Skip to content

Chapter 78

Chapter 78

Abadan Book One Complete Hausa Novel 1,267 words 0 views Progress saved
Download Book

rafin ya debeta tayi baya luuuu zata koma cikin ruwan ''maryam!'' muryar abdallah da take a shaqe ta daki dodon kunnenta ba zato babu tsammani,cikin ikon Allah ta turje bata kai ga fadawar ba ta dawo gaba ta kwasa a guje ta dira a gabanshi cike da tsananin mamaki,ko ina na jikinta rawa yake,sai hawayen idonta da take ta yiwa waigi ya balle baki daya,ta rasa me ma zata yi,hawan mero tayi da bala'i ta inda take shiga bata nan take fita ba,dn me tana gani zata barshi ya fado akan me?,duk masifar da take taqi kallonshi yayin da ahi kuma ya zuba mata ido yana karanta al'amura da dama daga gurinta ''shshshhhhh''din ta taji yace yasa ta rage masifar da take, a hankali a hankali,daga qarshe taja bakinta tayi shiru ''ki taimakamin na koma kan kujerar tukunna madam'' ya gaya mata karo na farko taji,muryarsa ta fita sosai,wani abu taji yana ratsa ta tako ina. har yanzu jikinta bai bar rawa ba don haka qarfinta ya gaza kaiwa har sai data haqura mero ta taimaka mata suka maida shi,bata sake cewa komai ba ta soma turashi suka fara barin gurin tana goge qwallarta lokaci lokaci,ta kasa tantance yanayin da take ciki,gaske ne koko mafarki,yau abdallah ke magana da bakinshi?. Dab da zasu fara shiga cikin mutane taji yace ''bai kamata ki shiga cikin mutane kina kuka ba ko?,dakat kadan ki daidaita yanayinki'' bata qi shawararshi ba ta tsaida wheelchair din din ta ciro dankwalin atamfarta ta goge fuskarta kana ta maida dankwalinta,amma maimakon hawayen ya tsaya sai wasu sabbi,ma dake bulbulowa har mero ta iskosu ya limshe ido ya maida bayansa sosai ya kare da kujerar yana fadin ''ya salam,to me aka yi miki?,idan don warkewar baki na ne ai godiya zaki ma Alah ko,tunda dama shine mai kowa mai komai,idan kuma don fdowar da nayi ne ai gani sumul,ba ba abinda ya gutsireni mijinki baiji ciwo ba'' batasan ta harareshi ba sai data ji yace ''maida idon kada kija min asara,don ba qaramar asara bace idan na rasa wadann nan golden oily eyes din ba''. A nutse suka ci gaba da tafiya kamar yadda suka zo,saidai canjin yanayi da aka samu,a dazu mero keta faman zuba cike da farinciki abunta abdallah na kalle kalle babu bakin magan,wannan karon kuwa tasbihi hailala da salatin annabi ke fita a bakinshi zalla,yayin da maryam ke cikin wani irin yanayi,jin ta take kamar an rage mata wani nauyi daga cikin nauyin da aka azawa zuciyarta,mero kuwa amsa kuwwa muryar abdallah ke maya cikin kunnenta,dadin muryar ya kasa barin dodon kunnenta,tsabar kulawa da qauna da take iya hangowa daga dukkan kallo da ikin abdallah da kewa maryamu,da gaka suka qarasa gida ana qwala kiran sallar magariba. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽 [7:29pm, 9/25/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺 💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖🌺💖🌺 💖🌺💖 🌺💖 💖 *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 🌺💖🌺💖🌺💖 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 💖🌺 💖 © *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *_home of expert and perfect writers_* 4⃣7⃣ *_Manzan Allah S A W yace:shaidanu suna nisantar gidan da aka karanta suratul baqra a cikinsa har na tsawon kwana uku_* *_mala'iku sukanyi duba izuwa sararin duniya,yayin da suka kalleta suna hangota ne baqiqqirin basa ganin komai face hasken gidaje ko guraren da ake karanta alqur'ani a cikinsa_* A bakin murhu suka tadda inna wuro tana kwashe tuwo,sallamarasu ce ta janyo hankalinta bakin qofar shigowar ''kun dawo kenan mer.....'''sauran maganar ta maqale wa inna wuro ganin har da abdallah cikin masu sallamar,marar hannunta da take kwashe tuwon ta saki ta miqe tana fadin cikin dafe qirji ''Allah qaadiran ala mai yasha'u,bawan Allah?''ta fada tana kallonsa tare da qarasowa gabansu. murmushi yayi yana kallon innar ganin ta kasa magana ''babu mamaki cikin ikon Allah inna,nine da bakina nake magana,yau Allah ya amince min'' kiran sallar magariba ya katse su ''inna muyi sallah tukun''ya dubi maryam dake tsaye guri daya tana faman goge qwalla lokaci zuwa lokaci ''gimbiya a dauran alwala,inna ki mata magana tun dazun nace tabar kukan nan taqi''inna wuron dake daura da maryam din ta dafa kafadarta ''haba meramu,farincikin da zaki nunawa ubangiji shine ki masa godiya ba wai kika ba,share hawayenki ki daurawa mijinki alwala'' ''to inna''ta fada cikin rawar murya tuni har mero ta debo ruwa cikin buta tazo gaban abdallan ta ajjiye ta koma bakin rijiyar ta ja wani ta fara daura tata alwala,dukkansu nan bakin qofar dakin innar suka shimfida karauni biyu sukayi sallar magaribar,shiru ya ratsa tsakar gidan kowanne na tasbihi cikin zuciyarshi banda mero da moysa bakinta kawai takeyi duk motsin abdallah ta cikin hasken qwan solar na kan idonta,har maryam ta fuskanci haka,dauke kanta tayi don ji da tayi ranta na aon baci taci gaba da tasbihi da yatsunta. Ranar har sha daya na dare suna zaune suna hira,hiransu suke sosai shida inna wuro da yake jinta kamar maminshi. Yana jin kewar mamin nashi sosai har bazai iya fadar adadi ba,mero ma tsakiyarsu tana sanya musu baki yayin da maryam taja bakinta ta tsuke,lokaci lokaci abdallah yana satar kallonta,ji yake tamkar ya jawota jikinshi ya rungume ko ya shiga zuciyarta ya jiyo damuwarta,shirun nata bai masa dadi sam,don haka sha daya na cika yace da inna wuro yana jin bacci zai kwanta ''nikuwa kamar mu kwana nan hirar yau tayi min dadi abdullahi,gashi yau kaima da bakinka akeyi da kai''mero ta fada yana kallonshi baki a washe,murmjshi kawai yayi ya girgiza kai,bata bar gidan ba sai da taga sun shige dakin kana ta waiwayo ta yiwa inna wuro sallama ta fice cike da jin dadin jin daddadar muryar abdallah da yau ta morewa. sanye yake da jallabiya milk mai gajeran hannu yana zaune saman katifar tasu hannunahi dauke da qaramin al'qur'ani,daya hannun kuma riqe yake da wayarshi ya kunna torch din yana haskawa,ya sake satar kallonta sha biyu har da kwata amma bata da niyyar kwanciya,hakanan kuma ta kashe musu qwan solar dakin saboda ta lura da yadda yake ta nacin kallonta,tana zaune dirshan bisa dadduma sanye da hijabi da carbi a hannunta tana ja,ya saka zare kan shafin da yake na karatun qur'ani ya shafa addu'anshi,ya tabbata koya kirata kam ba zuwa zata yi ba indai ba cewa yayi yana buqatar wani abu ba. ''madam,a ataimakawa bawan Allah da ruwa mana''ya fada murya qasa qasa kamar mai rada har yasa tsigar jikinta tashi,ta ajjiye carbin kana ta miqe ta isa inda catoon na ruwan gora ke ajjiye ta ciro daya tare da cup ta hawo gadon,ta tsiyayo ta sake matsowa gabanshi ta miqo masa,jadawa yayi harda hannun nata ya riqe gam yana son saka qwayar idonshi cikin nata,ta soma qoqarin qwace hannun nata saidai ta kasa garin hakan har fiye da rabin ruwan ya zube a katifar. Ta dago da niyyar dubanshi idanunta cike da qwalla da ya rasa ta meye,take idanunsu suka hadu,da sauri ta janye nata idanun don bata iya dauke nauyin idanunshi cikin nata ''ka sakemin hannu kaga duk ka.....'' ''bazan sakeki ba,sai kin gayan meke damunki,tunda bakina ya budu baki,barni nayi magana da ke ba sai wasu ke tayani hira?'' ta sake kau da kanta kana tace ''to me kake so muce ko ince maka ne?'' ''bana tunanin baki san me zaki gayan ba maryam,nasha hango maganganu da dama boye cikin idanunki,kin hana bakinki ya

Table of Contents

Chapters

138 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138