Skip to content

Chapter 119

Chapter 119

Abadan Book One Complete Hausa Novel 1,294 words 0 views Progress saved
Download Book

cewa komai ba ta taimaka mata tare da koya mata wasu dabarun data fusknaci meron bata sani ba,ta tausaya mata tsoro ya sake cikata,jikinta duk yayi sanyi saidai bata nunawa meron ba din kada ta karya mata gwiwa,haushin labaran ya kamata,me yasa sam su,basu da haquri,atleast ai ya bari yan uwanta su koma Kukan mero yaqi qarewa,zama tayi ta dinga mata bayani sannu a hankali ta fahimceta,ta samu ta daina kukan bayan digon bayani data mata,duk da ita ma ba sanin wani abun tayi ba ga kunya na yadda zata mata bayanin,bata kai ga tafiya ba kiran abdallah ya shigo wayar ta,da sallama tare da sanyin jiki ''shine kika gudu ko?,idan kin gama da maryar labaran din kicewa mami na fita amma bazan jima ba zan dawo,shima gashi nan muna tare ki gayawa amaryar tasa''kunya ta cikata kada dai ace ya sani abdallan,kamar kuwa ya san me take tunanin yace ''ba wani,abu yace da ni ba,nina fuskanta da kaina,naga kuma yana buqatar training,so kada kunya ta ta qaran miki akan ta da''ya qaraahe maganar yana dariya ciki ciki A sanyaye ta sauke wayar a kunnanta,ji take ma kamar ita yakewa dariyar,ta dubi mero dake kwance hajaran majaran ta miqe ''maigidan naki sun fita da abdallah,zan je mu gaisa da su mami,amma dole ki dinga qarfafa jikinki kada ki nunawa su inna wani abu kin fahimta''kai ta gyada mata ta yi mata godiya ta fice Tuni har sun tashi,kasancewar mutumin qauye ya saba da tashin wuri,baya malalacin baccin nan na bayan sallar asuba,Allah ya taimaketa mami bata fito ba,don haka anutse suka dinga gaisawa daga bisani ta shige dakin da inna wuro take. *mrs muhammad [truncated by WhatsApp] [3:19pm, 10/12/2017] HugumaπŸ‘‘: πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’– 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺 πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’– 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 πŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ πŸ’–πŸŒΊπŸ’– πŸŒΊπŸ’– πŸ’– *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’– πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’– πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ πŸ’–πŸŒΊ πŸ’– Β© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*πŸ’‘ *_home of expert and perfect writers_* β–Ά6⃣3⃣ *Daga jabir dan Abdullahi R A yace:naji Manzan Allah S A W yana cewa ''((idan mutum zai shiga gidansa sai ya ambaci sunan Allah yayin shigar tasa da yayin ci abincinsa,sai shaidan yace:baku da abinci baku da gurin kwana(a cikin gidan),idan kuma ya shiga ba tare da ya ambaci sunan Allah ba yayin shigar tasa sai shaidan yace:kun samu gurin kwana,idan bai ambaci sunan Allah ba yayi da zaici abinci sai yace(shi shaidan din):kun samu gurin kwana da abinci))* Tana dakin suna ta hirarsu da inna wuro mami ya shigo dauke,da kwando wanda ta zuba kayan breakfast a ciki na inna wuron,da sauri maryam ta tashi ta amsheta kamta aduqe tana gaidata,ta amsa mata asakekamar kuma ba aurukarta ba yadda dai sjka saba,zama tayi itama aka soma hirar da ita duk da maryam taja bakinta ta tsuke,saboda kunyar mamin,sai ta tsugunna tana hadawa inna wuro tea. ''ni inna wuro dama zamanki kikahi wlh damu,da kiwa,naji dadi sosai''inji mami,kama bakinta inna wuron tayi ''rufani ki saya ni bintu,ina ni ina zaman maraya,wannan ao saiku,dubi fa don Allah wai wannan ruwan ahine karin safenku,ina kuwa zakuyi qwari''ta fada tana nuna tea din dake hannun maryam tana figita mata,dariya ta basu,baki daya,kai imna wuro nanu dama,duk yadda mami taso ta yadda tayi zamanta aje a taho mata da tsoho alhajinta sam ta qiya. ''amma dai inna ai kya zauna har a raka mairamun taki nata gidan anjima ko,ku gano nata dakin''maryam dake gefe gabanta ya fadi,sai walwalarta ta ragu,tsoro ne fal ranta ''nan fa daya,nifa yau sai qauyen ni'ima bintu''da qyar tasha kanta amma fa saidai a rakata taje ta gano don babu faahi yau zata koma,ta bar tsohonta shi kadai a gida(hmm,mata irin na da kenan masu iya tattala miji da bin umarni) ''kema sai ki zauna ki karya don hajja laila ta iso yau takeso itama ta koma audan din,tana can gun takwararki ana mata gyaran jiki da qunshi,sai kije can ki samesu don nan ba zaku sake na saboda mutane''kamar an dira mata dutse haka taji ta amsa da ''to'' ''sannunki bintu,ke dai kin zama uwar kowa kenan,kin kama kowa kin riqe kamar yadda hausawa suke cewa da na kowa ne,arziqinki na kowa ne,Allah ya albarkaci rayuwarki data yaranki,da za'a samu ire irenki cikin al'umma su wadata da an bar kukan yunwa qunci da talauci,Allah ya jiqan mai gidanki''inji inna wuro ''ameen ameen inna,ai shi arziqi da Allah ya baiwa dan adam tamkar ka dauki wani abu ne mallakinka ka baiwa,wani kace ya amfana ya kuma amfanar da wasu,muma aro Allah ya bamu da rabon mu aciki da rabon wasu,ma'ana ka ci ka ciyar da wasu,ruwanka ka ci kai kadai ka tashi ran qiyama cikin wahala,don Allah na narka dukiyar ne ya dinga maka azaba da ita,abinda ka bayar shine rabonka don shi zaka taras a cikin littafinka ranar gobe qiyama,wanda kaci kuma banza ne don na wani ka yiwa ba bare a rubuta maka ladar ka ciyar da dukiyarka ga wani,kai kanka baka da tanbas din dawwama cikin dukiuar,wataran Allah na iya karbe kayansa ya baiwa wanda yaa dama,ko ka muti kabar zuriya to baka aikata alkhairi na wa kake zaton zai kula maka da su?'' ''wannan haka yake binta,Allah kasa mu dace''inji inna wuro,maryam na gefe tana jinsu ita kanta addu'a takewa mamin cikin zuciyarta,ko bata taba mata komai ba ta haifa mata *GWARZON MIJI DAYA TAMKAR DA DUBU ABDULLAHI BAWAN ALLAH*,bare babu irin halaccin da bata mata ba,mami mutum ce wadda samun kamarta zaiyi wuya ruwan shayin kawai ta sha taji cikinta gaba daya ya cushe don haka ta fice tabarsu adakin,dakinta ta koma tayi wanka ta saka baqar doguwar riga don kada kayan ta su baci garin lalle,can ta tars da haj laila tana hada lallen qunshi,tuni mero an shige cikin dilka da kurkum ga bayaga halawa da aka sha. Ita kanta kasa gajiya tayi da sabawa fatarta sabulu saboda wani irin santsi da taji tana yi na ban mamaki,itakam dama ko ba'a gama gyaran jkkin nan ba a yau zata cewa haj laila abarta haka,tana kallon yadda mero keta fama ina ga ita,fitowarta kenan haj lailan ta miqa mata wani anu cikin cup sai qamshin citta da kanunfari yake tace ''shanye diyata''haushi ma kamata yayi bata ce komai ba tayi kurba uku ta faki idonta ta fita da shi da niyyar zubarwa cikin garden na gidan ta shiga ta daga zqta fara zubarwa taji an riqe hannunta,a hankali ta dago kanta sai suka hada ido,sanye yake cikin suit baqi da ja saidai yar saman ya cireta tana singalalin hannunshi,da alamu har ya dawo daga fitar da yace mata zaiyi sai da ya mashe mata ido daya sannan yace ''shigowata kenan naga wani haske ya cika gidan nan,ina waiwayawa naga ashe kece,shine na biyoki ina fata banyi laifi ba''ya fadi maganar yana qoqarin amshe cup din daga hannunta,tana qoqarin boyewa ta bashi amsa ''um um,ko daya bakayi laifi ba'' ganin yana qoqarin maida abin babba yana son ya rungumeta yasa ta sakar masa cup din a sauqaqe,sai ya leqa ciki yana fadin ''hala wanann abun dadi ne mami ta baki ko,Allah yayi da rabo na kenan nasha?''ya tambayeta yana kallonta,wani irin kyau yaga tana fitarwa,tambayar kawai yayi amma bai gane me yake fada da sauri ta girgiza masa kai ''a'ah,kada kasha'' ''why?,muba muta ne bane''yayi tambayar yana dan zaro ido gami da dage gira.

Table of Contents

Chapters

138 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138