Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

Abadan Book One Complete Hausa Novel 1,259 words 0 views Progress saved
Download Book

da kuma tudu,idanunta irin idon nan ne da ake cewa oily eyes wanda zakayi tsammanin qwalla ko ruwa ne suka taru cikin qwayar idon,bata da baqin qwayar ido sosai,sanyin muryarta da zaqinta ke dada bayyana kyawun halittar da Allah yayi mata wanda hakan ya ja mata yawan masoya da maqiya ciki harda 'yan gidansu haka aka sha bikin yan uwan nata su hudu yayin da ita kuma ta duqufa karatunta,maryam badai qwaqwalwa ba,hakan ne ma yasa bata samu cikas ko ksdan a karatunta ba,cikin nasara komai ke tafiyar mata,janye jiki da masoyanta sukayi a lokacin bai dameta ba don dama bata buqatar wani damuwa karatunta ne kawai damuwarta,cikin nasara ta shige B U K inda anan ta samu shaidar degree dinta kan fannin girke girke ba jimawa,da kammalawa kuwa ta samu aiki da wani katafaren gurin cin abinci da shirya bukukuwa ,wanda cikin qanqanin lokaco ta samu matsayi mai girma na shugabantar dukka masu girka wani abunda za'aci ko a gurin ko kuma aka basu kwangilar yi na biki,qwazo himma gaskiya da amana su suka jawa maryamua wannan matsayin wanda hatta da wadda ta kafa gurin *HAJIYA ATIKA ABUBAKAR BAFFA* ke qaunarta ta bangaren 'yan uwanta kuwa saidai ace Allah ya rufa asiri kawai domin dukkaninsu cikin shekara guda babu wadda bata da tabon saki wanda tsantsar rashin tarbiyyarsu ya hanasu zaman arziqi da mazajensu,a haka dai ake gurgurawa har kawo wannan lokaci,hankalin maryamu bai fara tashi ba sai da aka zo auren qannanta zagaye na biyu wato *azara* *shamsiyya* da *maraqisiyya*,tsantsar gori habaici da baqar magana idan da tana tsiro a lokacin to da tuni ta yiwa maryam,sai Alla ya halicceta mai haquri da kawaici hakanne yasa bata fiya zafafawa kan lamuransu ba,idan suna yi dauke kanta take kamar yadda tun usuli ta tashi taga mamanta nayi samuwar aikinta ya taimaka qwarai wajen kyautatuwar rayuwarsu,wanda alfanun ilimin da ta gani ya sata jajircewa da tsayawa qanwarta daya tilo don ganin itama ta amfana,duk lokacin da ta daki albashinta bata fasa siyan wani muhimmin abu ta kaiwa mahaifinta ko ta ciri kidin tsaba ta bashi,babu kuma wani jin nauyi zaisa hannunshi ya amsa da sunan ai yarshi ce,haka rayuwar maryamu ta taso cikin tsangwamar *'yan uba* wanda har yau ita take gani ba kuma tasan ranar qarewarta ba _*WANNAN KENAN*_ *Mrs muhammad ce*πŸ‘‘ πŸ“šπŸ“šπŸ“šβœπŸ»βœπŸ»βœπŸ» [9/17, 12:50 PM] 80k: πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’– 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺🌺 πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’– πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’– πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ πŸŒΊπŸ’– πŸ’– 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’– *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ πŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ πŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’– πŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ πŸŒΊπŸ’– 🌺 β–Ά8⃣ Cike da tawakkali da yarda da qaddara ta miqa dukkan lamarinta ga Allah,a yanzu kam ta sanya jabir ne kawai cikin addu'o'inta kamar yadda raliya ta shawarceta,domin tausayinsa ne fal cikin zuciyarta,tana ji a cikin zuciyarta ta sanadinta ne ya afka wannan qaddarar abu guda ne ta kasa tinsa komawa walwalarta da aikinta tamkar,yadda take yi a da duk da yadda take son aikin,ta barwa ranta cewa ta ajjiye aikin zata kuma jira har lokscin da ubangiji zai musanya mata da da wani mijin ko da baikai jabir dinta ba πŸŒ²πŸŽ„πŸŒ²πŸŽ„πŸŒ²πŸŽ„ misalin biyar da rabi ne na yammaci,zaune take a rumfar tasu wadda ta sha mopping tayi fes,dai qamshin turaren tsinke take,mamanta na dakin babansu tana gyarawa don ita ta amshi girki,don sam bata lamunce don ranar girkinta bane ta tura yaranta su share dakin baban nasu ba kamar yafda taga su huwaila nayi tsabar ganda,yayin da hindatu ke makarantar islamiyya sanye take da maroon din material dinkin doguwar riga da yake ma'abociyar son dogayen riguna ne ko don tsahon da take da shi,yatsunta sunyi kyau da jan lallen da tadan qunsa iya yatsu,a lokaci irin wannan idan bata da abinda duka zatayi,taka duqufa wajen research din girke girke a daga sashukan dake watso kalolin abinci na qasashe daban daban,kadan kadan hankalinta ke rabuwa gida biyu,wani lokaci yayi tsakar gida da yaran inna hadiza keta faman ta'adi cikin falon gyatumar tasu da hayaniya na 'yan fadace fadace atsakaninsu kuma babu wanda ya isa yace zai tsawatar musu cikin haka ta jiyo sallamar inna hadizar,abu na farko da ya biyo bayan sallamarta shine ashar da ta dura wanda har sai da maryamu tayi ta'awizi cikin zuciyarta ''kaga tsinannun yara shegu,ke balaraba da na bar muku dakin a bude shine kuka maida min shi sansanin fada da kokaye kokaye,kuma saboda tsabar baqincikin Allah yayi maka arziqi a rasa mai tsawatrwa uaran salon su fasa ma abu kosu lalata ma su jawo maka asara,dadin abun ma yanzu kana da arziqin da zaka gyara'' sarai mama tasan da ita take amma kasancewar ko da can ma da jini ajika ba kula shirginta take ba yasa yanzun ma tayi mata dif,saiga huwaila ta fito daga wanka takalleta ''a'a,ina kuma kikaje?'' ''yo ina kuwa zanje da ya wuce gidan doyar albarka jamila''ta fada tana shirin shigewa dakinta sakwatoto huwailan tayi ''amma inace baki tafi ba don wanna wanka da nayi na shirin zuwa ne,tunda munyi tare zamu je'' ''kiji hiwaila da wani zance,don,lawai zaka girin naka sai ka jawo bare?''binta wadda tare suka je da innar tata ta maidawa huwaila raddi ''kinga ba dake nake ba 'yar ayi jikar na saba'' ''a'a,dakata don ta fadi gaskiyarta,kada kiyi haushin kaza huce kan dami''inji onna hadiza cikin salon tare mata ''au bayanta kike goyo kenan?'' ''qwarao,yo akan me?'' baqinciki ya,hanata cewa komai sai qwafa kawai da ta ja ta shige dakinta qarar wayarta ce ta sata dawowa daga diniyar da su inna jadizan suka shigar da ita,a kullum kwanan duniya sake gasgata zancan raliya takegame da abinda ya faru tsakaninta da jabir,jikinta a sanyaye tabi wayar da kallo ,da kamar ba zata daga ba amma ganin sunan *mama* ya sata babu jinkiri ta daga,cike da,girmamawa take gaidata ''babu abinda zaki cemin maryamu,wa yafi qarfin qaddara a rayuwa?,abun nan ya riga ya wuce addu'a ce kawai mafita,amma anyi anyi ki koma gun aikinki kinqi,na tambayi haj rabi ko wani laifin aka miki sunce babu komai,ko an miki wani abu ne agun?'' cike da girmamawa tace ''babu abinda aka yimin mama wallahi'' ''to shikenan,indai da gaske haka ne kizo gobe gida ki sameni da la'asar,da akwai aikin da aka samu kuma gaskiya a iya hasashena babu wadda ta dace da aikin sai ke,don na yaba qwarai da tarbiyya gaskiya da riqon amanarki'' ba zata iya musu da mama ba wato hajiya atika abubakar,banda haka da wata ce zqta ce mata ta gode bata buqata,amma girmanta da qaunar da take gwada mata ta wuce haka a gurinta don haka tace ''to mama,na gode Allah ya saka da alkhairi insha Allahh goben ina hanya'' ''to shikenan a gaida mutan gidan'' ''zasu ji insha Allah'' ta sauke wayar tana jin wani abu na dan taba zuciyarta,mama da bata kima da shigowa ba tace ''ke da waye?'' ajiuar zuciya ta saki ''haj atika ce,wai tana nemana gobe'' ''to Allah yasa lafiya,ko zancan komawarki ne gurin aikin?'' ''a'a,tace wani aiki ne ya samu,amma sai naje goben zanji'' ''Allah ya rufa asiri ''ta fada maman tana ficewa dauke da wankakken zanin gado da rigar filo murmushi maryam tayi tana jinjina kai,wato miji da mata sai Allah,maman ta tana burgeta matuqa,bilhaqqi take kula da mijinta,bata duba komai sai zatin Allah da kalmar nan ta *aure bautar ubangiji* πŸŽ„πŸŒ²πŸŽ„πŸŒ²πŸŽ„πŸŒ² washegari ta shirya tsaf cikin

Table of Contents

Chapters

138 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138