Skip to content

Chapter 133

Chapter 133

Abadan Book One Complete Hausa Novel 1,287 words 0 views Progress saved
Download Book

cikin asibitin,daki daki suka dinga bi suna raba taimako,kudade ne masu tsoka suka dinga bayarwa tare da biyan kudin magunguna ga duk wanda ya kasa biya,wayyo Allah,kada kaso kaga abun tausayi kala kala,talakan qasata yana cikin wani hali,talauci yunwa fatara jahilci duka ya tattaru ya narke a kansa,wasu har kukan dadi suka dinga yi,maryam kuwa tuni zuciyarta ta karye,tunvtana share hawayenta a boye har ta saka kuka saboda azabar tausayinsu,abdallah ne ya fara jin sheshsheqarta,gefe ya janyeta hankalinsa a tashe ''sai da nace kiyi zamanki a gida dear kkka ce sai kinzo bayan ba lafiya ce da ke ba,sai na maida ke gida idan ba zaki iya jurewa ba''da sauri ta goge hawayen tana danne kukan din batason ya maida ta din,ganinsu na qara mata imani tare da godewa Allah kan matsayin da take kai,ya zabeta ya dorata ba don tafisu ba,ta yiwuwu a cikinsu ma akwai wadanda suka fita kusanci da Allah amma ya jarrabesu don ya sake tabbatar da imaninsu da shi,duk da haka fakar idinsa ta dinga yi tana goge hawayen ta handkherchief sabida abun tausayin ya isa A haka suka gangara dakin 'yan haihuwa,tsoro ya kama maryam sosai ganin masu larura kala kala,akai kai ta dinga gigr hawayen nata wanann karon,ta tsorata sosai da haihuwar,daga bakin wani daki suka ga jama'a tsaitsaye agun anata hayaniya,mami ta tambayi jama'ar dake tare da ita,daya cikinsu ya mata bayani ''yarinya ce aka kawota daga gidan mahaukata zata haihu,ta jima agunsu ana bata magunguna ashe ba mahaukaciyar ba ce,to da suka kawota sai kuma suka yi tafiyarsu suka barta,kuma bazata iya haihuwa da kanta,ba don bata da isashiyar lafiya da zata iya jurar naquda,shine ake ta neman wanda zai sanya hannu kan fike din da za'a mata aikin an rasa mai yin signing tunda ba'asan kowa nata ba,shine aka fito da ita daga gadonta aka sanya wata akai kafin asan yadda za'ayi da ita''haushi takaici da tausayin yarinyar ya kama mami duk da batasan ko wacece ba,fada ta dinga yi sosai ''saboda tsabar rashin imani,ko cikinku ai a samu mai saka hannu dai,sanadiyyar haka fa tana iya rasa ranta,kuma idan ta mutu shikenan ta mutu a banza sabida bata da gata bata da galihu ko''da wannan fadan da takeyi suka qarasa gun da take kwance tana matagugu Ba qaramin tsorata mami tayi ba da ganin zahariyya kwance male male cikin wani mawuyacin hali,batasan lokacin data isa gareta ba tana kiran sunanta saboda tsabar tqusayinta daya kamata,lokaci guda ta manta duk wani abu da sukayi mata ita da uwarta,kafin ta qarasa gabanta abdallah ya shiga tsakaninsu cikin tsananin nacin rai yana girgiza kai,tuni,idonsa ya sauya kala ''kada ki isa gareta mami ki barta don Allag,wannan shine sakamakon abinda ta aikata a rayuwarta,kallo daya zaki mata ki tabbatar cewa sakamako take karba'' tsawa mamin ta daka masa''matsa daga gabana kafin na tsinka maka mari abdallah,baka da hankali ne?,kasan naquda kuwa?,kasan irin azabar da take ji yanzu haka?,ciwon 'ya mace na 'ya mace ne''cewar mamin cikin fushi,ba musu ya kauce ya bata gu don baison bacin ran mahaifiyarsa Ba qyamata ko tsangwama mami ta tattarota jikinta cike da tausayi,suna hada ido da mamin itama ta fara kiran sunanta,fadi take mami ku yafemin keda abdallah,kuyafemin mami mutuwa zanyi,tuni mamin ta bada umarni aka dauko gado don dorata a ahigar da ita tiyatar gaggawa,ana shirin daujarta tace ta saki murmushi tana kallon mamin ''mami,dama qyaleni kukayi kada ku bata lokacinku,don nasan cewa mutuwa zanyi,kuma ina farinciki da hakan,ta yiwuwu Allah ke sona yayi nufin wankeni daga zunubaina da zai dauki raina ta hanyar naquda,mutuwata a yanzu ta fiyemin rayuwata mami'' tuni hawaye ya cika idon mamin,duk da haihuwa daya tayi amma har yau bata mance zafin naquda ''ki daina fadar haka zahariyya,mata nawa ne suka haihu gasunan lafiya da su,ciwo ai baisan inda rai yake ba saidai idan kwana ne ya qare''sai taga idonta na kallon wani guri ne daban,a hankali taji ta ambaci''habiba'' duka sai suka juya,wadda aka ambata da habiban ce ke qarasowa inda take,zubewa tayi a gun tana kiran sunan zahariyya,ba wanda yasan alaqar dake tsakaninsu don haka mami ta sake bada umarni a dauki zahariyya a wuce da ita dakin tiyata,da sauri zahariyya ta tsaidasu ''mami,na fada muku wallahi a yau zan mutu bazan sake kwana ba aduniya,da tiyatar da zq'ayimin gwara ki barni nayi magana da wanann baiwar Allahn''jikinsu gaba daya yayi sanyi don haka mami ta matsawa habiba ta iso tana zubar da qwalla ''zahariyya,naga sakayya ta daidai abinda na aikata a rayuwata,aahe da gaskene son zuciya bacinta?,ashe da gaske idan baka godewa Allah ba zaka godewa azabarsa?,ashe daidai ne da ake cewa idan zaka gina ramin mugunta ka ginashi gajere wataqila kai zaka iya fadawa?,tabbas Allah ba azzalumin sarki bane kuma baya zalunci saidai bawa ya zalunci kansa......'' *mrs muhammad ce* 📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺 💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖🌺💖🌺 💖🌺💖 🌺💖 💖 *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 🌺💖🌺💖🌺💖 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 💖🌺 💖 © *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *_home of expert and perfect writers_* ▶6⃣8⃣ *Fiyayyen halitta dan gatan Allah Annabi muhammad S A W yace:((idan wanda kuka yarda da addininsa da halayensa/dabi'unsa yazo muku(neman auren 'ya'yanku)ku aura masa,idan ba haka ba☝🏽(kuka hanashi),FITINA DA FASADI MAI GIRMA ZAI YADU/WANZU A BAYAN QASA))* Juya kai kawai zahariyya take don ta qagu taji me ya faru da hqbiban duk da azabar da take ji,cikin kuka habiban ta dora ''na koma gaban mama na da baaba na,ba qaramin farinciki mahaifina yayi ba don ga zatonshi sace ni akayi tunda mamana tace masa bata nayi,haka nan itama mama tayi farinciki,tace nayi shiru da bakina kada na sanar da kowa halin da na fada da sanadin shigata wanann rayuwar da nayi,da na murmure zan koma gidan mijina,haka kuwa akayi bayan na soma murmurewa da wata biyu aka mayar da mi gidan enginer abubakar,a lokacin da aka maidani baya nan ya tafi umara,kada kiso kiga farincikin da fatima tayi,sai tausayin kaina ya kamani,naso ma cuceta amma da yake Allah ba azzalumin bawansa bane sai ya kareta daga sharrina ba tare da ita din ma ta sani ba,yarona wallahi fes da shi kamar sauran 'ya'yanta bashi da wata damuwa,sati na daya da komawa kafin enginer ya dawo na fara wani zazzabi mai zafi,wasa wasa sai tari,ba'a jima ba quraje suka feso min,idanuna suka canza kala,fatima ita ta tambayi engineer ya bata dama ta rakani asibiti'' sai habiba ta tsaya ta fashe da kuka tana tuna irin bala'i da tashin hankalin da ranar tazo mata da shi,da qyar ta saisaita nutsuwarta sannan tace ''abin takaici da baqinciki zahariyya gwajin farko aka gane ina dauke da cuta mai karya garkuwan jiki cutar sida wato HIV''kusan tare suka fashe da kukan wannan karon dom tuni zahariyya tqyi amanna itama da cutar ajikinta,tunda babu shakka habiba ta samo,cutar ta ne daga jikin malam na hayi,to kuwa dole itama ta kamu da ita babu shakka,kuka sukayi sosai kana habiban tace ''hakanan fatima babu yadda zata yi badon taso ba sai don kare lafiyarsu ta sanar da engineer ,bai bari ya dawo ba ma ya aikomin da saki uku qwarara,ban boyewa fatima komai ba kan dalilin fadawata wanan haki,wallahi baiwar Allah kuka ta dinga yi cike da tausayina ,hakanan tamin alqawarin riqe min yarona riqo irin na amana,da kanta ta daukeni ta

Table of Contents

Chapters

138 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138