Chapter 27
Chapter 27
washe baki ya shiga yi ''ah,lallai haihuwa mai rana,maryamu dukka haka,basuyi yawa ba?'' mirmushi ta danyi zuciyarta fal mamaki ''basuyi ba baba'' ''ah lallai wannan gidan aiki ya karbeki,to Allah yayi albarka ya bada miji na gari''ya fada yana irga kudin fuska qunshe da fara'a ko banza taji dadin addu'ar da yayi mata,tunda dai uba uba ne ba'a canzawa tuwo suna,sai take jin ranta yana mata dadi ina wuta inna hadiza ta saka maryam,qememe taqi karbar atamfar da ta bata din ai ita tafi qarfin atamfa wallahi,su yanzu atamfa saidai su bayar,ita kuwa huwaila hannu ta saka ta amshe kayarta tana tunanin gobe idan Allah ya kaimu taje kasuwar bakin rimi ta saida barta ko dubu biyar suka bata ta rage son tuni bokan uwani suka soma tatsarta,ita kuwa hindatu ta kalmashe tace gaba ta kaita, ''aikin banza aikin wofi,wa ma yasan daga inda kudin suka fito,an tura yarinya yawon karuwanci tana samo kudi tana kawo muku kuna karbewa an fake da gidan aiki aka kaita,a dai juri zuwa rafi da tulu diban ruwa wata rana zai fashe,ke kuma na dawo gareki munafuka makwadaiciya,an baki abu kinsa hannu kin karbe,to ni nafi qarfin atamfa wlh ehe'' ''Allah ko?,Allah sarki,mu gani a qasa mana wai inji kare ance ana suna a gidansu,idan akwai uwar makwadaita ta duniya to kece kakarta,kwadayin ne ya sakk cusa 'yarki inda bata da gurin zama,kuma da sannu unguli zata koma gidanta na tsamiya''ta yaue labulen dakibta ta shige tabar inna hadiza na ci gaba da babatu da sharrence sharrance kala kala lokacin da maryam ke sallama da mama tana shirin ficewa daga tsakar gidansu zuwa soron jamila ta danno kai zuwa,ta cake ado cikin wata yar ubansun shadda dinkin riga da skert na rashib arziqi,qam rigar ta kamata har boobs dinta na yowa sama,babu zancan mayafi sam atattare da ita sai daurin zamanin nan da ake kira ture kaga tsiya,waya take tana taku cikin isa da qasaita tamkar wata diyar qaruna ''yanzun nan na fito daga gidan mu hadu kawai a ni'ima guest palace din,amma fa gaskiya wannan karon bazan kuna ba gida zan koma,ok sai na iso''daidai lokacib da ta kammala wayar,bangazar kafadar maryam din tayi sannan ta juyo a wulaqance ta qare mata kallo,wata mahaukaciyar dariya ta saki tana ci gaba da kallonta ''sannu adda maryam,ana nan ana fama ko,ko da yake dai....''ta fada tana kuma kallonta daga sama har qasa ''ba laifi naga kin dan canza,ko an fara bin kwalta ne?'' waniabu ne ya tokarewa maryam dim maqoshi,rainin hankalin ya fara isarta dukan ya mata yawa,tayi mata uwarta ta mata,batasan lokacin da ta daga hannu ta zabga mata mari ba,ba ita kadai ba hatta da hindatu tayi mamaki,tsawon shekarun da suka dauka bata taba gwada yiwa wata cikin maraina wayon ta haka ba ''kan can uba,kut,me nayi miki,ko ko tsabar baqin ciki da qyashi ne...'' ''kika ci gaba da magana ina mai tabbatar miki zaki kwashi haqoranki a qasa,banza jahila dabba wadda batasan inda yake mata ciwo ba'' tsit tayi da bakinta don taga irin bacin ran da bata taba gani cikin idanun maryama ba,gaskiyar hausawa dake cewa wargi ma guri shika samu daga haka bata dada ba ta mewayeta tayi wucewarta,dadi kam tamkar maryama ta taka rawa saboda farinciki,mama ma wannan karon bata ce uffan ba,don tsan yau da gobe tafi qarfin wasa,fitarta waje babu inda idanunta suka kai sai kan jabir dake zaune mazaunin direba,idanunshi qur bisa qofar gidan tamkar dama an sanar da shi maryam din na fitowa,mamaki da tausayi suka cika maryam,jabir ne wannan,jabir ne ya koma haka,ina gayu davtsaftar jabir suka tafi?,me yake faruwa da jabir me ya sameshi?,mamakinta bai sake daduwa ba sai da taga ya dauke kansa daga gareta tamkar ma bai taba saninta ba cikin matuqar sanyin jiki take takawa har ta isa bakin titi ta tari napep tayi gida lokacin da ta isa gidan tuni anyi sallar magariba duhu ya riga ya shigo,ba haka taso ba taso ne ta koma da wuri ta dora musu dinner din,saidai lokacin ya riga ya qwace mata,kitchen din ta nufa kai ysaye bata ko doshi dakinta ba,mami,ce gaban gas din tana ta hidimar hada abincin,yayin da kuna dan shagwabar nata ke tayata da dauko wannan dauko wancan ''idan banda rigimar abdallah don Allah ina kai ina girki?,nace ka...''sallamar maryam ta katseta ''sannu mami da gida,har kin dawo?''ta fada tana ahirin amsar aikin daga hannunta ''yauwa maryamu ya kika barosu?'' lafiya mami suna gaidaki?'' ''kinga maruamu barmin nayi yau dai daya ki huta kema,nima na wasa qwaqwalwata ko?''mami ta fada tana hanata aikin da take qoqarib karba ''ayyah,mami da wuri ma naso na dawo lokaci ne ya qwace min'' tsaki abdallah ya ja hadi da barin miqo albasar da yakewa mami ya koma ya zauna ''ki bata mami aikinta ne,idan baki bata ba ma acikin albashinta na wani watan'' yau ranta abace yake tana jinta daidai da duk wanda ya taba tane,hakan ne yasa ta maida masa raddi ''babu damuwa,mami ina jinta ne tamkar mama na ne saboda haka babu ciniki tsakaninmu,ko ba kudi qimar shekarunta sun biya in mata aiki'' baki ya tabe kamar mace ''gaskiya ne naga kina amsar albashinki,ai da,sai kice kin yafe'' murmushi tayi cikin gatse,sanann cikin qasa da murya ta yadda mami da ta tafi sink wanke albasa ba zata ji ba ''kada ka manta haifata akayi yadda akayi yadda aka haifeka,aiki nake kamar yadda kake wa qasarka aiki da albashi ake biyanka,am not a servant,ciniki kuma ko tsakanin da,da uwa halas ne'' tofa baki yasan me zai fada tuni fuskar 'yan maza ta sake hadewa a zafafe yayi niyyar maida raddi saidai isowar mami gun ya katse masa hanzarinsa,tilas ya hadiye abunda ya qunso ''zan zuba miki albasar maryamu kafin nan ki shiga daki kin ajjiye kayan hannunki kin sauya kaya ko?'' ''to,mami na gode''maryam ta fadi gami da juyawa ta bar kitchen din,abdallah ya bita da kallon zaki san koni waye,yayin da ta daga kafadu alamun dake nuna masa am ready *mrs muhammad ce* [9/17, 12:52 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺🌺 🌺💖🌺💖🌺 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 🌺💖 💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖 💖🌺💖🌺 🌺💖🌺 🌺💖 🌺 ▶2⃣3⃣ *_an karbo daga abu hurairah Allah ya qara yadda da shi yace:manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gareshi yace: kalmomi guda biyu,masu sauqi akan harshe,mafiya soyuwa agurin ubangij,masu nauyi akan mizanin auna ayyuka SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI,SUBHANALLAHIL AZIM_* su biyu cikin falon misalin qarfe goma na dare,mami na bisa computer dinta tana tsara wata saminer da zasu gabatar yayin da maryam ke zaune gefanta tana tayata hira ''abdallah shiru bai dawo ba,halan yau aiki ne ya tasaahi gaba''cewar mami lokacin da take ci gaba da typing ''da alama''maryam tace mami tadan bar abunda take ta juyo da hanklainta ga maryam ''wai ni kam maryam meye matakin karatunki ne?'' murmushi ta danyi ''degre ce'' ''ta daya ko ta biyu?'' dan bude baki tayi alamun mamaki ''a'ah mami,ta dayan dai'' ''mai zai hana in maida ke makaranta ki samu wata degree din kan fannin kasuwanci?,na fuskanci kina da amfani matuqa atattare da mu,sa'annan ina buqatar mai kula da kamfanonin abdallah mai amana kamar ke,kamfanoni wadanda ya gada da kuma wadanda ya bude daga baya,ya kike gani maryam zaki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138