Chapter 4
Chapter 4
sai take jinta a takure,gashi daga raliyan har nasir din shiru kamar an shuka dusa ''madam haka ake kula da baqi?'' tajiyo maganar lokaci guda,ta daga kanta don ganin me maganar,shije zaune opposite dinta,sanye yake da shadda hartin da hula,murmushi ta danyi a taqaice ''ai bani bace matar gidan,ku jirayi fitowarta'' ''ke da ita din ai daya ne,don na tabbata yarda ce tasa suka barki da baqinsu'' sai ta maida idonta kan wayarta don bata da abun ce masa,Allah ya taimaketa masu gidan suka qaraso gaishe gaishe ne suka biyo baya da 'yan hirarrki,saidai duk lokacin da bisa kuskure idonta ya kai sashen da wanda ake ka kira da jabir sai ta tsinci idanunsa na bisa kanta,wanda hakan har ya fara damunta,nasir ya musu jagora zuwa dining domin cin abinci hakan yasa ta cema raliya ''to ai na gama ko,bari na wuce gida'' ''tunda ba da mota kika zo ba ki bari mu kammala sai mu wuce tare ko?'' ta jiyo muryar jabir din na fadi ''kasan kuwa kusa da unguwar take ba''inji nasir ''haka,ne fa,shikenan kin huta hawa keke napep''inji raliya ''amma kinsan baxaiyiwu su kaini gida ba,idan mama ta ganni kuma nace mata su waye?'' ''indai mama kike ji zan kira tq na gaya mata''inji raliyar cikin zuciyarta ta ja tsaki, ''wannan jabir dan shiga hanci ne wlh''babu damar musu tunda duka ido na kanta haka ta koma ta zauna tana jira su kammala,yana bisa dining din amma idanunsa na kanta har raliya ta ankara,cike da gulma ta tabota ''ke,inafa tsammanin kinyi tsuntuwa yau a gidannan'' cikin rashin fahimta tace ''ta me fa?'' hararta tayi ''kiji min 'yar rainin sense,kina nufin baki lura da irin kallon da jabir ke miki ba?'' ''shine me?'' ''wlh sonki yake bisa dukka alamu'' wannan karon ita ta maida nata hararar''kijimin mata,kawai daga kallon sarkin fawa sai miya tayi zaqi?'' ''wlh da gaske nake,jabir mutumin kirki ne diyana,kada kice zaki qishi don Allah'' ''a'ah,kinji ta da wani guntun wa'azinta,ashe har yace miki ma yana sona ko?'' ''ni na gaya miki zai fada miki'' Can saman dining dinma jabirne ke cewa cikin qasa qasa da murya ''kai mutumina nifa nazo gidanka a sa'a,Allah yasa bata da wani'' dariya ya saka''tuni na harbo jirginka ai,indai bilkisu ce a iya sanina ba'a tsaida mata miji ba'' ''ai kuwa bazan tsaya kallon ruwa ba,a yau zan kafa kaina'' A bakin layinsu tasa ya tsaida motar,ta bude murfin tana cewa ''na gode'' ''haba madam da sauri haka?'' sai ta juyo cikin mamaki tana dubansa ''eh mana,ya zaki min illa kuma ki tafi ki barni ba tare da kin bani magani ba'' ci gaba tayi da dubansa,sai ya saisaita nutsuwarsa,baiji ko,nauyi ba ya bayyana mata duka manufarshi,da farko ta ja masa yace shikam yace baisan wannan zancan ba,babu inda,zata tafi ta barshi cikin qila wa qala,idan,ko ta tafi to zai tare ne a qofar gidansu har sai ta amsa masa koda zai shekara maganar da sukayi da raliya ce ta fado ranta ''maryam,wlh indai aure kike so kiyi kada kiqi karbar tayin jabir matuqar yayi miki maganar,jabir bazai taba tararki da maganar banza ba,nasan jabir tuntuni,abokin nasir ne da dewa,halayensu kusan daya,hakan shi ya qara danqon abotarsu'' ita kanta a zahirance bata ga wani aibu ba tattare da jabir din,yana da kyau daidai wanda duk hassada ba zaka kira shi mummuna ba,a iya abinda ta gani da bayanan da raliya ta mata ta fuskanci zata iya amsa tayin jabir,ko don ma ran mahaifiyarta yayi fari,ko don ta samu itama ta zauna a nata dakin kamar sauran qawayenta da 'yan uwanta ganin shirun nata yayi yawa yasa ya sake marairaice mata ga tsammaninsa zata wofantar da buqatarsa ne ''shikenan,Allah ya shige mana gaba'' ''um um maryama,wannan ba amsa bace,kice ina sonka jabir shine magana'' kanta ta girgiza cikin alkunya tace''don Allah ka barni na wuce gida,na tabbata zan sha fada gun mama,don na kai magariba a waje,tunda ka kwaahe min numbers ai sun isa'' fitowa yayi ya zagayo ya bude mata murfin yana cewa''shikenan,kin bani izini na kiraki?'' kai ta gyada masa,kafin ta dauko jakarta yayi sauri ya rigata ya bude zif din ya jefa mata kudi,ta noqe alamun ba zata amsa ba shi kuma yace indai bata karba ba to tana nufin bata sonshi,tilas ta karbi kyautar tasa,sukai sallama amma sai taga ya ja ya tsaya,kallonshi tayi ya daga mata gira ''sai na hango,shigarki gida don tsaron lafiyarki da kuma gane gidan naku koda na tashi zuwa'' murmushi kawai tayi tajuya domin shigewa layin nasu katsam idonta kan isyaku,kai ya gyada sannan ya kwasa da gudu yayi gida,la'ilaha illa nata subhanaka inni kuntu minaz zalimin,tasan tamkar a idanun iyayenshi tayi,cikin fargaba taci gaba da takawa jabir na mata rakiya da idanu har ta shige gidan *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📓✍🏻✍🏻✍🏻 [9/17, 12:49 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 🌺💖🌺💖🌺 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 🌺💖 💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 🌺💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖 💖🌺💖🌺 🌺💖🌺 🌺💖 🌺 ▶4⃣ sai da tayi dira dira a soron kafin ta gano ainihin hanyar wucewa,saboda cike yake da 'yan zance,can hauwa can binta can maijidda kai abun takaicin ma harda zainabu wadda du du du ba zata wuce shekaru goma sha hudu ba kacal a duniya ta tsakiyarsu ta raba ta wuce,taji dadi sosai da babu wadda ta tanka mata a cikinsu cirko cirko ta samesu a tsaye cikin tsakar gidan,inna hadiza ce da baba huwaila sai babansu dake bakin famfo yana daura alwala da alama haramar sallar isha'i yake yi,sai kuma isyaku dake qame a gefe da alama tuni ya gama fesar da abunda ya qunso ''la ha ila ha illallahu,muhammadu dan abdullahi''suka dauko salatin tare yayin da huwaila ta dire ita daya ta kuma dora ''wlh yaya da gaske ne yaro baya qarya,tayani gani don Allah,suturar jikinta ma ai ba da ita ta fita ba,lallai dandi na dada samun gindin zama a gidannan'' inna hadiza dake ta faman gyada kai tana kallon maryamu wadda ke tube takalmanta a qofar dakinsu ba tare da ta dubedu ba tace''qwarai da aniya,ya gama yawon barikin da ita ya kwashi na kwasa ba dole ta canza sutura ba,yo zata shigo mana gida ne da najasa ne'' ''ke meramu zo nan'' kiran baban nata da baqin qazafin da suka jefeta da shi ya daki zuciyarta lokaci guda,a sanyaye ta dawo gabansa ta durqusa kanta a qasa ''wanne dan iska ne ya dauko ki a mota har gidan ubanki?'' muryarta a sanyaye tace''ba dan iska bane baba,gidan raliya muka hadu yace yana sona'' ''yana sonki?'' huwaila da hadiza suka fadi kusan a tare bai biya ta kansu ba ya dora da nashi bayanin ''alhmdl dama ni na gaji,na gaji wallahi kullum rana a unguwarnan sai anyi da ni kan na ajjiye babbar mace a gida,saboda haka ki shaida masa matuqar da gaske yake to na bashi kwana goma ya fito ayi kowa ma ya huta'' ''yo idan banda abunka malam amadu saurayin qwarai ne zai dinga yayibar yarinya yaro kwararo kwararo kuma yace zai aureta,ai qarya ne dan yaudara ne kawai''inna hadiza ta,cafe maganar ''oho,koma dai meye nidai na gama magana,tashi ki bani guri'' jikinta a sabule ta miqe tayi hanyar dakinsu,har yanzu kunnuwanta badu daina jiyo mata qananun magan ganun da suke yi bq marasa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138