Chapter 30
Chapter 30
mun gama da abdallah zan kiraki,da fatan ba zaki qi zuwa ba'' ''Allah ya bani iko''ta fada da gaggawa tana wucewa don ganin abdallah na isowa gurin duk da haka bata kasa jin abunda yake fada ba kasancewar sun biyota ne a baya ''hisham,wlh hisham ka fita a ido na,kai me yasa baka jin shawara sai shegen taurin kai?''dariya ya qyalqyale da ita ''kai kuma mai yasa kake da girman kai da kafiya,Allah bai haramtamin harinya ba na gani inaso to kuwa ba zaka hanani ba'' ''ok haka kace?''ya fadi cikin huci yana dubanshi ''yes,haka nace,idan kuma kai ke sonta ai sai ka fada sai in janye maka'' a zafafe ya soma fadin ''na rantse hisham zaka jawo mu samu sabani mai girma da kai,in rasa inda zanyi ajiyar soyayyata sai gun house girl kuku?,ina da dukiyar da zata iya bani duk kalar macen da nake so na aura,ko 'yar wane kuma ko awanne qasa take,wanda nake tare da shi ma yafi qarfin auran house girl,indai ko zaka ci gaba kan qudirinka ka tabbatar cewa yana daidai ne da datse igiyar abotarmu''yayi gaba cikin hanzari abunka da qaqqarfan mutum ko cikin parlour din ma dambarwar da suka dinga yi kenan sai da mami ta shiga maganar ''hisham ka qyale rigimar abdallah,maruam ta cika macen da za'a so,tana da dukkan halaye managarta,uwa uba kyau,don haka babu hujjar da abdalla yake da ita da zai hanaka neman maryama,ni na goyi bayanka saidai idan ita tace bata so'' ''toh...nima haka na gani mami,nace masa ya fada idan yana so ne shima sai....'' ''dakata hisham,don ina nema maka hanya mai bullewa kake cimin fuska?,to kayi na farko kayi na qarshe,duk lokacin da ka sake cewa inasn waccar abar wallahi sai na fasa bakinka'' ba hisham ba hatta mami abun ya bata dariya,abdallah mai rikicin gangan inji hisham,a haka abida tq fito ta taddaau,wannan karon ma cikin shigar doguwar riga take mai sulbi saidai armless ce,a mutunce suka gaisa da hisham don sunsan juna,ta juya ga abdallah ''soulmate,me yasa kamin haka don Allah,na diro naija da daukin ganinka sai kuna kayi tafiyarka aiki sai yanzu zan ganka?'' ''da kika ganni yanzun ma ki godewa Allah,a tsare gobe ne haduwarmu,haka ne?''da sauri hisham ya shiga maganar ganin abdallah nason qarawa kwabar ruwa ''shareshi don Allah,kanshi ne ke hayaqi tun dazun'' tuni abida ta rudevta dawo kukerar da abdallan ke kai tana tambayar wa ya taba mata ruhinta,tsam mami ta miqe ta basu guri,banza ya bawa ajiyarta don haka kawai yake jin ransa na zafi ''wlh abdallah nan naki rigimamme ne sai kinyi da gaske,haka kawai ya haqiqance wai bazan auri maryam ba?'' ''wace maryam?''ta tambaya tana duban abdallah ''mai shirya masa abinci kullum yana dirkewa'' ido ta,zubawa abdallan,lokaci guda wani kishin maruam din ya dirar mata,take taji ta tsaneta ''amma soul mate mene hujjarka na hana hi....'' a fusace ya miqe ''ke dakata min,kinsan banson titsiye ko?''yaja tsaki ya juya zai fice a sashen kuka abida ta saki,wannan wane irin jaraba ce,daga dirarta a qasar ko kwana batayo ba abdallah ya aona bata mata rai,lallai abunda kake so shike wahalar da kai kukanta bai dameshi ba ya juya ya fice,da sauri hisham yace ''kiyi haquri bari,na sameahi ranshi ne a bace''cikin hanzari ya bi bayanshi amma da yake gwanin sauri ne tuni ya miqe balcony yayi sashensa bai damu da hade girar sama da ta qasa da ya sakeyi ba duk don kada ya masa qorafin abunda ya yiwa abida ya hau masa fada tare da cewa yaje ya lallasheta ''wa?,ni?Allah ya tsareni,bani da lokacin lallaahin mace wallahi,ruwanta ta ci gaba da sona ruwanta tace ta haqura,amma babu lokacin rarrashin mace a rayuwata indai ba mahaifiyata ba'' karab cikin kunnen maryamu dake kwance saman gadonta don sun iso saitin window dinta,miqewa tayi ta zauna saman gadon,wani irin haushi da tsanar abdallah suka kamata wanne irin nau'in mitum ne shi? taqama da gadararsa sunyi yawa,dukiya?ita ke rudarshi ko kyawun da yake da shi?,haushi da takaici suka kamata tamkar da ita suke maganar,haushinsa ta dinga ji sosai,da tana da iko sai ta masa dukan tsiya ko zata samu sauqin abunda take ji haushinsu abida ya kuma kamata don me suna mata da Allah ya yiwa baiwa da ado da kunya su dinga watsi da baiwar,so hauka ne?,ta godewa Allah da bai dora mata wannan masifar ba,gwara da Allah ya bar zuciyarta wankakkiya kuma kubutacciya daga dukkan soyayyar wani kusan awanni biyu da shigewarsu mami ta turo qofar dakin ta shigo fuskarta qunshe da murmushi ''maryamu diyata,jeki harabar gida hisham abokin abdallah na son magana da ke,duk abinda ya tambayeki kada kiyo nauyin baki ki sanar masa da gaskiya kinji ko?'' ba zata iya musu da mamin ba tilas ta amsa da to sannan ta fito yana jingine jikin motarshi ta isa gareshi,da fara'arsa yake fadin ''barka da isowa,tun dazun nake jira har ma na fidda rai?'' ''uhmmmm''kadai ta iya cewa taja bakinta tayi shiru tana sauraren bayanan hisham,ya rufe da fadin ''ina son inji gaskiyar abunda yake ranki'' tayi shiru kamar ba zata ce komai ba,bata jin ko dis a ranta zata iya hada dangatar aure da duk wani abu da ya shafi abdalla, *MUTUNCI* shi take nemawa kanta, *DARAJARTA* itace mafi muhimmanci fiye da komai a gurinta,har sai da hisham ya sake maimaita tambayarshi ''ya hisham na gode da mutuntawa da karramawar da kamin har ka furta kana sona,saidai ina mai baka haquri tare da addu'ar Allah ya baka wadda ta fini komai da komai,amma bani da ra'ayin soyayya,kayi haquri idan hakan ya bata maka rai'' shiru yayi na wani dan lokaci da alamu baiji dadin,amsar da ya samu daga gareta ba ''babu komai maryam,ita dama harka ta soyayya babu batuntilas,na gode nima da yadda kika mutuntani,amma ina nan ina jira har zuwa lokacin da kika ji jin aminta da soyayya'' murmushin yaqe tayi,ita kadai tasan me take ji cikin zuciyarya,wani irin qunci take mata,kyautar dubu goma hisham din yayi mata,da ta doje tace bazata amsa ba yace shina kam yayi niyya bai fasawa,dolenta ta amsa ta masa godiya sanna ta juya don komawa ciki tuni an kashe qwayayen waiting parlour babu haske sai wanda ke fitowa daga sashen mami da nene,tazo tsakiyar parlour din taji an fincikota baya,razana tayi matuqa,tuni idanunta suka fito wajevta bude bakinta da niyyar qwalla qara saidai bata samu damar hakan ba,sakamakon hadata da bango da kayi aka saka wani lallausan tafin hannu aka danne bakin nata,qamshin daddadan turare ya mamaye hancinta,qirjinta ya shiga dagawa da sauka numfashinta ya soma tsere,minti kusan daya sannan taga haske kadan ya bayyana atsakninsu ,haaken screen ne na waya,fuskarsa ta fara gani abdallah ne,sanye da t.shirt fara sol cotting mai gajeren hannu wadda ta fito da murdadden damtsensa,kauda da qwayar idanunta tayi ta daina kallon fuskarshi sakamakon yadda take babu alamun rahama ko kadan a cikinta murya a kausashe kuma qasa qasa yake fadin ''kin taimaki kanki da baki amsa masa kina sonshi ba,wallahi koda wasa kika amsa kina son wani da ya jibanceni kin shiga uku,baki kai ajin da zaki shiga rayuwar abokan huldata ba,ki qara gaba zaki iya samun wanda ke muradinki acan wata rayuwar ba tamu ba,bana aon cusa kai cikin lamura na da katsa landan tun ba yau ba na gaya miki,ki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138