Skip to content

Chapter 1

Chapter 1

Abadan Book One Complete Hausa Novel 1,272 words 0 views Progress saved
Download Book

 [9/17, 12:49 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖 🌺 *DA 'IMAN*🌺 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 *written by safiyya Abdullahi musa huguma* 💖💖💖💖💖💖💖 🌺🌺 🌺 ⏯1⃣ A hankali ta tsallako tatitin kai tsaye kuma ta shige dogon layin dake gabanta,ta dubi tsahon layin duk da yawan al'ummar da yake da shi a dade yake babu kowa tankar anyi shara,hakan baya rasa nasaba da irin ranar da ake kodawa kamar mutum yaa dora hannu akansa yace wayyo Allah sannu a hankali take ci gaba da tafiya tamkar mai tausayin qasa,a zahirance idan ka ganta sai kayi tsammanin ranar bata dameta ba saboda yanayin yadda take tafiya,saidai sam tana daga cikin wadanda rabar ma tafi gallaba,don har Allah Allah take taga ta isa gidansu,saboda leshin dake jikinta dinkin riga da skert da kuma dogon hijabinta mai hannu dake qara mata zafi wanda ya zamo too match ne da kaya jaka da 'yar jakar swagger dake maqale a kafadarta babu wata doguwar tafiya ta iso qofar gidan nasu wanda ke rukunin gidajen marasa wadata,duk da ginin bulo da bulo ne saidai bai samu arziqin fulasta ba bare a kai ga fenti,ta cire jakar kafadarta tana shirin shiga soron gidan idanunta ya sauka kan hauwa wadda ta cakare cikin kwalliyar atamfa,wani matashin saurayi ke fiskantarta wadda yanayin tsaiwar tasu kawai zai fahimtar da kai zance suke,dauke kanta tayi tamkar bata gansu ba don wannan dabi'a ta hauwan bama ita ba duka yaran gidan na bata haushi ta tsakiyarsu ta raba zata wuce kasancewar babu wata hanya sai ita taji saurayin na fadin‘’barka da dawowa antyn mu‘’ ‘’yauwa sannunku‘’ta amsa masa ba yabo ba fallasa tare da shigewa cikin gidan hauwa dake binta da harara kamar qwayar idonta zai fado ta ja wani matsiyacin tsaki ''gaskiya haruna kana bada ni wallahi,wai ksi me yasa kullum baka da,burin da ya wuce ka yarfani a gun wannan matar ne,me ma kake nufi ne ni fa ban gane ba'' ''yanzu laifi ne kulu don na gaisheda yayarki,kuma fa kin sani tana da kirki wlh,uwa uba ilimi da nutsuwa'' cike da masifa hauwa ta qwalalo ido ''iyeee,to ko zaka koma gurinta ne haruna,a gabana zaka dinga yaba wata uwar mata da ta shekare gaban iyaye aka rasa mai dauka?'' ganin hauwan ta hau da yawa yasa ya sassauto''haba kulu na,wata kai yake a gurina ai kema kin sani,ni mai zanyi da wata mace a duniya indai ba ke ba?'' duk da koda tan da yayi ta dade a kumbure kafin ta sauko ta yarda suci gaba da tadinsu sallama tayi tsakar gidan kamar yadda ta saba duk da ta san babu mai amsa mata matuqar ba mamanta bace a tsakar gidan ko hindatu,ile kuwa bata samu kallon arziqi ba bare na tsiya duk da inna hadiza dake zaune gabas da tsakar gidan nasu tana kasa wake da shinkafar siyarwarta cikin samirun da duka suka sha lamba,zaune kusa da ita kuma huwaila ce ke nata zarafin na qulla kunun tsamiya cikin farar leda tana lodawa a botiki bata fasa ce musu sannunku ba kamar yadda basu fasa ja mata tsaki ba tare da binta da harara har ta cire toms dinta ta kwashesu a hannunta don gudun samun sabani ta shige rumfar mahaifiyarsu ba da sallama,tana iya jiyosu sun fara sana'ar tasu wato yada habaici da baqaqen maganganu ''hmmm idan da ranka kasha kallo,kaje ka gama yawon dandinka ka dawo dakin uwa kayi zamanka'' ''kema huwaila idan banda abinki a banza suka qi aurar da ita?ba ana fasa musu kai da cewar kyakkya wa,bace 'yarsu?,ai dole su maisheta jari'' ''hmmm,Allah wadaran naka ya lalace kuwa,wataran kuwa za'a dire abun kunya cikin gidan nan,a juri,zuwa rafi da tulu debo ruwa'' duk sunajin abunda suke fada daga ita har maman tata,wanda idan da sabo tuni sun saba,saidai babu mai tanka musu,kan dadduma ta taradda maman tata,da alamu sallar azahar take abatarwa,saboda haka ta sabule jakarta ta ajjiyeta saman kujera hade da hijabinta ta sake yowa tsakar gida don,dauro alwala,har ta gama,alwalar tata basu fasa muna nan maganganganunsu ba,babu wadda ta daga kai ta kalla a cikinsu duk da irin suyar da zuciyrta ke mata da radadi,ta ajjiye,silifas,din da ta daura alwalar tana niyyar shigewa rumfar tasu isyaku dan wajen inna,hadiza ya tawo a guje hannunsa dauke,da kwanonsha cike da kunu,bata ankara ba taji shi yana bin skert dinta ziwa qafafunta,da,sauri ta kalli yaron dake tsaye qerere ya zuba mata ido tace''haba isyaku me yasa baku iya tafiya ne a hankali?'' baki ya murguda ya galla mata harara ''eh din,ba sai a koya min ba,ban iya ba,aikin banza taqi aure ta damu mutane cikin gida'' ranta ne yayi masifar baci,yaron da a qalla ta bashi shekaru kusan goma sha biyar shi zai tsaya a gabanta yana gaya mata haka,hannunshi ta,finciko ya qaraso gabanta,kafin ta aiwatar da komai ta jiyo muryar inna hadiza cikin kaushi da haya gaga tana fadin ''ke,kada ki kuskura ki taba min yaro wallahi,idan kuwa kika sake hannunki ya kai kanshi to zamu kwashi 'yan kallo dake wallahi'' bata saurari kurarinta ba ta yarfawa isyaku mari domin dama ko da,safe kafin ta fita sai da ya mata wata tijarar kuma tana kallo bata ce uffan ba sai dariya ma data sheqe da ita ,ai kuwa kanta tayo yana fadin ''kutumar uba,wallahi yau sai kin gane shayi ruwa ne'' gadan gadan ta nufota wand hakan yayi daidai da shigowar malam mamuda cikin gidan ''kai kai lafiya?'' ''yauwa malam gwara da Allah ya kawoka,wallahi mun gaji da zaman wannan balagaggiyar tsakaninmu,ita ba aure ba ita ba karuwanci ba,ta ishemu ta ishi yarranmu?''ya katseta da fadin ''to yanzu me kuma ya faru?'' ''wai wannan dan talilin yaro ta daddage ta zabgawa mari don kawai ya zuba mata kunu bai sanig bau,to wallahi ba zan yarda ba,ko ya rama ko ni na rama masa da kaina'' ''kai isyaku me yasa haka'' ''baba ban sani bane ba fa,kuma ni wallahi sai na rama'' ''ke *maryam* bashi haquri'' babu yadda ta iya haka tace kayi haquri shi kuma ya tubure ramawa zaiyi,da qyar uwar tasa ta lallabashi ya haqura hawaye na bin kuncinta ta shige dakin nasu,maman na zaune bisa daddumar yadda ta barta ko motsawa bata yi ba bare tasa baki a cecekucen da akeyi,bata ce da maryam din uffan ba kamar yadda itama batace din ba,ta dauki dadduma guda daya daga inda suke ajjiyewa ta tayar da sallah ta dade akai tana miqawa Allah kukanta kafin ta sallame,tana ninke sallayar ne taji maman tace ''na sha gaya miki maryam dole kici gaba da haquri matuqar dai kina zaune ne cikin gidan nan''wasu sabbabbin hawayen ne suka zubo mata,ta koma gefan daya daga cikin kujerun falon ta zauna tana fadin ''mama,ke kanki shaida ce akaina,amma duk yadda kakai ga haqiri wataran mutanen gidan nan sai sun saka kayi misbehaving,yanzu mama kamar isyaku fa qanin bayana mama?'' ''ya isa kada ki saka abun cikin ranki,Allah yana tare dake ba wai ya manta da ke bane'' cikin sanyi wanda ya zamto halittarta ta goge fuskar tata cike da tawakkali da miqa lamuranta ga Allah ''to mama''shine abunda ta fada a sanyaye *mrs muhammad ce* 📚📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻 [9/17, 12:49 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖 *ABADAN*💖 🌺💖🌺💖🌺 *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 🌺💖🌺💖🌺💖🌺 🌺💖🌺💖🌺 🌺💖🌺 🌺💖 🌺 *assalamu alaikum masoya,xaku ga nun canzs sunan littafin

Table of Contents

Chapters

138 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138