Skip to content

Chapter 95

Chapter 95

Abadan Book One Complete Hausa Novel 1,277 words 0 views Progress saved
Download Book

nakeji game da ke cikin zuciyata kuwa''ya fada yana tura hannunta cikin qirjinsa bayan ya balle maballan rigarsa,take tafin hannunta ya mannu da fatar qirjinsa dake cike da gashi ''kina iya jiyo bugun zuciyata a haka?''kai ta gyada masa tana murmushi don tana jin yadda zuciyar tasa kera fat fat fat da sauri kai ya girgiza ''abinda kika ji yanzu baikai kaso daya cikin dari na yadda nakeji cikin zuciyata game da ke ba,idan da zan iya zuciyar zan ciro miki dungurun gun na ajjiye miki ita wata qila kya iya ganin kaso hamasin cikin darin abinda nake gaya miki,ragowar hamsin din sai ni da Allah'' qayataccen murmushi ta sakar masa tana sadda kanta qasa,da sauri yace ''dago ki kalleni da kyau maryamu na,kallon da kike min kawai na rage radadin da nake ji''bata musa din ba ta dago taci gaba da kallon nashi fuskarta dauke da murmushi ya matso kusa da ita har suna gwaren numfashi ''i love d look in ur eyes maryam''murmushi ta kuma yi tana dan kawar da idanunta ''i luv ur smile,maryam ke ta musamman ce u make me feel safe nd secure,ban damu da duk wani abu da na rasa ba idan ka cire mami na matuqar ina tare da ke,i know u luv me 4 who am,pls maryam tell me kina sona...kina son abdallah'' idanunta ta lumshe kana ta bude tattausan labbanta ''abdallah'' ''yes ina jinki'' ''abdallah ina.....'' ''umh comeon baby ina jinki'' ''abdallah'' ''na'ammmm'' sai taji amsawar ta qarahe tamkar ido biyu ne ba cikin mafarki ba,a hankali ta fara bude idanunta don tantance a inda take,yana zaune sosai kan kekenshi idanunsa akanta kamar wanda ya samu hoto,a firgice ta miqe ta zauna dirshan kan gadon innna wuron tana mutstsuka idanu ''me nayi miki da kika zo kina mafarki da ni?,kin daga mana hankali muna ta nemanki tun la'asar gaahi har magariba ta gota ana shirin yin isha'i ashe ke mafarkina na ma kika zo kina yi?''ya fada fuskaraa dauke da murmushi wanda sai ka kuka sosai zaka gane shi kwance kan fuskarshi haushin kanta ya kamata,kunya da taoro suka dirar mata,kada dai ace kamata yayi tana ambatar sunansa,kai amma kam da ya gama da ita,duk da ba haske bane tarwai cikin dakin sai data harareshi ''waya damu da kai da zaiyi mafarkinka? kai kadaine mai sunan?'' hannayenshi ya ware na alamun ba ruwana ''bani na kar zomon ba,ratayar ma ba'a bani ba,kuma ni din ma na dade da sanin ba'a damu da ni ba,tsabar haushina ne yasa kike ambatar suna na cikin mafarki cikin yanayi ma shauqi ko?''ya tambaueta tana tsatstsareta da kallon nan nashi,bata san me zata ce masa ba duk da barazanar kare kanta da takeyi ba,sai kawai ya juya kekenshi zai fita yana dariya qasa qasa ''ko yanzu kasuwa ta tashi dan koli yaci riba,na bada darasi abdallah ba rago bane,ki fadi abinda ke damunki idan ya kama taimako sai a taimaka miki''ya fice daga dakin,ba qaramin quluwa tayi ba,ya akayo ya sake ma ya kamata tana mafarkinsa,ta ciji yatsa tayi dana sanin ma yin barcin nan gaba daya,dole haka ta sauko daga gadon tazo ta wucesu suna zaune abinsu hisham tsoho alhaji inna wuro da abdallah,garwashi ne da wasu magunguna gaban tsoho alhajin wanda da alamu duka hade haden abdallah ne,taje ta dauro alwala tana jinshi yana basu labari ''gadonki taje ta naushe miki inna,taji laushin katifa tana ta mafarki barkatai,inaga alhaji sai ka bata magani ma don ina zaton akwai wani aljani abdullahi mai irin suna na da ya kamata''dariya ya basu yayin da ita kuma ta sake quluwa ta daura alwalarta ta wuce dakin inna wuron ta tada sallarta Cikin kwanakin gaba daya tayi qaura dakin inna wuro nan take kwana saboda hisham na gidan tare suke kwana da abdallan,iyakarta da tsakar gida ta fito ta taya inna wuro aikace aikace ta koma daki abunta,sam ta hana haduwar da abdallah duk cikin qoqarin tana hana kanta jin duk wani feelings dake barazanar kamata,kusan tayi a banza tunda ko shi bai ganta ba ita tana ganin giftawarsa ko ta jiyo muryarsa shi da su tsoho alhaji wanda ya duqufa ka'in da na'in wajen magungunan abdallah wanda alhmdlh cikin jikinsa yan jin wani irin sakewa da sukuni Ko daya inna wuro bata ce mata uffan ba kan zaman daki data aura,sai ta tuqe kana zakaji tace ''ummm,Allah ya kyauta,kowa dai ya debo da zafi bakinsa''ta fuskanci sarai da ita take cikon kwana na ukun tana kwance kan qaramin gadon inna wuron misalin uku na yammaci da littafin riyadul jannah a hannunta tana dubawa,yaye labulen inna wuron tayi tana fadin ''ki tashi kije ki gyara dakinsu hashimu,shida malam sun fita bayan gari debo ganye,amma fa idan zaki iya(da yake haka innan ke kiransa)'' ta fuskanci kamar da zafin ta innar ta fada,bata ce mata komai ba ta ajjiye littafin gefan gadon bayan ta saka alama,hijabinta ta,ciro ta ware ta saka kana ta fice innan ta bita da kallo tana tabe baki ''Allah dai ya sawwaqewa matan maraya wallahi''ta jita amma bata tanka ba tsaye tayi a bakin qofar dakin zuciyarta na wani irin bugawa,kamar ta juya ta koma haka ta dinga ji,fargabar shiga takeji,jin motsin futowar inna wuro daga daki ya sanyata yin saurin daga labulen ta fada dakin tare da sallama idanunta a qasa kan kujerar dakin wannan karon ta tadda shi zaune,yayi kyau cikin baqar rigar jallabiyya data haska fatarshi,a haka sai kayi tsammanin lafiyanshi qalau saboda kyan da yayi,ganinshin da batayi ba kwana biyu sai taga kamar an canza shi ne,wayarshi ce a hannunshi yana danne danne,da alama wani muhimmin abu yakeyi,amsa mata yayi kallon farko kadai yayi mata yaci gaba da abunda yake kamar bai santa ba tana kallon kan katifar da kaya ke baje a aki da sauran tarkace tace ''zan danyi gayaran daki ne'' ''oh,na bayar baki gidan ne har nasa a gayara din ma'' wani abu ya dan taba ranta sai tayi shiru wanda hakan yasanya ya dago kai ya saci kallonta qasa qasa taji yace ''if u luv some one be sure to hold them close,if u don't some one else will'' ''me kace?''ta fada cikin son nuna mishi bata ji abinda ya fada din ba ''no,ba dake nake ba,bismillah''ya fada yana ci gaba da abinda yake yi katifar ta soma kintsawa,tana aikin amma jikinta na gaya mata kallonta yake,batayi qarya ba don gaba daya ya bar hankalinshi daga kan wayar ya maida kanta,duk wani motsi nata na kan idonshi,cikin zuciyarsa hakanan yaji tana burgeshi,bai taba zaton zai samu macen da zaiso ta wofantar da soyayyarshi ba,bil haqqi da gaskiya take son nuna masa iyakarsa Wannan karon duk yadda yaso kauda idonshi kada ta kamashi yana kallonta abun ya faskara sai da suka hada ido,kamar kuma an manne idon ya kasa daukewa,ta juya ga zatonta zai daina kallonta amma sai taga yaci gaba,bata rai tayi ''gabana faduwa yake idan aka fiya samun na mujiya''murmushi ya sake yana janyo laptop dake gefansa ''ayyah am sorry''ya fada yana kunna system,bayan ta saitu ya shiga gun hotuna ya bude daya daga cikin hotunan ciki Gefanshi taje zata dauke abun sallar dake shimfide a gun idanunta ya kai kan system din,hoton mero ne ya cika screen wanda da alama shi abdallah yake kalla batasan

Table of Contents

Chapters

138 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138