Skip to content

Chapter 90

Chapter 90

Abadan Book One Complete Hausa Novel 1,272 words 0 views Progress saved
Download Book

lokacin takeyinsa,babu shakka ta tabbatar abdallah da maryam duk inda suke suna da buqatarta,suna da kwadayin ganinta maganganun nene suka sako kai suma kada kuyi mata magana,shikenan kun karya min asiri asiri? asiri wanne iri take nufi,wa aka yiwa asiri kuma akan ne ya karye?duka daga shigowarta gidan a tau tunaninta ke ta mata shawagi,mutanen da ta gani sun fita daga gidan kamar ta taba ganinsu cikin gidan,cikin wani dare cikin kuma wata rayuwa data yi a baya,rayuwar data dinga jinta kamar rayuwar cikin mafarki,cikin rayuwar ta dinga tsinto halin da taga abdallah,abunda ya faru da ita ranar da zata soma rayuwar mai kama da mafarki,a hankali tunaninta ya dawo zuwa yau,maganganun nene sunqi daina yi mata amsa kuwwa a kunne,a dazun sam hankalinta bai nasu muhimmanci ba sabanin yazun data dage kai da fata sai ta tuna dukkan wani abu da nenen ta fada,ficewar da adnan yayi da sauri daga gidan ''taurin ran abdallah ne duka ya jawo mana halin da muke ciki,idan da ya mutu salin alin da mun huta'' maganar nenen ta qarshe kenan sanda take surkuda mata allurar bacci taurin ran abdallah? ya mutu?abdallah kenan abdallah na? tambayoyin sun mata tsauri da yawa,saidai data hada dukkan abubuwan dake wulgawa cikin idanunta sai taso sansano qamshin wani abu wanda ya sata ta qarasa shugewa rudani na haqiqa,ita kadai ke fadin duk inda abdallah yake sai ta nemoshi ba zata iya rayuwa,cikin duniya ba cikin salama ba tare da tasan ina abdallah yake ba,wanne hali yake ciki?,a kullum addu'arta shine Allah yasa ta riga abdallahn mutuwa,zata masa addu'ar samun juriya da qarfin gwiwa kan rashinta,sabanin ita da bata da wanda zai mata wannan addu'ar,ta yaya zata jure rasa abdallah da mahaifinsa ta iya ci gaba da ingantacciyar rayuwa cikin dunuya A hanzarce ta kima sashenta ta wuce bedroom dinta kai tsaye,kayan jikinta ta sauya ta dauki muqullin motarta,haqiqa dukkanin wani zatonta game da yadda rayuwarsu ta cukurkude lokaci guda ra dorashi ga nene,duk da ta sani wani bawa,bai isa ya dora maka wani abu ba face da izinin ubangiji amma akwai silar komai,nene ita ce sila haka zuciyarta ke gaya mata ta bude motarta ta shige tana qoqarin tashinta usaini ya qaraso ''hajiya zaki fita gasu ibrahim kuma na zuwa''ta dubeshi kana tace ''idan sum qaraso kowa ya koma bakin aikinsa na maidashi,gobe idan Allah ya kaimu zamu tattauna da ku duka''ta samu damar fada sakamakon ambaton Allah da take yi cikin zuciyarta wanda hakan ya taimaka qwarai da gaske wajen zaunar da nutsuwarta cikin jikinta Allah yana fada cikin alqur'aninsa mai girma (KU SAURARA,TABBAS DA AMBATON ALLAH KADAI ZUKATA KE NUTSUWA) Babu inda yafi dacewa ta dosa irin gidan kawunta wanda yake a yanzu tamkar mahaifi a gareta,mutum ne mai nutsuwa qwarai da fahimta babu bata lokaci ta fice a gidan kanta tsaye ta nufi can 🍃🍂🍃🍂🍃🍂 Ranar wunin gaba daya akanta ta qare tana zaune qofar gidan ta tasa uban ruwan dake ambaliya agabanta,tun tana zuba ido taga ta inda jirgin agajin su nene zai dira har ta sare baki daya,ta sake laluba wayarta da niyyar kunnata ko zata iya kira saidai sama ko qasa ta nemi wayar ta rasa,wasa wasa ta miqe ta hau zazzage zazzage saidai ko qyallin kalarta bata hango na,abu kamar wasa sai da ta zazzage dukkan akwatunanta amma babu ita babu alamarta,dariya taji ana qyqyata mata ta dago kanta da sauri,malam na hayi ta gano yana keta ruwan yana takashi da qafafunsa tamkar wanda yake kan tsandauri ba ruwa ba,ya qaraso gabanta ya ya daga hannunshi sai ga wayar ''duk abinda kike aiwatarwa yau na sani,kina tsammanin kubuta daha hannu na ne?,to kinzo gidan da idan aka shiga saidai a fidda gawarka,ina jinku habiba ta baki labarin abunda ya faru da ita ko?,wato wanna bai zamamiki izina ba ke yar masu taurin kai,bari na baki shawara qwaya daya a taqaice,ki fidda sa dan komawarki gida muna tare mutu ka raba,koda yan uwanki ma sunzo basu isa su gane hanya ba haka zasu qaraci walagiginsu su koma,mune maganin makwadaitan mata irinku masu butulcewa hanyar Allah,kunqi Allah muma munqi shi kinga kenan mu muka fi dacewa da ku,kin riga da kin zama matar malam na hayi na zama mijinki'' cikin zafi ta bude bakinta da niyyar yaba mishi rashin kunya,bakinta cike yake fal da maganganu masu zafi da takeson ta gaya masa,raahin mutunci ta nado mai uawa zata masa wanda tana tsammanin tunda yazo duniya ba'a taba yi masa makamancinsa ba,da saurinsa ya daga hannunshi na hagu take bakinta ya rufe qam ''daga yau ba zaki sake magana ba sai idan na baki izini ko naso,ba zaki sake min musu ba ko wani ma ba ni ba''kai kawai take gyada masa kamar bawa da ubangidansa ''wuce ki tafi dakinki,daga gobe zaki amshi girki,yau na daga miki qafa kiyi jimamin rabuwa da gida irin na amare iya na yau kawai''nan ma kai ta gyada masa ba tare da tace komai ba ta tsugunna zata kwaahe akwatunta ''shiga ciki kawai,kafin ki isa su sun riga ki isa''nan ma kai ta gyada kana ta juya sum sum sum ta shige cikin gidan,ya isa gaban kayan ya dafa su take suka bace a gun bat,wata magaukaciyar dariya ya saki yaba yiwa kansa kirari kala kala,sai kuma ya dinke fuskarsa cikin yan sakanni tamkar bai taba dariyar ba ya juya ya shige cikin gidan 🍂🍃🍂🍃🍂🍃 Su biyu ne ita da inna wuron zaune qarqash bishiyar lalle take kwabawa innan wanda zata saka a qafarta saboda dawiqar tsoho alhaji gobe daga qasa mai tsarki,har mamakin tsohuwar take bata ganin tsufan kanta ko na mijinta,adonta take daidai shekarubta wanda zai burge mijinta,dazu ta saka sabulu mai qamshi ta wanke kanta tas tace maryam din zata yi mata kitso Tun kafin ta dago ta jiyo muryoyinsu,gabanta ya soma faduwa don ko kusa ko alqma bata sha'awad ta bude ido taga yarinyar,haka suka shigo cikin gidan tana tura wheelchair din suna hira abinsu,tunda ta dago kanta suka hda ido da abdallah ta dauke kai bata sake marmain kallonsu ba,miqewa tayi tsam ta isa bakin rijiya ta wanke hannunta sai tayi shigewarta daki duk da ba wani abun zatayi cikin dakin ba,tsaye tayi tana jin uadda suke hirarsu su ukun sun ma maisheta tamkar wata bare,kada ma abdallah yaji labari wanda a a yanzun ya koyi zuwa masallaci daga nan idan yaga damq yayi zamansa qofar gidan nenen suyita hira da samarin qauyen,idan kuwa ya tashi dawowa to mawuyacibe ka ganshi ya dawo shi kadai ba tare da mero ba,duk yadda taso danne zuciyarta da hanata jin kishin abdallah abun ya faskara yafi qarfinta,daga qarshe ta yiwa kanta hukunci ta yarda tana kishin abdallah saboda amanarsa da mami ta barta amma ba wai don so ba Ko daya bata ji shigowarsa ba sai gyaran murya da ta ji a bayanta,ta dan waiwayo da sauri wanda hakan kadai ya isa ya gaya maka tunani takeyi ''excuse me madam''ya fada yana nuna mata hanyar da zai wuce din ba tare da ya kalli fuskarta ba sai ta janye gefe ta zauna saman kujera ya qaraso ya wuce bangon dakin inda laptop dinshi ke ajjiye,tayi qasa da yawa hannunsa bazai iya kaiwa ba,tayi zaton wannan karon zai nemi taimakonta sabida gaba daya yanzun duk abinda hannunshi

Table of Contents

Chapters

138 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138