Chapter 46
Chapter 46
da ta bi gidan da kallo,duk kyau na gidansu mamin wanna ya dokeshi,bude motar yayi yay ficewarsa ba tare da da yace mata komai ba zaman kusan awa guda da rabi tayi kafin ta sake ganin fitowarsa,a dan bakin qofar ya tsaya kafin ya qaraso tana iya hango jikin wanda suke magana tare,da alama macece don ga gefan mayafi nan,ba qaramar qufula tayi,ba cikin zuciyarta ''zance yazo kenan ya barni a mota ko yayaοΌ''ranta sai ta kuma ji ya baci,ya bude motar ya shigo ''zance da ranar Allah cikin watan azimi,wanne wane irin tsari ne''ta ja tsaki,saidai cikin subutar baki tsakin ya fito juyowa yayi kalleta ''wa kike ma tsakiοΌ''sai ta juyo tana kallonshi itama ''idan kika sakemin tsaki sai kin fita min a mota tunda bada kudinki aka siya ba''sai idanunta suka wal ''daina kallona''ya fada bayan ya dauke kanshi da sauri daga cikin idanunta ''kada ki cuceni''ya fadi can qasa yana lumshe idanu tarw da yiwa motar key,bata kawo komai cikin ran ta ba ta dauke idonta cike da jin haushinsa ππ²ππ²ππ² Ashirin ga azumi mami ta bata kayan sallarta,a dinke suke dinki ne na gayu wadanda suka mata cif a jiki,atamfofi uku lace daya material daya,sai codelace shima daya,duka atamfofin dogayeb riguna aka mata don mamin ta fuskanci tana sonsu,jaka biyu takalmi biyu sai mayafi biyu hijabi daya,sannan tace ashirin da biyar ga azumi zasu fita sai ta zabi fashion da zatayi amfani da su,bata fasa yiwa mami gidiya ba duk da ta gaya mata diyarta ta yiwa no need tace sai ta gode mata,godiya kuwa ai tamkat wajibi ne tayi mata don ko daga gurin mahaifinta bata taba samun makamancin irin wannan gatan ba abida kam akwati guda medium abdallan ya hada mata bayan takurawar da mami tayi masa kan ya hada matan,don shi totally baiyi niyyar mata komai ba cikin irin kyautar da mamin ke yawan yi mata ta fidda atamfa biyu ta baiwa tela ya dinkawa mamanta,ta siya mata mayafi takalmi da jaka,albashinta na watan ciki ta cira ta baiwa hibdatu tayi siyayyar salkarta babanra ma shadda ta siya masa kala biyu ta hada mishi da kudin dinki da takalmi da hula daidai,kai kada ksso kaga baqinciki,ina wuta a saka maman da iyalsnta,godiya kam gun baban ba'a magana ''sai yanzu nasan na haifa,yanzu ne na fara cin albarkar haihuwa''baban ya fada lokacin da yake gwada hular da ta kawo masan ''oho dai,wlh malsm ka guji ranar da zaka karbi shegen jika cikin gidan nan,ka gama cin dadin dai wuyar na tafe,shi yasa gata nan har yau babu mashinshini yo kowa yasan aikin tsiyar da take aikatawa'' inji baba hadizar don daga ita har huwailsn babu wanda yasan da zancan kawo kudinta,ranar kamar Allah ya kadasu duk suka fice unguwa suda qananun 'ya'yansu,huwaila tayi gurin boksn boginta ita da uwale hadiza ma ta bazama ga nata bokan,sunacan yawon asara har yan kawowar suka tafi,'yammatan da zawarawan kuma na nade a gado suna bacci don wadan nan sukan kai sha biyu da rabi zuwa daya basu tashi ba huwaila kuwa cewa tayi''mu namu ai shegensu mukayi muka shigo dasu gidan ko,ko ince tsinannu ne''shidai babu wadda ya kula cikinsu ya kwashe kayanshi ya shige dakinsa ππππππ Qarfe goma suka dawo daga siyan kayan kwalliya da suka fita harda mami da abida,tayi sallama da mamin ta shige dakinta don da wuri take son yin bacci ta tashi akan lokaci sallar dare saboda yau an kai azimi ashirin da shida zuwa anjima daren ashirin da bakwai zai shi daren da akesa ran dacewa acikinsa zuwa sha daya na dare takammala komai ta haye gado bayan ta gama addu'o'in kwanciya ta karanta saqon abdur rahim fuskarta fal da murmushi,kusan cikin watn gaba daya wayarsu bata fi aqirga ba sai tex akai akai,yace shikam bazai iya jurar jin muryarta ba,tana shirin kashe wayar kira ya shigo,ta zubawa lambobin ido tana kallonsu,tana tunanin inda ta taba saninsu tabbas ta taba sanin numbers din,har wayar ta tsinke ta kasa dagawa,second biyar tsakani wani kiran ya kuma shigowa,jiki babu qwari ta sanya hannunta ta daga ta kara akunnenta ''assalamu alaikum wa rahmatullah''itace abinda yavdaki sodon kunnenta,mummunar faduwa gabanta yayi,babu inda zata ji muryar ta kasa ganeta,amma tan tama take kiran nata ne ko batan kaine,ta sake cire wayar akunnen ta tayi ta kuma duba screen din wayar mai kiran dai na bisa layi kuma ita din aka kirar *mrs muhammad ce*π ππππβπ½βπ½βπ½ [9/17, 12:54 PM] 80k: ππππππ πΊπΊπΊπΊπΊπΊ πΊ *ABADAN*πΊ ππππππ πΊπΊπΊπΊπΊπΊ ππΊππΊ ππΊπ πΊπ π *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* πΊππΊππΊπ πΊππΊπ πΊππΊ ππΊ π Β© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*π‘ *_home of expert and perfect writers_* βΆ3β£4β£ *_daga abu hurairah Allah ya qara yarda da shi yaceοΌan tambayi manzan Allah s a w wanne musulmi ne yafi falalaοΌ,sai yaceοΌwanda musulmi suka kubuta daga sharrin harshensa da sharrin hannunshi(ma'ana bai cutar da kowa da harshensa ta hanyar magana,ko kuma da hannunshi ta hanyar ayyukansa,daure ka/ki zama daga cikin musulmin da suka fi falala,abun ba wuya ππ½matuqar ka jajirce kafi qarfin zuciyarka,Allah ta bamu iko ameen)_* ''wa alaikumus salam''ta fada asanyaye shiru ya dan ratsa tsakani kadan ''da alamu baki ji dadin jina da kika yi ba ko maryamuοΌ,hala ma kin manta da niοΌ'' ''ko daya,ban kuma mance da kai ba'' ''da fari kafin nace momai maryam,nasan bani da kalmomin da zasu gamsar da ke gurin ban haquri,amma duk da haka ina roqarki don Allah don annabi ki yafemin,ba da gangan abinda ya faru tsakaninmu ya faru ba,bada sani na bane maryam,ki yafewa jabir masoyinki'' tausayinshi ya kamata ta dan kumshe idonta kadan ta bude ''kada ka bata bakinka gurin bani haquri jabir,tuntuni gaskiya ta dade da yin halinta,anyi walqiya komai ya bayyana'' yaja dogin numfashi kana ya sauke ajiyar zuciya ''alhamdulillahi rabbil aalamin,dukkan godiya ta tabbata ga Allah,babu shakka ke din jaruma kuma nagartacciyar masoyiya ce,bana tantama zaki zama mace ta gari uwa ta gari gurin 'ya'yanta,bazanyi nauyin baki ba ba kuma zanyi qauro ba maryam inason ki bani damar fitowa neman aurenki karo na biyu,tare da cikakken fatsn babu wani da ya sha gabana'' sai da gabanta ya fadi,tayi shiru tana son daidaita bugun zuciyarta sannan daga bisani tace ''qaddara ta riga fata jabir,Allah ya qaddara run da dama ni ba matarka bace,hakaza matar mutum kabarinsa,bai wuce sati biyu da kawo kudin aure na da wani ba'' ''la haula wala quwwata illah billah''ita ya dinga maimaitawa tsawon mintina biyar ''yanzu kina nufi maryam na rasa ki kenan,zaki auri wani naοΌ,ki bani dama maryam mai rabo shi zaya samu tunda har yanzu ba'a daura aurenku ba balle kice kin haramta a waje na'' ''kai mai sani ne jabir bakin gwargwado,ka sani cewa nema akan nema haramunne,baya ga haka ma daga ni har kai babu wanda aka bawa qudirar rubuta kundin qaddararsa da kansa,kuma buwayin sarkin dake rubuta msna din mai dumbin adalci ne,babu yadda za'ayi ya rubuta mana abinda zai zama zalunci ne a garemu'' ''haka ne maryam,alhndlh Ala kulli hal,na gode maryam,na gode matuqa da gaske,bazan taba iya mantawa dake cikin kundin rayuwata ba,na barki lafiya'' tafi minti biyar riqe da wayar ra kasa ajjiyeta,tausayin jabir dinne kadai ke dawainiya da ita,babu shakka bazata iya manta dumbin alkhairansa gareta ba,koda ta tashi sallar dare bata mantashi cikin addu'o'inta ba,ta roqa masa alkhairi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138