Chapter 87
Chapter 87
tayi fari ga cikinta da ya fara dan dagawa kadan,kallo daya tak mai hankali zai mata ya bawa kansa amsar ciki ne da ita fuska ta yatsina tana kallonta tare da qiqarin boye cikin ''wlh nene nima bansan me yake damuna ba''hannu ya saka ta daki cikin jikinta tace ''don uwarki don ubaki tsinanniya ga abunda yake damunki nan''take zubaidan ta durqushe tana dafe da cikin hadi da cewa ''wayyo Allah na''nenen bata damu ba ta finciko ta sai ganinsu adanan yayi tana janye da ita bata saurara mata ba taci gaba da janya sai da ta kawota har falon qasa kana ta watsar da ita ''don uwarki sai kin gayan wanda ya miki cikin nan,shegiya tsinanniya mara amfani,gwara na kasheki na kashe banza bani da asara,cikin shege a jikinki zubaida''ta kai mata duka ta kuwa sameta,qara zubaidan ta saki wanda yayi daidai da shigowar kira a wayarta a niyyarta ta cilla da wayar sabida tashin hankalin da ta fada amma ganin sunan zahariyya yasa jiki na rawa ta daga tana fadin 'yar albarka komai sai ya tsaya mata cak jin bayanan bakin zahariyyan data yi wanda tana kuka tana zayyane mata,bata ma gama ji ba ta dakatar da ita tana fadin ''gani nan zuwa har gun malam din,shi ya isa shi din banza,a kaidina baisan komai ba yau zai sani''qita taji wayar ta katse haka zahariyyan taji,tana dubawa taga kudinta ne suka qare haka wayar ta soma warning na battery low,dama a power bank dinta da ta taho da ita take chargyn tunda ko sau daya bata taba ganinsu da wutar lantarki ba,kai ko igiyoyin wutar ma babu a ina ma zasu samu suna dajin Allah?,tana ji tana gani wayar ta mutu,hannu ta dora aka ta saki wani sabon kukan ta kife kanta tsakanin cinyoyinta Sau uku nene na trying na kiranta sai ace mata is switched off,tilas ta haqura ta kalli adnan ''muje adnan gurin malam,wani bala'in yake son jawo mana''adnan ya zaro ido don shi,kam ya gaji da jin wannan bala'i kala kala har yau kuma babu sauqi,zaiyi magana tace ''kame bakinka muje koma mene kaji a mota''ta juya ta kalli zubaida dake durqushe ''ke kuma idan ba shirya barin duniya kika yi ba to ki nemo wanda ya miki ciki tin kafin na dawo na aikaki lahira''ta kaimata mari tana sake tsaine mata ta kuwa sameta akuncinta,dafe kuncin tayi tana fidda qwalla ba don komai ba sai don azabar zafin marin ''ga wanda yamin cikin nan''taji zubaida ta fada,ta dago kanta daga qoqarin sanya mayafin ta da take tana duban inda zubaidan ke nuna mata,saura kadan numfashinta ya dauke sakamakon ido hudun da sukayi da muuugu da yaranshi,fuskarnan yadda kasan wanda ya dauko saqon mutuwa a hade take tsaf,abu biyu zuwa uku ne suka daki zuciyar nene lokaci guda,kudinsa da yazo karba wanda a yanzu bata da shi bata da shi bata da dalilinshi,na biyu cikin da yake jikin yarta wai nasa ne?,na uku yadda taga sun cukuikuye adnan ko cikakken numfashi baya shaqa sakin adnan din sukayi yaci qasa kana ua tako a hankali gaban nene yana jujjuya wuqar dake hannunshi,batason ta nuna masa tsoratarta don haka ta tattaro yar mitsitsiyar dauriya ta dorawa fuskarta don bata kai zuciyarta ba,hannu ya miqa mata,sai ta kalleshi sheqeqe ''me kake nufi?''dariya ya kece da ita wanda har hantar cikin nene sai data kada balle adanan da ya dade da sakin gudawa,don b qaramin tsoron mutuwa yake ba arayuwarshi ''banda ke mara mutunci ce har sai na miki bayani ma,zan mkki bayani amma ki tabbatar a bakin rayuwarki'' ta tsorata ainun amma sai ta fara masa haukan qarya ''banda kai matsiyaci ne baka da kunya ko misqalazarratin,ka dirkawa diyatq ciki sannan kuma kace na biyaka wadansu kudade,to wallahi na fika iya iskanci,baka isa ba'' Daya dagq cikin yaransa ya matso yana fadin ''ke hajiya ki iya bakinki,ai dama kowa yasai rariya yasan zata zubda ruwa,bamu da mutumci kamar yadda ke ma baki da shi don babu mai mutumcin dake hada sabgarsa da mu'' ''kai yaro dakata a haife na haifeku gaba dayanku,to wallahi duk ba tsoronku nake ba,kudi ne bazan biya ba kuma ku saurari sammacin kotu sai nayi shari'a da kai kam cikin da ka yiwa diyata tun.......'' wani kyakkyawan duka da ya sauka tsakiyar kanta ya haddasa wa qwaqwalwarta daina aiki na wucin gadi,wasu taurari suka kewaye idanunta take ta sulale ta fadi a gun,sai da ta kusa kusan minti biyu sannan jinta ya dawo sai ta kasa bude idanunta,mugu ya tako inda take ya tsaya qerere a samanta yana dubanta ''da niyyar kasheki nazo ke da wancan wawan dan naki qauran mata,amma kunci darajar abinda yake cikin yarki wanda dana ne kuma jikanki,nasan kina jina don ban miki dukan da zaki mutu ba,amma zan baki zabi biyu,ko ki biyani kudina ko kuma na dauke yarki ta zama matarmu,na baki nan da kwana biyar kiyi shawara'' ya juya ya isa inda zubaida take ya dagata ya rungumeta yana shafa cikinta ''kada ki sake ki bari wani abu ya samu cikinan don ina buqatar wanda zai gajeni,duk dan kaza kazan(ya duro ashar) da ya kuma takuraki ki takashi kema yadda ranki keso''ya fada yana sakinta,ga mamakin adnan murmushi yaga tana yiwa mugu har suka juya suka fice daga gidan wanda shigowar mami suka yi kacibus suna ficewa a qasa ita kuma tana shigowa da motarta bayan ta faka motar cikin mamaki ta fito ta nufi gun security guda uku da su kadai yanzu suka rage a gidan cikin girmamawa suke gaidata don har yau suna son uwar gijiyar tasu,tambayarsu tayi ''wadan nan mutanen kuma daga ina suka fito'' daya daga cikinsu ne ya amsa mata ''daga cikin gida''fuskarta qunshe da mamaki ta sake tambayarsu ''cikin gida kuma?,gurin wa suka zo?'' wannan karon wani daban ne ya amsa mata ''gun hajiya nene,ai sun dade suna zuwa gunta,ko kin manta ne hajiya,kwanaki ke ta saka kika basu kudin mota'' cike da mamaki ta nuna kanta ''ni?ni kuma usaini?'' ''eh hajiya ke'' ganin sun zuba mata ido sunata kallonta sai ta dauko wani batun ''yanzu ina su samuel da ibrahim'' ''hajiya duk an dakatar da sh daga aiki,kuma da aka tambayeki kika ce kin amince,yanzu saura security biyar daga cikin goma sha biyar dake aiki cikin gidannan'' wani mamakin ya sake kamata,jinjina kai ta dinga yi don duka batasan anyi haka ba,ta yaya zata kori su ibrahim bayan sune manya manyan security na gidan tun zamanin alhj abdulkareem mai nasara na da rai,muta ne ne masu amana da cikon alqawari ''ka nemi numbers dinsu ka kira ka kirasu gaba daya kace ina son ganinsu daga yau zuwa gobe,wanda baka samu,contact dinshi ba ka dauki mota ka bishi inda kasan zaka sameshi'' cikin jin dadi yace ''yes madam'' don dukkansu suna fara ganin alamun lallai sauyi ne wata qila yake tunkaro gidan Har tayi gaba ta dawo ''kada a sake barin wani mutum makamancin wadancan mutanen su shigo gidan nan'' cike da bin umarni suka amsa waiwayo wa ta sakeyi ''amm...usaini,bama su ba duk baqon da za'ayi ku tabbatar da wane shi kafin shigowarsa gidan nan kamar dai yadda aka saba a daa''nan ma amsa mata sukayi a ladabce kana tayi gaba idanunta suka kai ga hanyar sashen abdallah,can qasan zuciyarta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138