Skip to content

Chapter 115

Chapter 115

Abadan Book One Complete Hausa Novel 1,277 words 0 views Progress saved
Download Book

ya lalace yana gaya mata yadda take da tasiri cikin zuciyarsairin girman matsayinta,da irin yadda yake ji game da ita,yadda sonta ya dade da illata zuciyarsa,duk inda ta duqa sai ya hanata,yace ta barshi yau ya bararraje ya fidda duk wani feelings da yake ji game da ita,daga qarshe tallafe kumatunta tayi tana kallonshi,tayi imanin ya zauce cikin so kamar yadda ita ta zauce,saidai tsakanin shi da ita batasan wanda yafi wani ba,sau biyar hisham yana kiransa yana katsewa,qarshe ma ya daga yana fadin ''kaga malam idan zaka kama hanyarka ka wakilceni shikenan,nikam a inda nake yanzu ko mami,nasan zata min uziri''da yaga yaqi daina kiran nasa sai ya kashe wayar baki daya ya jawo bedside ya wullasu ciki yana jan tsaki ya sake dawowa sukayi zaman dirshan saman gadon suna kallon junansu cike da shauqim bege da qauna Itama mamin ba ta nemi ko daya daga cikinsu ba kamar tasan tsiyar da abdallah ya qulla,cikin dakin sukayi sallar azahar har ma da la'asar,babu wanda yayi tunanin wani abu waishi abinci a cikinsu,wani irin shauqi ke dawainiya da su wanda gaba dayansu basu taba zaton akwai irinshi ba,a haka ma maryam na doddojewa saboda tsoro da gudun kada a tafka abun kunya cikin gidan suruka,ya qaraci fitinarsa sau biyu yana wanka tana kallonsa, Sai da suka idar da la'asar maryam tace ''ya kamata ka tafi haka,kaga kada mami taga rashin,hankalinmu''kamar ma ba da shi take ba sai ua dira kansa saman cinyarta yayi kwamciyarsa yana fadin ''babu rashin hankali,tsakanin miji da mata sai Allah ita kanta mamin ya sani,nasam ta mana uziri,uziri kam dole ne ayi mana musamman ni Allah sarki da na jima ina faman rainon soyayyarki tun kima qwaila''ya qarshe maganar cikin salon zolaya ta fara tura bakinta tana qoqarin tureshi ''ni daga ni,nikam ba qwaila bace ko a da dinma''yadda ta turo bakin ba qaramin sha'awa ya bashi ba,bai iya haqura ba sai da tsotseshi tas,abdallah na haukata ta iya yau da salon soyayyarshi tana zaton na gaba sawa zaiyi ta manta kowa da komai cikin haka sukaji ana knocking,aka rasa mai magana tsakaninsu,murya qasa qasa tana zare ido tace ''mami ce fa'' kafada ya daga ya ware hannunshi kana ya miqe ya nufi qofar,ido ta sake zarowa ta biyoshi da sauri tana roqonsa qasa qasa saitin kunnanshi kada ya bude sai yasa rigarsa ''sai na cire wanann ma na zauna da boxer ki da kanta ma idan mami ce anjima zata kaimu gidanmu''kunu tasha tana miqo masa rigarsa kana ta fece bandaki ta saka maqulli ta buya,bai kuwa saka rigar ba ya budewa mamin,ita kanta sai da taji kunya ta kamata,ta kautar da kanta sanan tace ''ba kai nake nema ba diyata nake nema,kasan bata gama warkewa ba akwai sauran magungunanta da zata sh'' shima sai ya hau sosa kai don ya gama fuskantar inda mamin ta dosa ''mami ki kawo sai na bata'' hararasa tayi gafara min ni na wuce,haka zaka dirka mata maganin bata ci komai ba tun safe?,baka iya kula da mutum ba sai sakarci ka iya''ba shiri ya matsa ma ta shigo,ta kalli gadon da suka yamutsashi don akai suka yini salla ke sauko da su ta dauke kanta tana kiran sunan maryam din,gyaran murya ta yiwa mamin kamar maiyin wani abu a bandakin sai ta samu gefan kujera ta zuan bayan ta ajjiye maganin kan madubi,shima gefan madubin ya jingina yana fadin ''kinsan kuwa mami cikin wadanda na kama tare da alhj hamza da yaranshi harda adnan?,mami ashe yana daga cikin manyan yaranshi,duka poising da naci sau biyu har da hadin gwiwar alhj hamza din''salati mamin ta saka tana tafa hannayenta ''kai Allah ka tsare mana imaninmu ya Allah,wadan nan mutane wadan nan mutane sun cika butulu,amma dama hausawa sunce idan zaka gina rakin mugunta ka ginasho gajere wataqila kai zaka fada,yanzu gashi su suka fada din,nene kam ba ita ba labarinta har yau ita da zubaida,yanzu don Allah meye ranar wanann?'' kanshi a duqe yake jijjiga kai,har yau yana jin takaicin yadda mutanen suka ci amanar mahaifinaa da mahaifiyarsa,har yau yana tuna yadda babanshi da mamanshi suka hada gwiwa aka auro nene gidan cikin halin qunci da wahala ita da yayanta amma yau da ita akayi yunqurin rusa su badon Allah baya bacci ba ya basu kariya da kariyarsa,kasa cewa komai yayi don idan ya tuna su bacin ransa ne ke tashi qwarai da gaske,badon mami tace ya qyalesu ba dukkanau sai ya nemo su yayi shari'a da su har igiya tayi saura,amma gashi a yau ya samu adnan wanda ko tantama baya yi hukuncin kisa ne zai rataya awuyansa sabida irin barna da kisa da suka dinga yi shuru shiru maryam bata sake motsawa ba,babu yadda mami batayi ta fito ba amma ta kasa,shi kuwa abdallah na gefe yana musu dariya,da mamin ta gaji tilas tace ''aishikenan gasu nan idan kin fito din kyasha,ki tabbatar da kinsha kuma sabidayau hajiya lailan tace kisha shi''ta juya ga abdallah dake masu dariya ''ka shiga tsakaninmu ko,zaka dara da kyau musamman idan na saka ranar tarewarku nan da watanni goma'' ''lokacin ta haihu kenan ta gama wankan jego'' 🙄,ya fada qasa qasa yana duban sama ''me kace?''mamin ta tambaya,da sauri yana dariya yace ''babu komai mami,Allah bani na shiga tsakaninku ba,kunyarki dai kawai take ji'' ''gafara min,ka maidani wata kakarka ko,tamu ce ni da kai''ta fadactana rabeshi ta fice qasan zuciyarta cike da farinciki,ta tabbatar cewa irin qaunar da take sha'awa danta ya samu ga matarsa ya gama samunta sai godiya ga Allah,abdallah kam ta sani bamai wasa bane gun kula da nunawa iyali soyayya tuntuni ta sani halinshi ne a qidarsa ce Wanka kawai ta zarce da yi bayan ta ji fitar mamin,kayan jikinta ta maida don ta tabbatar abdalla yana dakin,towel ta rufawa kanta sabida jikqewa da sumar tata tayi,yana tsaye bakin madubin hannunshi daya ya dafe amdubin da shi dayan kuma yana ruqe da yar kwalabar maganin yana karanta rubutun lrabcin dake jiki,ta qarasa gaban madubin da sauri da niyyar tattare magungunan don batason ya gane na meye,ajjiye kwalbar yayi ya zare towel dake kanta yaci gaba da goge mata ruwan gashin nata na burgeshi tare da bata sha'awa ''baby kici abinci gaskiya kisha maganin nan'' ''na ciwon kaine kuma ya riga da ya sauka''ta fada akunyace dariya ya saka kana yace ''eh kam gaskiya ne,na gani ai'' ta tsargu don haka tace ''qarya nayi kenan?''ta fad tana hade rai din kada ya bullo da wani abun,ai kam bai fasa ba sai da ya ja habarta yana dariya yace ''gaskiya na sake tabbatar da irin son da mami na kemin,ya Alah ka sake jamin da ranta ka qara mata lafiya da tsawon rai mai amfani,kice gyarani kawai take yi ni ban ma sani ba,i luv my momma''sai kuma tayi shiru bata data cewa don ta tabbatar ya gani sai ya leqa fuskarta bayan ya jawota ua rungumeta ta baya kana ya dora habarsa kan kafadarta yana cewa ''kina zaton Abdallah bai iya larabci ba ko yammata,zan baki mamaki kamar yadda na saba,kwanan nan zan daina magana dake da hausa'' dariya ta subuce mata ''ni din ma akace ban iya bane?'' ''i know baby na,ke din gwanace ta kowanne bangarr tunda kika iya sace zuciyar abdallah tun ruwanki bai isa

Table of Contents

Chapters

138 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138