Chapter 12
Chapter 12
kyauta'' ''hmmmm,ameen bari naje maman fati sai anjima''maryamu tayi mata sallama ta fice bata tarad da haj atika ba,sai babanta da mama dake zaune ''baba gani''ya fada bayan ta samu guri gefe da su ta zauna ''maryam'' ''na'am baba'' ''ki shirya gobe idan Allah ya kaimu ki hada duka abunda kike da buqata hajiya zata zo zaki tafi gidan nan da kukayi magana da ita ta samar miki aiki'' cikin rashin fahimta ta dubeshi ''amma baba ni ina ganin koda zanyi aikin ma ai bani da buqatar tafiya da kaya na,tunda ba wani garin bane ko?'' ''ke,bani son sakarcin banza,na riga da na gaya miki,ki hada kayanki,suna da buqatar zamanki ne a can gidan,yo idan kin zauna anan din me zaki tsinana min,illa inyita ganinki baqinciki na ci gaba da damu na?,kije kawai banason kuna sauran qorafi kinji ko?'' kai ta gyada hawaye na layi bisa kuncinta,wannan sam bai dadashi da qasa ba ya miqe ya fice abinsa,kai ta hada da gwiwa ta rushe da kuka,duk yadda taso daurewa zuciyarta ta kasa ''wai me yasa baba baya sona ne mama,me nayi masa?''ta tambaya cikin kuka ''kul maryam,kada na sake jin wannan mummunar maganar a bakinki,mahaifinki ya isa da ke,saboda haka nima bana buqatar wani qorafi kibi umarninshi kawai'' bata iya cewa konai ba face miqewa da tayi ta shige dakinsu zuciyarta na zafi tare da jin tsanar wannan sabon aikin,aikin da zai nisanta ta da mahaifiyarta,zai nisan tata da 'yar uwarta,mama binta tayi da kallo tana jin tausayin diyar tata sosai na sauka cikin zuciyarta,addu'a kawai take mata cikib ranta Allah ya yanke mata wahala,ya kawo lokacin da zata zauna ta huta cikin dakin mijinta 🎄🌲🎄🌲🎄 jikinta duka a sanyaye take shirya kayanta cikin sabon dan trolly dinta mai kyau pink wato ruwan hoda,hindatu ce ta rufe mata sannan ta jawo mata shi cikin parlour don bata da kuzarin da zata iya janshi tsaye tayi cikin falon ta kasa cewa maman nata komai,don hawaye ne fal cikin idanunta da suya da zuciyarta ke mata,ji take kamar ta bar gida kenan,tana jin tamkar ta bar mamanta kenan,sai maman ce tace ''kuje hindatu jiranta suke,Allah ya bada sa'a,abu guda zan fada miki,ki riqe mutuncinki a duk inda kike,ki tsarw ksnki maryam ki kuma ji tsoron Allah,don babu wani abu da zan iya yi miki a lahira,iya kacin amfani na a duniya ne wajen tunatar da ke bin hanyar Allah,ki riqe amsna ki zauna da kowa lafiya'' kuka ta saki ta fada jikin mama,sai da taci kukanta sannan a sabule ta fice hindatu tabi bayanta da akwatin sam basu lura da su ba sai shewa suka ji,inna hadiza nw da binta har da tafawa kamar sa'annin juna ''haka dai za'a qare a boyi boyi''inji inna hadizar,hindatu na shirin maida mata martani maryam ta damqe hannunta ta jata suka fice ba tare da ta bata damar tsayawa sun taya yinsu ba *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻 [9/17, 12:50 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 🌺💖🌺💖🌺 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 🌺💖 💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 🌺💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖 💖🌺💖🌺 🌺💖🌺 🌺💖 🌺 ▶🔟 shiru tayi cikin motar tana maida ajiyar zuciya,zugi take jo tana yi mata har ga Allah da tana da iko ba zatayi aikinnan ba,sam bai kwanta mata ba ko kadan a rai ''maryam,kiyi haquri kinji,na fuskanci baki son aikin nan,amma ni mai sonki ce maryam,na yadda da tarbiyyarkk,ke yarinyace mai hankali da nitsuwa,idan da nasan zaki cutu a gidan wlh bazan gaba kaiki ba,ki kwantar da hankalinki na tabbatar zaki samu nutsuwa da jin dadi cikin gidan *haj hasiya*na da dadin mu'amala,insha Allahu ba zaki samu matsala ba,ki cire damuwa a ranki don Allah kinji maryamu'' ta sake sakin ajiyar zuciyar a bayyane ''to msma insha Allah''ita kanta tasan ta fada ne kawai amma Allah ne kadai yasan ranar daina damuwarta,bata taba rabiwa da maman nata ba sai yau tafiyar mintina kimanin talatin suka iso unguwar,tun daga farkon unguwar zaka gane cewa ba qananan muta ne ke zaune cikinta ba,daga get din farko allo ne mai dan girma dauke da rubutu kamar haka *welcome to millonier quaters* sannu a hankali suke ratsa layukan,layuka ne tsararru tamkar a qasar waje,shuke shuke ne jere reras qofar kowanne gida,hakan sai ya yiwa layin ado ya zamo cike da furanni,layin ya burgeta sosai,duk,da uadda,zuciyarta ke mata babu dadi qofar wani gida suka ja suka tsaya,dauke yake da madaukakiyar katanga da get mai tsawo da girma,horn tayi har kusan uku kafin wata qaramar qofa ta bude kallo daya zaka masa ka tabbatar cewa qaqqarfan mutum ne,sanye cikin kaya riga da wando ruwan bula wanda ke alamta unifoarm ne a jikinsa fuska a hade yake tambayarsu cikin karyayyen turancinsa na brooking ''wa kuke nema?'' haj atika ce ta amsa masa''gurin hajiya muka zo,ta san kuma da zuwan mu''ya sake tambayarta mene sunanta ta gaya mishi bai sake cewa komai ba ya wangale mamakeken get din motarsu ta fada ciki gurin parking ne wanda yake cike da motoci na alfarma a qalla guda goma,haj atika ta raba tata gefe kana suka fito,sunyi tafiya ta kusan minti biyar kafin su cimma dogon valcony din dake fuskantarsu wanda lullube yake da nau'in furanni kala kala masu qamshi da kyawun kaloli,qofa ce mai fadi cikin valcony din wanda suna shiga ta kaisu ga tafkeken falo wanda ya lamushe rukunin kujeru har set biyar saboda girmanshi iya qawatuwa an qawata falon iya ganin mai kallo,saidai kawai na barwa mai karatu ya siffanta shi iya yadda zai iya,shiru falon yake sai qamshin freshner da ya gauraye falon da na a.c _kuyi haquri da wannan don Allah,ku bini bashi gobe uxiri ya riqeni_ *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻 [9/17, 12:50 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 🌺💖🌺💖🌺 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 🌺💖 💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 🌺💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖 💖🌺💖🌺 🌺💖🌺 🌺💖 🌺 ▶1⃣1⃣ tsit falon yake tamkar babu kowa cikin gidan,da ido suke kallon falon tare da yin sallama koda zasu samu wani a akusa ya amsa musu,saidai har yanzu babu motsin kowa qofar dake hannun hagu suka ji an murda an bude,duk da 'yar tazarar dake tsakaninsu suna iya jiyo dariyar su,su biyu ne daya a gaba daya abaya matashiya ce 'yar kimanin shekara ashirin da biyar sai wata agefenta wadda zata iya bata shekaru uku basu kula da su maryam ba dake tsaye a tsakiyan katafaren falon ba har sai da suka zo daf da su,ta gaban ce mai kimanin shekaru ashirin da biyar din ce ta soma qare musu kallo,kallo ne na qurilla da saka tsarguwa,sai da ta gama tace ''mu je ko jidda na taka miki''ta fada tana kallonsu sama da qasa har zasu gota haj atika tace ''ji mana''ba tare data dawo ba ta waiwayo tana jirqn me zasu ce ''don Allah ko zaki mana magana da haj bintu?'' cikin halin ko in kula tace''ku zauna ku jirayi fitowarta,may be yanzu zata fito''daga haka tayi gaba abinta tare da jan hannun wadda suke tafiyar tare,haj atika tace ''zauna maryam,bari na kira hajiyar'' maganar second uku fayi da ita ta kashe wayar,cikin minti biyar katafariyar qofar dake hannun dama ta bude,kyakkyawar mace ce 'yar kimanin shekara talatin amma a zahiri ta kai shekara hamsin da uku,kyawun jiki iya ado da kwalliya hade da tsafta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138