Chapter 113
Chapter 113
falin qasa ta zauna saboda maryam din ta fara jiyo kakarin amai,da hanzarinta ta shiga dakin,ita ta wanke gun data bata din ta maidata gado ta kwantar tana mata sannu,ta taba jikinta kana cikin damuwa tace ''maryam anya ba ciki gareki ba kuwaοΌ'' duk da tana cikin ciwo sai da tambayar tq bata kunya,tayi qasa da idonta tana girgixa kai,sake matsowa mamin tayi tana lallabarta ''kada kiji kunyata idan shine ki gayan kada na yita baki magunguna muyi asararsa don Allah'' nan ma kai kadai ta iya girgiza mata ta kasa hada ido da ita ''to shikenan,allura dama zan miki naji zazzabin yaqi sauka'' sam bata qaunar allura,da kayi mata allura gwara ka zabga mata mari,ita ta sani ciwonta ba na magani ko allura bane,da sauri cikin murya ta marasa lafiya tace ''don Allah mami ba yanzu ba,a barshi sai anjima zai iya sauka''ta fahimci allurar ce bata so don haka ta qyaleta ta sake bata wasu magungunan Ranar kam har kusan biyu na dare ana fama,qarshe dai allurar da bataso mamin ta mata,bayan tasha fama da ita kafin ta tsaya din,sai kusan uku saura na dare ta samu bacci ita kuma mamin ta koma dakinta ππππππ A daddafe ta tashi tayi sallar asuba sakamakon baccin daya cika mata ido,duk da zazzabin ya sauka baki daya sai ciwon kai dake son matsanta mata kuma,da qyar ta gama sallar ta kwanta saman daddumar zuciyarta babu dadi,duk wani minti idan ya wuce sai taji kamar yana sake nesantata da abdallah ne A hankali taji an turo qofar dakin,ta daga kai tana amsa sallamar da akeyi,mami ce cikin hijabinta da carbi a hannunta da alama idar da sallarta kenan itama,tayi qoqarin tashi zaune don gaisheta mamin tace a'ah yi kwanciyarki,a haka suka gaisa ta duba jikin taji babu zazzabin,shuru tayi bata ce mata kan nata na ciwo ba din kada ta daga mata hankali ''yanzu maryamu jinkirin dawowar abdallah yasa kika matsantawa kanki da damuwa haka har da ciwoοΌ,lallai ba shakka gaba guduwa zaki dinga yi kibi mijinki kuna barina kenanοΌ''ta fada cikin tsokana da zolaya,kunya ta kama maryam sosai,ita kanta batasan tana misbehaving har haka ba,batasan ya akayi abun ya hudata haka ba har yake bayyana kanshi da kanshi ba tare da ta sani ba. ''a'ah daina jin kunyata,ni hakan dadi ya yimin sosai,Allah ya qara hada kanku,aikin da yayi ne ya tsaudashi jiya kafin na kwanta saiga kiranshi,amma alhamdulillahi an samu nasara ya kama dukkan jama'ar daya shirya kamawar sai mu yiwa Allah godiya'' hakanan taji wani sanyi na sauka tun daga kanta har tafin qafarta,a gida ko a waje abdallah jarumi ne tabbas babu kokwanto,a hanakali cikin zuciyarta ta dinga fadin alhamdulillah ''sai ki kwanta kiyi naccinki sosai,kiyi bacci harda minshari ko''ta sake fada cikin zolaya,murmushi tayi tana sake sunkuyar da kanta mamin ra mata sallama ta fice Ta lumshe idonta tana jin wani shauqi na kamata,duk da ciwon da kanta yake murmushi sai daya subuce mata,ta dan dafe kanta idanu a lumshe,a hankali bacci mai dadi ya sureta ππππππ Sannu a hankali taji yanayin baccin nata na sauyawa,ta dinga bude idanunta a hankali har ta kammala budesu tas,yana zaune gefan gadon nata sanye da baqar jallabiya mai hula irin ta maza ya zuba mata idanu kamar wanda aka bashi aikin zana fuskarta,wani abu mai kama da farinciki taji ya ratsata ''welcome dear''ya fada a nutse ''an tashi lpy gimbiyaοΌ''ya tambayeta idanunsa har yanzu na kanta,kasa amsawa tayi sai cusa kanta da tayi cikin hijabinta,yayi maganar amma taqi dagiwa sabida haka ya tashi tsam ya koma gabanta yana qoqarkn dago fuskarta amma ta qiya,shima bai sakar mata qarfi ba ya qyaleta yana fadin ''kin daga min hankali da yawa baby,tun asuba na baro abuja duk sabida nazo na ganki amma kin min rowar fuskarki,shikenan na gode''ya fada yana miqewa zai fice a dakin,sai ta bude ido daya taba satar kallonshi tamkar ta tsaidashi tana kallo ya fice a dakin a hankali kamar wanda aka qididdigewa iya takun da zaiyi Kunya da tsoro ranar suka hanata sakewa ko fitowa,sai taci gqba da kwanciyarta kan gado abinta mami na kulawa da ita a tsammaninta jikin da saura,tana son ta fito ko zata sake ganin fuskarshi amma kunya ta hanata,tana jiyo muryarshi a falo lokaci lokaci shida mami suna maganar bangaren nene da ta ga ana sawa sababbin furniture _WASHEGARI_ Tas ta jita ta warke sosai,ko guntun ciwon kan ma babu shi,qarfe tara ta hada ruwa mai zafi tayi wanka,muradin ganin abdallah take,shi kuma kamar ya sani tun jiyan bai sake leqota ba duk da ya turo mata guntun sms _sorry dear na zama busy kan wani abu,see u later_,iya abinda ya turo kenan Ta shirya cikin atamfa riga normal da zani rafa,tayi lite make up kana ta feshe jikinta da turaruka masu dadi,ta daura dankwalinta bayab ta gyara gashinta kai azabar santsi ta hadeshi da ribbom madaidaici,haka nan ta tsinci kanta da yin kwalliyar,ba qarya ta mata kyau matuqa,muryarshi da jiyo a parlour ta haifar mata da fargaba,sai ta koma bakin gado ta zauna ta fasa yunqurin fitar da takeyi,ta dauki wayarta ta fara danne danne kanta a qasa Raliya take turawa tex don taga missed call dinta na kiran data mata tana bacci A hankali taji ana taba qofar kana aka turota,cikin qananun sakanni tattausan qamshi ya buwayi hancinta,qamshi ne mai kwantar da rai tamkad zai saka bacci a nata bangaren wani shauqi ya qara mata,kallo daya ta masa ta sauke idanunta qasa,kunya take ji sosai,ga wani maganadisu dake fisgarta cikin idanunshi,wani kyau na musamman taga an qara masa,gani take kamar mami ta gaya masa sirrinta,nauyin hada ido take da shi,yayi kyai sosai cikin light blue din shadda,babbar riga da yar ciki da wando,fadan irin kyawun da shaddar ta masa ma bata baki ne,shadda ce yar ubansu sai maiqo take tasha bugu,a hannunshi riqe da hularse,a gogone baqi a hannunshi na fata na kamfanin armani sai takalminsa half cover irin na maza,sai ya tashi sak dan kano don ba baya bane su wajen iya wankan shadda suna sahun gaba,ba qaramin amsarsa shigar tayi ba,do da wuya ya sanya kaya komai rashin kyawunsu suqi amsarsa ,fuskarsa cike da murmushi mai bayyana sirrin kyawunshi ''amincin Allah ya tabbata a gare ki baby,ina fata kin wayi gari cikin qoshin lafiya,af kice ma anko mukayi''ya fada cikin zolaya,sai a sannann ta dubi kalar atamfar da ta saka blue ce da baqi,duk da blue din ya dan dara nashi turuwa da kadan qarasowa yayi bakin gadon ya tsugunna kana ya dafa cinyoyinta,abinda taji a jikinta shima shi yaji,sai tayi saurin zame hannun nasa,dauke hannun yayi yayi murmushi yana yiwa hular hannunshi kari ba tare da ya dubeta ba ''am too busy jiya naso inzo in sake tozali dake,ina daya bangaren can ana jeran amaryata'' sai tayi dumm ta rasa yadda zara fassara maganarshi Ya miqe ya isa gaban madubinta ya daidaita hular bisa kanshi kana ya sake dawowa inda take ''wanne saqo kike da shi gun imna wuro,qauyen ni'ima zamu je,yau idan Allah ya nufa zan zama angon mero'' batasan lokacin da ta daga kanta ba,ta yi masa wani birkitaccen kallo ido cikin ido,wani irin zazzafan kishi baqinciki da takaici ya lullubeta ''naga kina duba na maryam idan da magana kiyi''ya fada yana sake matsowa kusa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138