Chapter 120
Chapter 120
Sai kawai taga ya dangwalo ya tsotsa ''hmmmm,gaskiya da dadi''ya fada yana kaiwa bakinsa,kafin ta qwace har ya kurba,ta karbe kana ta zubar ''na gaya maka mazq baku sha,idan poising ne kuma fa?'' sai taga ya saki murmushi mai fidda sauti kana ya harde hannunsa a qirji ''sai abun ya zama abun alfahari a gareni,masoyiya ta bawa masoyinta guba sabida tsabar qauna,kuma zaqinta zanji dear na,ballantana ma na sani ke din ba zaki iya ba,saboda wasu ma da suka yi yunqurin bani naci kin kawar da hakan,ko kin manta har asibiti kika je aka tabbatar miki da irin nau'inta da kuma qarfinta?'' ido ta zaro,wai abdallah aljanine ko kuwa yana da su ne? murmushi ya kuma yi,ta bude bakinta da niyyar yin magana,sai yayi azamar qarasowa gabanta,yasanya tafin hannunshi ya rufe labbanta yana kallon qwayar idonta tare da cewa ''yi shiru da bakinki,ki adana duk wasu tqmbayoyi da kike da,su,wannan hiran na daya dagq cikin hirarrakin da na tsara mana,cikin gidan mu na qauna,a kan gadon soyayya,a kuma qirjin masoyi''ya qaraahe maganar yana kashe mata ido. kunya ta kamata sai ta zame bakinta tana murmushi ya sake matsowa kusa da ita yana yin qasa da murya saitin kunnenta ''ina fata kin tanadarmin salo salo na soyayya da,qauna wadda zaki shayar da ni,kinsan abdallah dan soyayya ne,yana son soyayya musamman ga matarsa''ya fada yana qoqarin janta jikinsa,gabanta ya shiga faduwa,ta faki idonsa ta zille tayi hanyar fita,baiyi yinqurin binta ba don ya tabbatqr da mutane a wajen amma sai ya matso uadda zata iya jinsa ya biyo bayanta ''ki gama zulle zullenki yarinya,awa,nawa,ne ya rage?''hakan da ya fada sai ua sata tsayawa ta juyo ta dubeshi idonta har ya cika da qwalla,dariya ya sa mata tayi hanzarin ficewa daga gun. Zuwa la'asar gaba daya hajja laila ta gama da kyawunta,tamkar buga qunshin akayi aka dayeshi,banu kuskure ko daya aciki,ja ne amma har saman hannu da saman qafa,abinka da fara ya fito kuwa yayi marun,kyau kam basai an fadeshi ba ya gama yi,tuni yan kawo mero sun tafi don yaci ace ma zuwa la'asar din sun kai gida,saukowarta kenan daga saman mami dauke da wata leda wadda wani arnen codenet ne a ciki da aka fidda wa dinki na garari,kudadr mamin ta saka masu yawa ta siyawa maryam din sabida wannan rana,sallama akayi aka shigo falon qasan,raliya ce janye da hannun fadil(yaronta)sai hindatu da lubabatu da kulu,baaba huwaila da hajiya atika. Cikin dakinta suka shiga ita da raaliya hindatu lubabatu da kulu,baaba hadiza da hajiya atika kuwa suna sama gun mami,mami ce tasa duka suka zo don yi mata rakiya,hira suka dinga yi wanda zuwansun ya rage mata fargaba sosai,lubabatu da kulu nata kallen kallen gidan mami don yau ne zuwansu na farko,sun tabbatar cewa Allah ya yiwa adda maryam din baiwa ba qarama ba. Raaliya ce ta shiryata tsaf cikin codenet din orange da yellow,kana ta dora mata alkyabba da mamin ta hadota cikin kayan,yellow ce mai ratsin fari,fadar irin kyawun da tayi ma bata baki ne,su kansu tsayawa sukayi kallonta,kai tsaye gin mami suka fara zuwa kana suka fice suka barta ita da ita,kallonta mamin take cike da farinciki,burinta kam ya gama cika a yau,hannu ta miqawa maryam din ba musu ta bata,gefeanta ta zaunar da ita kana tace ''maryam,da farko abinda zan fara cewa dake shine kiyi haquri,don babu wani abu da ya wuce haquri da mace zata riqe wanda zai,zame mata jagora kuma madogarar gidan aure,haquri maryam shine komai a rayuwa,kiyi haquri a duk yanayin da zaki tsinci kanki a gidan aurenki,duk wata mace da kika gani zaune gidan aurenta wallahi ba za'a rasa wata matsala da take fuskanta ba komai qanqantarta,ta wata ne tafi ta wata,qila wadda kikewa hangen ta haye ta huta da zata buda miki cikinta wallahi saikin tayata kokawa,komai dadinki da mimi wataran sai kun samu sabani,donko tsakanin harahe da haqori ma ana sabawa,na biyu riqe sirri ki riqe sirrinki ke da maigidanki maryam,koni idan bai zama dole ba bana buqatar jin sirrinku ke da abadallah,ku riqe amanar juna,ku riqe sirrin juna,ku zauna da juna cikin amana''nasiha ta dinga mata irinta tsakanin da da uwa,kuka sosai ta dinga yi har sai da mamin tace ''a'ah,ai kuma zaki batawa abdallahn kwalliyar me akayi kenan kuma uhm.....maza share hawayenki,duk da haka kowacce mace ta saba yau hashi kowa na zaune agidanta''. Da kanta ta kama hannun maryamun har harabar gidan ta sanyata cikin sabuwar range robber baqa wul wadda kyauta ce mamin ta yi mata,tukuici ne ta bata,kadan daga cikin irin abubuwan da take ji zata iya yiwa maryamu,yadda ta kama hannun mamin itama sai ta karya mata zuciya har sai da ta share qwalla,motocine kusan shida don akwai yayar mami da qanwarta,sai yayar marigayi alhj abdulkareem mai nasara da qanwarsa,tana nan tsaye mamin har motar ta daga suka fice daga gidan kana ta juya ta koma ciki,tun daga lokacin ta soma jin kewar maryamun,bangare daya ga abdallah dake shirin tafiya shima,babu shakka kewarsu zatayi ba kadan ba,don ma ga mero nan,amma kafin su saba su maye mata gurbin maryamunta ai ba nan kusa bane Sai da suka fara zuwa gidansu suka kaita gun mama da malam mamuda mahaifinta kafin su wuce da ita gidanta. Wani irin yadine ajikinsa orange colour mai bala'in kyau da taushi,dinkin babbar riga 'yar ciki da wando,fuskar nan tashi tayi wani irin kyau na musamman,hisham ke riqe da wata iriyar jaka da aka qawata ta da rubutu mai kyau suna tafe yana masa tsiya har suja qarasa gun mami,tana falon nata tana sallah ya tura qofar suka shiga,kujera suka samu suka zauna suka jirayeta har ta idar,sai data shafa addu'a kana ta tashi ta dawo kan daya daga cikin kujerun itama ta zauna,hisham ne ya fara magana ''mami gashi na kawo miki shi,ayi masa nasihar zaman aure''mirmushi mamin tayi tace''ka kyauta kuwa,shi yasa nake sonka hisham badai hankali ba'' harararsa abdallah yayi''jimin dan rqimin wayo,kana nufin zan iya tafiya banzo ga mami na ba?'' dariya ya masa don ya fuskamci yanayin fuskarshi har ya canza ya kuma san ba wani abu ne ya tabashi ba sai barin mamin da zaiyi. ''abdullahi''ta kira sunanshi da salon da bata taba ba,take ya dago idonsa ya kalleta,sai ya kasa civgaba da kallon nata ya duqar da kanshi,son ya hango magana zata masa bata wasa ba ''shi aure da kake gani girma ne da shi,daraja da shi qima gareshi,sunna ce guda ta wanda akayi duniua da lahita dominsa wato annabi muhammad S A W duk wanda ya wulaqantashi baya tare da annabi na tabbatar kuma bazaka so haka ba,a duk sanda ka dauki yarinya,aka rqbata da uwa da ubanta da inda ta taso tavgirma,aka rabata da danginta aka rabata da duk wani wanda ta saba da shi aka baka to ka tabbatar da xewa amana ce aka baka mai girma,kasan sarai hikuncin wanda ya tozaratar da amana ko yaci amana ko?,ka tuna ko yauahe cewa matarka ba siyanta kayi ba,ba baiwarka bace 'yace 'yantacci ya mai yanci,kada ka dinga mu'amala da ita irin mu'amalar bawa da ubangidansa,a'ah,ka mu'amalance ta wani lokaci kamar 'yarka,ka tsawatar mata ka bata shawaea ka tausasa mata kaja girmanka,ka mu'amalanceta wani lokaci kmar mahaifiyarka,ka tausasa mata,ka kyautata mata,ka girmamata,ka mu'amalanceta wani lokaci kamar qanwarak,ka qaunaceta ka kauda duk wani abu da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138