Chapter 68
Chapter 68
a kanmy yake don babu bakin magana ne'' cikin fushi ya dago ya dubi nene ''to wai nene ke wanne mataki kika dauka yanzu,na rantse da Allah ba za'a zubar min da jini a banza ba''wani shu'umin murmushi ta saki ''ni yanzu duk wani mataki nawa nafison abdullahi ya wuce tukun shine babbar matsalarmu,yaron ne shegen taurin ran tsiya kamar kyankyaso.....amma yanzun bamu da nutsuwar da zamu tattauna wanna batu ku tashi kuje jibi zamu zauna,na kira malam na hayi yace baya nan sai jibi zan kira shi naji mataki na gaba,zan sanar da bintu abinda yarinyar tayi don bani da burin da ya wuce ta sata ta bar gidan saidai abun mamaki duk irin aikina bata kudina da nake taqi sallamarta hakanan ko ma samu sauqin tafiyar da aikin....'' itakam zahariyya ma kasa cewa komai tayi ''amma fa nene,naga hannun abdallah ya dawo aiki''ya fada yana kallon nene,da sauri zahariyya ta tashi zaune daga kashingidar da adazu tayi tana kallon fuskar nenen tana zazzare idanu wani murmushin ta kuma saki tana girgiza qafa ''ko duka jikin abdallah ne ya dawo aiki wanna karon naci alwashin abdallah bazai qara sati guda araye ba,don nima......'' tilas suka katse maganar kowa ya watse sakamakon shigowar zubaida dakin nenen ta bita da kallon mamaki don tayi zaton ciwon ABDALLAH zai sata a wani hali sai ta lura ma sam tunda ya fara cutar ko hanyar part din bata yi,hankalinta kwance kamar bata da wata damuwa da shi,hakan ba qaramin dadi ya yiwa nenen ba ππππππ Su uku ne cikin bedroom din,hisham da abdallah sai maryam dake zaune kan ressing chair data janyota bakin gadon inda abdallah da hisham ke kai hisham na bawa abdallan kunun gyada bayan masa wanka da canza kaya da aka masa ckkin baqin t shirt da trouser da suka sake haska shi farinciki ne fal zicjyar hisham sakamakon ci gaban motsa hannun da abdallah ke iyayi yanzun,yana bashi kunun suna hirar da maryam duk da nata bai wuce eh ko a'a,ba gwanar magana bace ama sanann bugu da qari kallon da abdallan keta tsareta da shi ke dada takura ta,wani kallo ya koya daga wayewar gari zuwa yanzun,duk wani motsinta na kan idanunshi,lafiyarta yakeson ji amma babu bakin tambaya ''kai man,irin wannan kallo haka ko na baku guri neοΌ''inji hisham yace da abdallah cikin zolaya,kallonshi kawai abdallan yayi ya saki murmushi,duk sai suka zuba masa ido don tunda ya fara ciwon wannna ne karon farko da suka ga murmushi kan fuskarshi cikin dariya hisham yace ''kai mutumina,anya daren jiya ba soyayya aka sha ba kuwaοΌ''kunya ta kama maryam ta duqar da kanta ,yayin da abdallah ya sake wani murmushin yana duban fiskar hisham bisa dukkan alamu akwai abinda yake son fada wanda ya kasa fada ''Allah ya baka lafiya abdallah''inji hisham yana dafa kafadanshi,ya dubi maryam ''me kikace dazu yana buqataοΌ'' kanta na sunkuye tace ''shaving za'a masa,naga kanshi yayi suma da yawa'' ya dan duba agogonshi ''eh gaskiya ya kamata,bari na masa na kai ke sqi kiyi masa na fuskanshi'' ''ai ban iya ba'' ''eh,ya kamata ki koya madam,zan nuna miki,akwai meeting da zamu shigavda ma'aikatan kamfanin suger na abdallah,don ina tsammanin gwara kawai a rufe kamfanin har zuwa lokacin da zai samu alfiya,saboda barnar da ake cikin kamfanin tayi yawa'' ''Allah ya taimaka'' ta ce bayan ta miqevta dauko masa kayan askin,ya kammala kana ya nuna mata yadda zata masa na fuskar ya musu sallama ya wuce ta bishi da godiya gefanshi ta dawo ta zauna ta fara matso cream din,a hankali take shafa masa a gefe da gefan fuskarshi,idanunahi qyar cikin nata,nauyi takeji da kunyarsa duk lokacin da ya zuba mata idanunshi,a hankali ta janye qwayar idonta tana ci gaba da shafa masa din,ta kammala ta dauko shever ta fara masa askin,ajiyar zuciyan da ya saki ya sata saurin kallonshi cikin tsoro,cikin sassanyar muryarta tace ''ko na yanke kaοΌ''murmushi ya mata ba tare da ya nuna alamun a'a ba,kusan sakanni uku sannan taci gaba,a hankali taji ya riqe hannun nata da take shaving di dashi,ta sake waiwayo ta kalleshi shima din ita yake kallo ta langabe kai ''da zafi koοΌ,dama na ce masa ban iya ba.....''bata qarasa ba taji ta kan qirjinsa sakamkon janyota da yayi ya rungumeta tsam dukan uku uku qirjinta ya shiga yi,tayi yunqurin tashi taji ya sake maidata,idanunshi a lumshe kamar yadda nata yake,dukkansu suna jin bugun zuciyar junansu da ta qara gudu fiyeda yada take bugawa,sannu a hankali taji kasala na kashe mata duk wata gaba ta jikinta,jikinta ta saki batasan yadda akayi bacci yayi awon gaba da ita kan qirjin nasa ba,shi din ma yanayin ya masa,ji yake amar ya tsaida lokaci don su dawwama a haka,tun yana jin saukar numfashinta har shima baccin yayi gaba da shi πππππ kusan lokaci daya suka farka,da hanzarita ta miqe daga jikinsa don tunawa da cream da ta bar masa a fuska,idanunshi a lumshe yake kallonta,sai taga ya kai hannunshi gefan kunnenta ya ciro wani abu ya nuna mata,cream dinne da sauri ta dauki madubin dake hade set da shaver din ta haska,ai kuwa gashi nan ta kwaaheshi ya bata mata fuska ta dubeshi suka hada ido sai suka saki murmushi tare,dan towel din askin a janyo ta goge fuskarta ta matsa ta dauki shaver zata ci gaba da askin,dora hannunshi yayi saman nata hannun da sauri ta janye hannun nata saboda tsigar jikinta da taji ta tashi,ya karbe abun askin ta fuskanci me yake nufi don haka ta dinga haska masa yana askin da kansa,idan ya gaji ya tsaida hannun nashi ya huta tunda har yanzun ba wani qwari ne da shi ba towel tasa mai mai kyau ta goge masa fuskan bayan ya gama,tana shirin miqewa taji ya riqo hannun nata ya sanya tafin hannunshi cikin natan ya matsa su sannna ya gyada kai ta fuskanci godiya yake mata,murmushi kawai ta saki ta sunkuyar da kanta kana ta zame hannun nata ta sauka daga kan gadon tana tattara kayayyakin da sukayi amfanin da su har yanzu idonshi a kanta yake,yanayinta kadai burgeshi yake,kominta anutse cike da tsafta tausayi da kulawa,ya maida idonsa ya lumshe bayan yaga fitarsa yana addu'ar Allah ya bashi damar da zai nuna mata nashi kalan halaccin koda bata sonshi da uammain mubarak ya kawo wheelchair da hisham yace ya kamata a fara dora abdalla atleast zai dinga jin dadi idan an fita dashi daga bedroom zuwa parlour zuwa balcony din saman tunda ba zata iya saukowa da shi ba falon qasa,yaji dadi kuwa don alamu sun nuna afuskarshi,yawanci idan la'asar tayi aka dorashi zata yita shawagai da ahi daga parlou zuwa kitchen zuwa balcony din wani sa'ilin ma ya mata alaman su zauna cikin kitchen musamman idan tana girki,ganin zaman shiru suke yi yasa tana girkin tana bashi labaraimasu debe kewa,hakan kuwa na matuqar sa farinciki a zuciyarshi,don zata ga fuskarsa ta fadada sosai da murmushi alamun yana jin dadi saidai kallon qurillar da abdallah ya koya tilas yasa take zama da hijabi,don ba qaramin kunya yake bata ba,ko ina yaso kalla kallonsa yake kanshi tsaye,da sun hada ido kuma ya wani lumshe ido ya basar kamar bashi ba,wani lokacin murmushi take cikin zuciyarta tace ''hali zanen dutse,babu abinda ke saiyawa dan adam halinshi,har yau halin abdallah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138