali ta maida firgitattun idanunta kan ledar,dankalin ya zagwnye ya koma kamar ruwan kunu,hakanan gabaki daya kalarshi ta sauya zuwa kore da baqi,kumfa ce kawai ke tsattsafa a samanshi tamkar ya ahekara ne da sarrafawa ba kwana daya ba,wani irin tsoro ya sake kama maryam,da sauri
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138