Chapter 16
Chapter 16
din tanan ta hango zubaida wadda fuskarta ke a dinke tsaf da alamu cikin bacin rai take yana tsakiyarsu,saidai dukansu ya fisu tsaho,tafiya yake cikin hanzari wanda alamu ke nuna cewa cikin kuzari da qoshin lafiya yake,fari ne sol wanda yasa ya zarta duka jama'ar dake tare da shi hasken fata,ko ba'a gaya mata ba ta fuskanci shine *abdallan mami*yawan jama'ar dake baibaye da shi ya sanya bata iya ganin fuskarshi saboda juya kanshi da yayi daya bangaren yana magana da wani saurayi da sauran jama'ar dake gefan nashi,abu uku zuwa hudu zata iya fadi a kanshi suit ne a jikinsa baqa wul mai sheqi wadda ko da bakasan kudin sutura ba kallo daya zaka mata ka tabbatar bata qananen kudade bace,sumar kanshi cike take kuma akwance luf ba tsayayya tamu irin ta hausawa ba,tafi kama data jaruman fina finan india ko larabawa,sai abunda ke saqale bayan kunnenshi guda daya wanda take gani gurin masu aikin tsaro,saidai wannan mai azabar kyau ne haka nan shima baqi ne har suka kammala wucewa tana tsaye a gun,ita kanta batasan me ya tsaida ta din ba,sai daga bisani ta saki ajiyar zuciya hade da sakin labulen ta koma ciki ta lalubo hijabinta ta zura ta tayar da sallah don wasu guraren har sun idar mami na tsaye qofar sashenta harde da hannayenta,duk yawan 'yan rakiyar abdallah bai hanata gano yaron nata ba,yayin da murmushin farin ciki yaqi bacewa fuskarta,daga hannun hagun falon kuma haj nene ce tsaye ita da zahariyya,idonsu tsaye car kan abdallah da zubaida wadda a yanzu ta bar bin bayanshi ta nufo inda suke tsaye zahariyya ce ta tabe baki''don Allah nene dubeta,aikin banza shegiyar yarinya kawai mahaukaciya,wai har wani murna take da dawowar abdallah,don Allah ki barni da ita nene wallahi sai na gyara zamanta'' dafa kafadar zahariyyan tayi tana wani murmushi da na kasa fassara shi''um...um,kinga matsalarki kenan zahariyya gaggawa,idan bakiti wasa ba zaki bata mana plan,ki bar zubaida tayi yadda take so loka ci ne fa,kuma ke kanki kinsan nasan me nake yi ko?'' ''to amma nene wallahi idan ba muyi taka tsantsan ba zata zame mana matsala'' ''ita din ubanta,ni na haifeta ko ita ta haifeni,ki rabu da ita dai a yanzu,akwai lokaci kamar yadda na gaya miki'' ''ko tazo kada ki mata maganar''nenen ta fada da sauri ganin zubaidar ta kusa cimmasu,dama mutanen dake falin ne suka hanata isowa da wuri har isha'i maryam na jiyo sauran hayaniyar jama'a,don haka tana idar da sallar isha'in tayi rigingine abunta bisa gado,kusan goma saura tunanin mamanta ya fado mata,layin hindatu ta shiga nema saboda muryan maman da takeson ji,saidai tayi rashin sa'a is switched off,tsaki taja cikin rashin jin dadi a ranta tana raya cewa da ta dauki albashinta na farko cikin abunda zata yi harda siyawa maman ta waya sabuwa da kuma power bank mai aiki da hasken rana tana tsaka da tunane tunanen nata taji an turo qofar dakin,mami ce wannan karon cikin kwalliyar atamfa super mai kalan blue maidan turuwa,abunka da fara sai tayi tas ''a'ah maryamu kwanciya akayi?'' ''eh wallahi mami''ta amsa mata tana mai miqrwa daga kwanciyar da tayi tana maida daurin dankwalinta da ya zame ''a'ah,yi kwamciyarki abinki,ai kinsha aiki bsna tasheki ba'' tana saka slipper dinta dake bakin gado wanda mami ta bata take amfani da shi tsakanin edroom din zuwa parlour zuwa kitchen ''ba komai mami me kije buqata'' tana shirin amsa mata wayarta ta dau ringing ta kara a kunnenta kai tsaye tace ''ya akayi abdallah'' cikin kwantar da murya yace ''mami yunwa nakeji,wayyo cikina mami'' dariya tayi ''kajimin shi don Allah,yaron goye ne kai,ka soma ci gani nan fitowa na shigo in taho da maryam ne don muci abincin tunda tare muke ci bayan baka'' ''wace haka?'' ''sabuwar mai girki kuma diyata'' ''ayyah mami,ayyah....,nikam nasan kin rage ji da ni,banda haka daga dawowata mami yau inason musha hirarmu mu biyu kuma saiki yo gayya,nidai mami ki taho ke daya abinki kamar yadda muka saba ko inzo in taho dake'' ''naji ya isa sarkin qorafi,kada ka shigo mana daki gani nan fitowa'' ''thank you my mammy,ki sauri na qagu ki fito'' dariya ma ya bata,abdallah kenan,ko yaushe idan yana gabanta daukan kanshi yake kamar qaramin yaro sai da ta dan kalli maryam ta gefan ido dake zaune gefan gado kanta a qasa tana fatan bata ji ba,ta riga da taji amma sai ta nuna kanar bata ji din ba saboda bata ji komai a ranta ba don itama batason ta shiga tsakanin wannan uwa da dan masu azabar shaquwa ''kinci abincinki e maryam'' ''sai anjima,amma dai na shigo da shi'' ''to shikenan ki kwanta ki huta,Allah ya huta gajiya,sai gobe idan Allah ya kaimu'' ''to mami'' har ta kusa ficewa maryam din tace ''a cewa ya Abdallah ina masa barka da zuwa'' murmushi mamin ta saki don har cikin ranta taji dadin kulawar da maryam din ta nuna kan tsoka daya a miyanta ''zaiji insha Allah'' ta fice bayan ta ja mata qofar kayanta ta cire ta sauya na bacci ta ja abincinta ta danci sannan ta kwanta baki daya Qarfe takwas a kitchen tayi mata,tana cikin hade haden abinda zata tanadar musu na bre fast taji an shigo kitchen da sallama,ta waiwayo tana amsawa,mace ce wadda a qiyasce zata doshi shekaru hamsin,ta qaraso kusa da maryam,a ladabce maryam din ta gaidata,itama ta amsa mata cikin fara'a sannan ta dora da cewa,ni suna na uwani,ma'aikaciyar haj bintu ce,naje hutu na ne da take bani na shekara sai yau na dawo,kin ganni da wuri ko?,qauyen mu ba mai nisa bane shi yasa na fito dacwuri gasji Allah ysa na iso da wuri,ni daga qauyen sumaila nake'' murmushi maryam tayi jin cewa suna da maqwaftaka da qauyukansu ''sannu baaba,ni kuma suna na maryam sabuwar ma'aikaciyar data dauka ce saboda kula da girkin yaronta,ni a cikin gari nake saidai asakin mu yan qauyen gaya ne'' cikin jimami da 'yar fara'a tace''Allah sarki kice maqota ne mu,kingawadancan ma'aikatan hajiyan maha'inta ne,da su aka hada baki aka zubawa yaron nan guba wallahi,Allah ne yayi da sauran shan ruwansa a gaba,don Allah mero ki riqe amanar hajiya saboda mutuniyar kirki ce'' dariya baba uwani ta bata jin ta ambaceta da mero ''insha Allahu baba,Allah ya bamu ikon riqe amana''hira baban ta shiga zubawa maryam tana maida mata labarin yadda lamarin ya auku,taso ta karbi wani abin ta taya maryam din amma ta qiya don hirar ma kadai da take mata tana debe mata kewa da sata jin qwarin gwiwar aikin,da haka har ta kammala hada fried plaitain with sauce,ta dafa tea da ya wadatu da kayan qamshi lemon grass,kimba da ginger,ta jada da coconut flour pancakes saboda tea din da yake ba mai yawa tayi ba duka kadan kadan ne daidaisu hakan ne ya bata damar kammalawa da wuri,ta zubawa bab uwani tana ci tana santi maryam na dariya,cikin haka mami ta shigo suka gaisa itama ta shiga dariyar santin da baaba uwani take bayan ta yi mata sannu da isowa,itama tayi mata barka da dawowar abdallah gida,mami tace ta bar baaba uwani ta gyara kitchen din ta wanke kwanukan don dama aikinta ne cikin kitchen din ta barsu ta shiga dakinta ta gyarashi kana ta shige wanka bayan ta wadati shi da freshner,koda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138