Chapter 101
Chapter 101
fita a dakin 🍂🍂🍃🍂🍃🍂 Daga alwalar sallar asuba ta hada da wankanta baki daya ta dawo dakin inna ta canzq kayan tunda ta debo kayanta ganin hisham yazo tasan dole tare da abdallah suke kwana bazaiyiwu kuma tayi ta ziryar dauko kaya ba shi yasa ta debo duk abinda take da buqata abin sallah ta saka tayi raka'atanil fajr wadda falalarta Manzan Allah S A W yace tafi duniya da abinda yake cikinta alkhairi,bata ko jira tayi azkar ba ta koma gadon ta sake nadewa,tanajin inna wuron na tada ta tayi banza da ita duk da idanunta biyu,ta baza kunnuwanta ne a tsakar gida ko zataji fitarsu abdallah ta shiga dakin ta dauki abinda ya mata saura Tun tana azkar tare da tsumayin fitowarsu har wani dan qaramin bacci ya sacera sabida rashin isashshen bacci da bata samu ba jiya Da addu'a ta tashi,ta zabura ta zauna kan gadon ganin rana ra gama fitowa sosai,ta,duba agogon dakin qarfe sha daya har da rabi na safe,takaici ya lullubeta,duka lissafinta iwar haka ta tsufa a kano,ta soma yaye bargon jikinta cike da takaici sallama aka yo cikin tsakar gidan,kunnenta ta kasa sosai don tantance da gaske ne ko irin mafarkan da ta saba yi ne,kamar kuwa ansan tantamar da take yi aka sake rangada wata sallamar Habawa ai duk tsawon gadon inna wuro mai rumfa batasan lokacin data dirgo daga kai ba kana ta kwasa a guje,bata dire a ko ina ba sai tsakar gidan,saura kadan suci karo da MAMI wadda ke tsaye tana son sake yin wata sallamar ga zatonta masu gidan basu jita ba Zubewa tayi gaba daya a gaban mamin ta saki wani kuka mai cin rai,bata taba tunanin ganin mamin na a irin wannan lokaci ba dama zuciya kuma a kusa,ita ma mamin kasa daurewa tayi ta durqusawa ta dago maryam din hawaye na fita daga idanunta,rugume maryaman gaba daya tayi a jikinta cikin wani irin yanayi,daidai lokacin da inna wuro ke fitowa daga bayi dauke da buta a hannunta tana mai amsa sallamar don tana cikin bayin yake jiyo ta ya zaci maryam na bacci ne,dan tsayawa tayi tana kallonsu,take jikinta ya bata mahaifiyar abdullah ce saboda diban kama kadan da sukeyi Dukkansu suna zaune kan tabarmar suna jimanta al'amarin,har yanzu maryam ta kasa matsawa daga kusa da mamin ganin take kamar har yanzu mafarki take,don ranaku daidai ne bata mafarki da mamin cikin baccinta kasa daurewa mamin tayi tace ''banga Abdallah ba,ina yayi ne?'' ''ya fita tattaki shi da hashimu nan bayan gari bakin rafi,kinsan an kwana biyu ba'a taka qafar ba'' cikin mamaki mamin tace ''hisham dai,dama hisham na tare da ku?''kai maryam kawai ta iya gyadawa ''Allah mai iko,shi yasa na rabu da ganinshi,babu irin cigiyar da ban ma hisham din ba ashe kuna tare'' kasa zama maryam din ma tayi ta shiga dauki ta dauki hijabinta ta sulale ta fice tun daga nesa ta hango su zaune su biyu shida hisham da alamu magana suke mai muhimmanci sosai,a hankali ta dinga takawa tana qarasawa inda suke dukka idanunta na kan kyakkyawar fuskar abdalla ''taqi ta gane hisham taqi ta fuskanta,basan ta yadda zan fasalta mata ba,bansan hanyar da zanbi ba hisham,am doing my best hisham,ka gaya min ya zanyi?'' abinda taji yana fada kenan ba tare da ta fuskanci kan me yake maganar ba,sai ta qara sauri ta isa garesu data tuna maqaaudin zuwanta gurin,ji yayi kawai an kama hanninshi kana ta fara jansa,a mamakance ya dago yana kallonta,kasa tambayarta ma yayi sai ido da ya zuba mata,ganin yadda ta dage tana janshi ya sanya shi sauqaqa mata wahalar ta hanyar tashi ya bita tamkar raqumi da akala bata bar jan hannunshi ba har sai da suka isa ga tsakar gidan inna wuro kana ta kauce daga gabanshi,tashin farko idanunsa suka sauka kan maminshi,runtse idonsa yayi ya sake budewa don ya tabbatar shin da gaske ne ko kuwa mafarki shina yake yi kamar yadda ya saba ''mami ce''hisham dake tsaye gefansa ya fada,ita din ma ajikinta ta ji zuwan nasa a hankali ta waiwayo suka hada ido da tilon dan nata,wani irin rauni abdallah yaji ya shigeshi,kewa qauna da soyayya irin ra da ya iyayensa ta taso masa,take jikinsa ya kama rawa yaji qafafunsa ba zasu iya daukarsa ba,yau maminsa ce a gabansa? durqushewa yayi a gun a kan gwiwoyinsa kansa na duqe a qasa,hawaye ne ya balle masa tamkar mace,jikin mamin a mace ta miqe ta isa gabansa ta kira sunanshi ''abdallah,abdallah na ka yafewa maminka'' da sauri ya miqe ya kama hannayenra hawaye na sauka kan fuskar kowannensu,rawa bakinsa yake yama kasa magana,duk abinda yayi niyyar furtawa sai ya kasa,qaunar mahaifiyar yasa ke sake tosa masa,shaquwa da soyayya dake tsakaninsu ba qarami bane,yana jin bashi da kowa idan ba mamin ba,a lokacin data guje musu ji yayi kamar ya mutu,tawakkaki da imani da Allah ne yasa ya iya danne zuciyarsa yasa mata yadda da qaddara kafin daga bisani ta gano cewa koma meye ta aikata musu ba bisa hankalinta bane Qarshe fadawa yayi jikinta yana jin nauyin da zuciyarsa na dada raguwa,wani sauqi ma samuwa cikin zuciyarsa daga abinda ya cunkushe mafa a da hagu da dama suke zaune sun sanya mamin a tsakiya,ko qwaqwaqwaran motsi sunqi yi,ta dubesu cike da tausaya da qauna ''abdallah ku tafi ku kwanta hakanan,Allah ya kaimu gobe ko?''murmushi duka sukayi abdallah ya girgiza kansa ''yau mami komai iya satar baccin banjin zai iya saceni,ko na kwanta din bazan iya baccin ba,itama haka don babu ranar da bazata yi maganarki ba koda cikin zuciyarta ne,saidai idan ke kinajin sai mu qyaleki ki kwanta ko'' girgizq kantq take cikin zuciyarta tana sake jinjina qaunar dake tsakaninsu,tsanar nene ta qara cika zuciyarta,tana jin mawuyacine ta iya yafe mata haqqinsu data dauka,raba qaunar data yi dake tsakaninsu na tsawon lokaci ba tare da sunji ko sun gani ba,haqiqa Allah ne ke saka soyayyar dan adam cikin zuciya A taqaice kwanan zaune sukayi su duka ukun don sai bayan sallar asuba kowanannsu ya kwanta Qarfe uku na rana suna tare da ita maryam abdallah da hisham,mamin ta dubi Abdallah ''gobe nakeson mu koma gida abdallha,saboda haka ku fara hada iya abinda ke da muhimmanci,saura ku barwa mutan gidan kafin komai ya qarasa daidaita ku sake waiwayarsu'' cikin shagwabar da ya jima baiyi wa mamin ba yace ''mami a daga min qafa zuwa jibi,akwai muhimmin abinda nakeson qarasawa kafin mu wuce din'' girgiza kanta tayi ''a'ah,gobe zamu tafi''cike da ladabi yace ''shikenan mami,amma sai la'asar ko'' ''Allah ya kaimu la'asar din'' wani abu ya darsu cikin zuciyar maryam,duk da zuwan mamin ya mantar da ita kaso sittin cikin dari na damuwar data shiga duk da cewa abun na manne cikin zuciyarta,ta bisu da kallo lokacin da ya miqe yana cewa hisham yazo ya raka shi,wani dan banzan kishi ua lullubeta hakanan zuciyarta ke gaya mata gurin mero zashi ''sannu maryama''maganar mami ta dawo da hankalinta,murmushi maryam din tayi ta sunkuyar da kanta,kama duka hannayenta mami tayi ''na gode na gode na gode maryam,haqiqa bani da abinda zan iya biyanki da shi,halaccinki da alkhairinki mai tarin yawa ne a garemu,haske ce hakanan alkhairi ce ke a rayuwarmu ni da dana *ABADAN* ba zamu taba mantawa da ke ba maryamu,tabbas babu wadda ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138