Chapter 36
Chapter 36
tana ci gaba da dame gadon aikin da maryam din ta saki ''a'ah,maryamu kin gaji ne,idan ba dama sai na aika hindatu ta kiramin laure ta tayamu'' girgiza kanta tayi alamun a'a ''mama haka abu ya faru da jamila kuma dai?'' ''uwar asugwi din ta fesa miki din kenan ko''maman ta fada tana qarasowa cikin dakin,ta kama kunnen hindatu ta dan murde har sai da ta saki aiririyar qara tana dafe hannun maman ''don Allah mama kunne na,zaki tsinke kunnen autar taki fa ki rage mata kudin sadaki'' ''ai gwara in tsinke kunnen tunda ya iya jiyo gulma ya fadawa addarshi'' da qyar hindatu ta zame a hannun maman jikinta babu qwari haka suka dinga aikin,har ga Allah bata ji dadin mutuwar auren ba,tunda yau babu wanda,zaiso ace nashi ne kullum a bazawara,sai magariba uka kammala aikin komai yayi neat da shi,ta cire kaya jikinta ta daura zani da hijabi tq fito bandakin tsakar gidansu tayi wanka,tsakar gidan shuru da shi qwal kowa yana daka da mugun abinshi a zuciya,girgiza kai kawai tayi cikin zuciyarta tana fadin Allah ya gyara,sam rayuwar gidan nasu a karkace take kowa da inda ya dasa tasa alqiblar tana cikin sallar isha'i kiran abdur rahim ya dinga shigowa wayarta,hindatu ce zqune kan kujerar dq wayar ke kai don haka ta daga,bata ankare ba taji sun shiga hira da hindatu,dama gata gwanar surutu,sai da ta idar sannan ta miqa mata wayar,kasa dagawa tqyi saboda kunyar ama dake gurin,itama maman na ankare da ita amma tayi kamar batq gani ba,dn tasan maryq din ba boye mata zata yi ba,cikin zuciyarta take addu'ar Allah yasa mijin aure ne diyartata ta samu su ukun cikin kwano daya kamar ko yaushe suka ci tuwonsu na masara miyar busashshiyar kubewa,santi kawai maryam ke ti wa mama don tayi missing girkin maman sosai,mama gwana ce ba baya bace gun tsara girki musamman namu na gargajiya zumudi yasa hindatu ta kasa shiru jin addar tata taqi tada zancan mutumin da ya kira din dazun ''wai adda maryam abdur rahim din dazun fa yace saurqyinki ne,kuma naji shiru baki ce komai ba'' hara rarta tayi ''wannan baki naki hindatu kamar ba'a gasa miki shi ba?'' dariya suka sa su dukka ukun,tilas yanzun ta yiwa mama maganarshin tunda tun ajiyan yake jadda da mata aure yake son yayi bada wasa ya zo ba,a kunyace ta yiwa maman bayani,farinciki fal zuciyar maman ''Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa,ya kade dukkan sharri da fitintinu,addu'a ce yanzu kawai abunyi gareki maryam'' ''insha Allahu mama,sai a tayamu muma da ddu'ar''ta fada cikin karyewar murya wanda ke nuna raunin zuciyarta,tausayinta ya kama maman ''addu'a ta zama dole akan musulmi,ballantana uwa ga 'ya'yanta,wacce garkuwa kike da ita da zaki basu wadda ta zarce addu'ar,uwar ma irina mai yara mata da take musu fatan samu mazaje na gari nagartattu,babu sallar da zan idar da ita maryama ban muku addu'a ba,ku kadai nake da su fa'' wata iriyar qauna hade da tausayin mahaifiyar tasu suka lullubeta,haqiqa uwa ba wasa bace,wata ni'ima ce daga ubangiji,cikin zuciyarta take fata insha Allahu wannan karon zuciyar mqhqifiyar tasu zata wanke daga dukan wani quncin rashin auren nata,hawayen da suka tqru suka fara sauka a idanunt cikin dabara take sharewa don kada maman ta gqni hankalinta ya tashi kiran abdur rahim ne ya sake shigowa,wannan karon ba tare da jinkiri ba ta daga don so take ta kaucewa idon amman kada tqyo tozali da hawayen da takeyi ''ranki ya dade lafiya kike kuwa?''ya tambaya a sanyaye ''lafiya nake me kaji?'' ''muryarki ce naji tamin kama da ta masu kuka'' duk da yanayi da take ciki sai da murmuahi ya subuce mata ''idan banda abun abdul har yaushe kasan muryata da zaka tantance kuka nake yi?'' murmushi ya saki har tana iya jiyo sautinshi ''na dade da sanin muyarki maryam,ke dince baki sani ba,kina gidanku ko?''ya qarashe maganar da tambaya,cikin mamaki da sigar tambaya itama ta maida masa amsa ''wa ya gaya maka?''maryam,kina shakka cikin son da nake miki ko.....any way....naje gidanku ance min baki nan kina gun mamanki'' a wani mamakin ya kuma sakata,son iya saninta babu mai shigowa gidan su mamin ta sauqi ''ya akayi kasan gidan da nake zama taya kuma ka iya shiga da sauqi irin haka?'' ''maryam,duka abdul ba mai daukar abunda yake so da sauqi bane,yana bashi muhimmanci ne afili da boye,ina fata kin fahimceni?'' ''jinjina ga irin wanna son da abdul yake min'' ''jinjina ga zuciyar data sadaukar min da kanta''sai duka suka yi murmushi ''ina fata zuwa yanzu mutanen gida sun san da zama na?'' ''tun yanzu abdul,duka duka jiya fa muka hadu'' ''ke kika hadu da ni jiya,nikam ba tun jiya ba kika zama wani bangare daga jikin zuciya ta,so inason asan da ni maryam,aure nake so nayi da,wuri idan da ina da iko ma cikin watan nan banqi ki zama tawa ba'' tilas abdur rahim ya bawa maryam dariya ''gaskiya na baka sarkin zumudi na duk duniya'' ''na amsa tunda sonki ne ya ja min'' cikin qanqanin lokaci ya cika zuciyarya da farinciki ta mance duka abinda take ciki,ba dadewa da gama wayar tasu bacci yayi awon gaba da ita don tuni mami ta yarje mata tayi kwananta a gida washegari taa dawo 🎄🌲🎄🌲🎄 qarfe tara na safe ta gama shirinta tas,a falo ta taradda hindatu na shirya musu abun kari kan center table daya daga cikin abunda jiya ya zama mallakinsu cikin girmamawa hindatun ta gaidata ta amsa mata tana tambayarta mama ''mama na gurin baaba'' ''ya dawo ne?'' ''eh ya dawo dazu da sassafe,kin sanshi da tafiyar asubanci,yauwa tace idan kin tashi ki shiga ku gaisa'' ''yanzu kuwa''ta fada tana ciro wayarta dake tsuwwar shigowar saqo tana dubawa saqon barka da asuba ne aga abdur rahim,zaqaqan kalmomi da suka sanyata mirmushi ita daya tamkar wata zautacciya,tana mamakin yadda zuciyarta ta nutsu wa abdur rahim lokaci guda,sai da ta kammala karantawa ta masa reply sannan ta koma bedroom ta ciro dubu goma cikin kudin da mami ta bita kyautasu jiya dubu goma sha biyar mamanta inna haule baaba hadiza sai lubabatu jamila da shamsiyya su ta tarar cikin dakin,kallo banza uka suka bita da shi,gefan binta ta matsa zata zauna,cikin rashin mutunci bintan ta janye jikinta tana wani harare harare da kumbure kumbure gaida su ,bata da isar da zasu amsa mata har gara inna haule ta ama din sama sama,cikin girmamawa ta gaida baaban nata,ba laifi a sake ya amsa mata har yana tambayarta gun aikin nata,shiru ne ya biyo baya na wasu mintina sanan baaban ya dubi jamila ''inatambayarki tun dazu kun min shiru,yaro yace shi baisan lokacin da ya aureki ba,to inason in san ta yaya akayi ya aurekin,tunda shi ya rantse ya mayq bai san ke matarsa bace kuma bazai dawo dake ba'' cikin fitsara da rashin tarbiyya ta zumburo baki ''toni baba....ka tamvayi hadiza mana'' ya juya ga inna hadizan ''to kimin bayani tunda tace a tambayeki'' cikin borin kunya da haqiqancewa tace ''haba malam,wannan wane irin abu ne,ya zaka zo kasuwa ka dinga kwance min zani,sai da ka tara min idon duniya ni da diyata zaka hau bin qwaqwafinmu'' ''ke hadiza dubanni nan da kyau,na gaji da iskanci da rashin mutuncin yaran nan,jiya tunda naje qauye fita ta daya na gaza fita,zance
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138