Chapter 91
Chapter 91
zai iya da kansa yake yi,ta manta yaushe rabon da ya sata wani abu,ko kwanciya ce ko dorashi saman kujerarsa mustafa ke taimaka masa Bata ankara ba taji yana kiran mero,cikin rawar jiki ta qaraso dakin ganin maryam sai jikinta ya mutu kuma,ta soma rabe rabe ''shigo mana,wancan computer din zaki dauka min da ita zamu tafi saboda hoto ko?''sai ta washe haqoranta ta rave maryam ta wuce ta dauko conputer tana qare mata kallo din ba qaramin burgeta tayi ba ta miqa masa suka fice a dakin,wani dubqulallen abu ne ya tokare mata wuta ya hanata ta hadiyi koda yawu ne,tana jiyo su suna yiwa inna wuro sallama sun tafi rafi sai kawai ta qarasa zamewa ta kwanta gaba daya kan kujerar tana hawaye sosai ''meramu fito,ki saka min lallen nan mana,so nake na cireshi kafin mangariba ki kitse min kan nan,don malam alhaji saukar hantsi zaiyi''ta jiyo inna wuro tana fada,da zata iya da ta cewa inna wuron ba zata iya fitowa ba ta saka da kanta,tilas ta miqe ta goge fuskarta bayan ta sake saka kwalli duk don kada innar ta gane ta fito tana kan tabarma lallen na gefanta,kallo daya ta yiwa maryamun ta maida kanta kan kwanon lallenta ba tare da tace mata komai ba,tun inna wuron na sako hira taga maryam din bata karbarta hannu biyu itama sai taja bakinta ta tsuke suka ci gaba da zaman kurame,duk yadda taso ta hana qwallar fita hakan ya faskar,haka ta dinga sulalowa tana sa gefan dankwalinta cikin dabara tana gogewa ''hmmmm,duniya kenan,Allah yana baka kana bana so,ba shikenan ba,garin kallon ruwa dama kwado kema mutum qafa,dana dam kuma dama ai butulcinsa yawa gareshi''shiru tayi gana jujjuya maganganun inna wuron cikin qwaqwalwarta masu zubi da gugar zana,sai tayi ta maza don kada ta gano kuka take ta tambayeta kanta na duqe kan qafar inna wuron da take sawa lallen ''lafiya inna,wani abu ne ya faru?'' tabe baki tayi ya kau da kanta ''a'ah a'ah,babu abinda ya faru,Allah dai ya rufa asiri,amma shi aure komai lalacewarsa ai aure ne,yafi gaban ace za'ayi shakulaton bangaro da shi'' ''hakane''maryam din ta fada tana ci gaba da abunda take,wani takaici ya kama inna wuron har taja qwafa duk da yadda taso daurewa bayan ta gama sa mata sai taja gefe,gani,zaman shirun ya,isa don innar bata sake tanka mata ba sai ta jawo kwanon lallen wanda yayi ragowa ta qunsa a yatsunta na qafa da hannu daf da kiran sallar magariba suka cire duka ita da innar,yatsun sunyi kyau kam,lallen ya kama ram da shi gwanin sha'awa tana gama daura alwala taji sallamarsa,wanann karon ma sai da gabanta ya fadin,idanunta ya sauka kan mero dake riqe da laptop dina abdallah taba ta shafawa bakin nan kamar gonar auduga,har uanzu jan jambakin data sanya kan ta kile yana nan radam baje baje kan bakinta,ta sake saura dankwalinta sai ta shige kawai dakinsu don ta tabbata zaman hirar,nan zasuyi,hirar da ayanzu babu abinda ta tsana kamar ta Tana shiga ta shimfida abun salla ta tayar da sallar,ko bayan ta idar zamanta tayi kan daddumar bakinta cike da addu'o'i wadanda suk riga da sun zame mata jiki,a kunnenta abdallah ya fita sallah ya dawo,inna wuro tayi kiranta ta fito taci abinci to tace mata har suka kammala bata fito din ba saboda tana jiyo muryar mero Awa daya tsakani ta sake jiyo innar ''ki fito ki lallabe min kan nan tunda ba zaki ci abincin ba,inaga azumin yammaci zuwa dare kika fara'' abdallah ya kalli innar qasa qasa yace ''inna dama bata ci abincin rana ba?'' baki ta tabe ''ina fa taci ta dorawa kanta nunqufurci'' ya marairaice fuska kamar yqdda yakewa mami idqn yanason wani abu ''amma inna banda zama da yunwa fa'' ''qyale shu'uma,cikinta ai da kanta zata nema idan yunwar ta rarakota'' kai ya kada yana jin ba dadi cikin zuciyarsa ''a'ah inna'' ''ka qyaketa nace bawan Allah,ai ba wani ya hanata ci ba'' kwanukan ya dauka ya danna kekansa ya nufi dakin,a kwance ya taddata,amsa sallamarsa tayi tana qoqarin boye hawayen fuskarta don kada ya gani,ta miqe tana gyara hijabin jikinta zata fice a dakin ''dawo ki zauna''taji ya fada,haushinsa take ji fal cikin zuciyarta don haka ta masa shiru,taku biyu ta qara ta sake jin muryarsa mai cike da dakewa da kwarjini ''zan saba miki idan kika sake koda taku guda''cak ta tsaya kana ta dawo da baya tayi zaune kan ledar dakinta bayan ta cusa fuskarta tsskiyar cinyoyinta,keanukan ya tura mata ''dauki ki cinye banason inga komai cikin kwanon''ba tare data kalli kwanon ba tace ''bana ci na qoshi'' ''tunda bakici ki fadi me kike son ci?'' ''na qoshi nace'' ''baki isa ba''ya fada kanshi tsaye,yanayin yadda yayi maganar ya tabbatar mata da gaske har cikin zuciyarsa bazai barta ba sai taci ''me zaki ci nace''ya kuma tambayarta cikin dakewa da ginshira ''fura mai kwakwa da shawarma''tana sane ta fadi hakan don tasan mawuyacine a nan a samu abinda ta fada din baice komai ba ya danna keken ya fice Awa guda ya dawo da baqar leda ''karbi kici''taji yace da ita ta miqa hannu ta amshi ledar fuskarta a qunshe,ga mamakinta duk abinda ta lissafa din ne a ciki babu yadda ta iya haka taja ledar ya tasata a gaba da zazzafan kallonshin nan yace a gabansa zata ci sosai ta bata masa lokaci duk don ya gaji ya fita amma sai ta lura baiko damu ba gyara zamanshi yayi ma,tamkar ma nishadi yangarta da zaunar da shi din da tayi take sashi duk motsin da tayi idanunshi na kanta musamman dan qaramin bakinta mai dauke da pink din lips dake motsawa yana rauna shawarmar cikin rashin son cin abincin,wani abu ya darsa cikin zuciyarshi wanda ya sashi limshe idanunsa,ji yake kamar ya kamaau ya tsotsesu tas,wani,barin na zuciyarsa ke gaya masa loka cine *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽 💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺 💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖🌺💖🌺 💖🌺💖 🌺💖 💖 *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 🌺💖🌺💖🌺💖 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 💖🌺 💖 © *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *_home of expert and perfect writers_* 5⃣2⃣ *_Manzan Allah S A W ya hana bacci bayan sallar magariba haka nan ya karhanta zance/hira bayan sallar isha'i_* *_daga nana Aisha R A tace na kasance ina wanke janaba daga tufafin Ma'aiki S A W sai ya fita sallar asuba da tufafin alhalin akwai ragowar danshin ruwan a jiki_* *_a wata ruwayar ta muslim kuma yace nana aisha tace''na kasance ina kankare janaba daga tufafin Manzan Allah S A W (kamar busashen maniyyi kenan)sai ya saka ya fita salla da tufafin_* *_wannan shafin sadakarwa ne gareki dungurun gum baki dayansa SADNAF bama ke kadai ba har da 'ya'yana AFFAN DA IKRAM Allah ya rayasu ya yiwa rayuwarsu albarka,Allah ya bar zumunci_* Idanunsa suka sake sauka kam yatsunta da take gutsirar shawarman da ita,yanayin yadda take ci kawai ya isa ya gaya maka kan tilas take ci din,don dama asalam ba cimarta bane da biyu tace ita don take so ga zatonta basai samo ba ba qaramin kyau suka yi masa ba,kasancewar yana gan da ita yasanya ya kamo hannunta ''yaushe kika yi wannan abun?'' ya fada yana kallon qwayar idonta,sai ta soma qoqarin zame hannin nata ba tare da ta bashi amsa ba ''maryam''ya kira sunanta can
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138