Skip to content

Chapter 61

Chapter 61

Abadan Book One Complete Hausa Novel 1,295 words 0 views Progress saved
Download Book

🌺💖🌺 💖🌺 💖 © *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *_home of expert and perfect writers_* ▶4⃣0⃣ *_An karbo daga Abu Hurairah Allah ya qara yarda da shi,Manzon Allah S A W yace''ana bude qofofin aljanna duk ranar litinin da alhamis,sai Allah ya gafartawa ko wanne bawa musulmi indai ya kasance baya shirka baya hada Allah da abokin tarayya,sai dai wani mutum wanda ya kasance akwai qulli ko gaba tsakaninshi da dan uwanshi musulmi,sai ace''ku qyale wadan nan har sai sun shirya,ku qyale wadannan har sai sun shirya_* mami na gaba yana take mata baya,sai mita take masa na ya tasota tana cikin mutane,shidai baice uffan ba in banda murmushi da yakeyi,suka ahiga falo tana qoqarin zama yace ''a'ah mami mu qarasa daki'' ''kai abdallah.....abdallah trouble maker,muje dai inga suprise din nan da aka hanani sakat,amma ka tabbata indai bai kai ya kawo ba to zan ck tararka'' ''na amince,amma mami idan ya kai ya kawo din fa,me ni kuma za?a bani?'' ''sai abinda naga ya dace....'' ''zoben daddyn dake gunki kadai nike so'' hara rarshi tayi lokacin da take tura qofan bedroom din nata ''kayi kadan yaro,gwara ka fadi amount na kudi in baka da na baka wannan zoben,bakasan tarihinshi bane har yau.....'' maganar ta maqale mata saboda ido hudu da sukayi da maryam,jikinta a sanyaye hankalinta a tashe ta nufeta ta kama kafadunta bayan ta zauna kusa da ita ''maryam,lafiya?daga ina?,ya akayi ika baro gidanki a idin wannan lokacin?,ina fata ba matsala bace ta faru?,ina maigidan naki?'' ''gani...''taji ance,ta waiga da sauri don tabbatarwa,shaf ta mance ma tare da abdallan suka shigo sai da yayi magana harararshi tayi ''kaga malam bana aon wasa,fice min a daki zamuyi magana'' idonshi ya kanne guda daya h gami da daga girarshi ''wannu batu kam ai mu ya shafa mami,nima diyankin ne,nine kuma mijin diyar taki dai,tuwonki manki''yayi maganar yana zama kusa da mami hade da dora kanshi saman kafadarta suka sanyata a tsakiya Ba don murmushin dolen da maryam ta qirqira ta dorawa allon fuskarta ba da babu shakka mami qaryata abdallah zata yi,duk da hakan sai da ta dubi maryam din ''bana son shashanci,maryamu gayan meke faruwa?'' da sauri ya karbi zancan ''ko zan miki wasa kan komai mami bazan miki kan wannan ba,idan maryam bani ta aura ba ina zan ganta ma a irin wannan lokacin naje na daukota''sai ya dawo gaban mamin yayi zaman dirshan harda lanqwashe qafafuwa,ganin haka yasa maryam itama zamowa tayi irkn zaman da yayi gabam mamin,saidai ita zuciyarta cike take da rauni,badon namijin qoqarin da take ba wajen danne zuciyar tata ba da tuni hawaye ya fallasa fa,cike da salo na iya sarrafa harshe cikin nutsatstsiyar muryarshi yace ''mami,zai iya yiwuwa kiga na miki qaton laifi,zai iya yiwuwa ma daga qarshe kice sai kin hukuntani kan maganar da zan gaya mikin yanzu,maryam bata da laifi ko daya don ni na nemi a boye abun,mun fara son juna har ta kaimu ga buqatar muyi aure,na boye miki ne mami saboda ina sane da dimbin so da qauna da kike wa tilon danki,farinciki bazaya bari idan na sanar miki ba ki kasa sanarwa da wasu mutanen ba musamman wadanda muke zqune gida daya da su wadanda bana buqatar kowa ya sani cewa maryam nake da muradin aura saboda tsaro,mami kinfi kowa sanin irin traps din da na shiga,an farauci dayuwata ba sau daua ba ba sau biyu ba kuma sau uku ba,wadansu trap din sun yi aiki wasu kuma Allah ya kareni basuyi tasiri ba,na tabbata da ansan maryam ce wadda zan aura ba abun mamaki bane wani mummunan abu ya faru da ita'' ''mami...ga maryam nan ta sake dawo miki a karo na biyu,saidai wannan karon uasha banban da sauran lokutta,wannan karon ta dawo gareki da matsayi guda biyu,diyarki kuma aurukarki,nayi kwadayin ganin irin farincikin da zako shiga ta sanadiyyata ne mami shi yasa na sake dawowa da maryam cikin rayuwarmu,sanin maryam kikayi mami a fili amma a badini nafiki saninta kuma zuwa gobe zan warware miki ita don wace a sarari ki gani,ina fatan samu sassauci cikin hikunci boye miki wadda zan aura da nayi mami na'' ga mamakinsu saiga mamin itama ta sauko gabansu,hawaye ne bisa fuskarta wani na nin wani,a rude abdallah yasa hanninshi yana shate mata hawayen ''idan na bata miki mami kiyi haquri,hawayenki bala'i ne mami a gurina'' sai ta kasa cewa komai,jikinta ta janyosu gaba daya ta rungumesu ''barni abdallah na nayi kuka,kuka ne na tsantsar farin ciki ba baqinciki ba,tabbas addu'a bata faduwa qasa banza,na jima ina addu'ar Allah ya baka mace ta gari,lokacin da maryam ta shigo rayuwarmu na fuskanci dukkan halayenta na gari sai maji ina maka sha'awarta,domin hasken alkhairai da nake iya hangowa qunshe da ita,ganin hankulanku bai gamu guri guda ba yasa na fidda burin daga daina na dungumi yi muku addu'a gaba dayanku,kai har wayewar garin yau maryam ce a raina da ita na tashi har ka cimmani a kitchen tunanin maryam nake'' ta janye daga jikinsu bayan ta dauke qwallar idonta,kama hannun abdallah tayi da na maryam ta hade guri guda bayan ta dora nata a saman nasu ''na godewa Allah da irin wannan zabi da ya mana baki daya,naji dadi matuqa da kasancewarki maryam cikin zuri'ata,maryam,ga abdallah nan amana ce na baki ita har bayan raina,na baki amanar abdallah har abada,bani da kowa sai shi,ki zauna da abdallah cikin amana da aminci,abdallah kaima na baka amanar maryam,matuqar ka cuceta bayan zamowarka miji a gareta ban yafe maka ba,ku kula da junaku''abinda ta fada kenan tana jijjiga hannunsu Duk yadda yaso ya daure sai da ya kasa,qaunar shi da maryam qarara yake ganowa cikin idanun mamin,baiso maryam din taga kasawarshi saboda haka ya kifa kanahi saman hannun mamin ya sumbata cikin dabara ya goge qwallar idonshi ''nikam na dauka mami,na dauka,Allah ya tayani riqo'' ''kefa maryamu na?''ta fada tana kalllob maryam wanda kanta ke duqe take cure guri guda,abune goma da shirin suka cunkushe a qwaqwalwarta,zuciyarta na gaya mata wayo kawai abdallah yayi mata,mai yasa bata bar gidan salin alin ba tare da mami ma tasan wadda abdallah ya aura ba bare ta mata wanna kandagrakin mai daddaure jijiyoyin jiki?,zata iya watsawa mami mai dimbin alkhairai da karamck qasa a ido koko zata yarda ta zauna da abdallan ta sarayar da dukkan wani haqqi da 'yancinta da ya take,ya aureta ta sigar 'yar burum burum,zata barshi yaci nasara a kanta ya sameta a bulus ya sameta ta sigar qarfa qarfa da banga banga?,wani sashen na zuciyarta ke mata qarfafa ata gwiwar alqawari ya daukar mata,kuma ta riga da ta cika masa gabar farko na yarjejeniyarsu,bata jin kuma zai karya alqawarin daga qasa kuma hannunta yaketa yamutsa mata cikin wani irib salo da yake sa taigar jikinta tashi saboda nata hannun na kife ne cikin nashi tafin hannun,dob samun hanyqr tsira do son cire hannunta daga nashi tayi saurin cewa ''na karba mami,insha Allahu''cikin zuciyarta tana sauya qudirin ma'anar na karba in don kada Allah ya tuhumeta Mami dake sauri ta koma gun mutane sai gata ta rashe a cikinsu,hira sabuwa ta barke duk da maryam na rakube gefe guda,ga zaton mami surukuta ce da kunya irin wadda tasan maryam din ko da can baya da ita bare yanzun,saidai ga maryam kuwa takura ce data sanyawa

Table of Contents

Chapters

138 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138