Skip to content

Chapter 29

Chapter 29

Abadan Book One Complete Hausa Novel 1,283 words 0 views Progress saved
Download Book

zauna bayan yayi qasa da muryarshi ''nene,nifa na gaji da wannan shirin kisan ta bayan fage,ki barni kawai na tari abdallah na kasheshi da hannuna'' ''kai dalla gafara can''nene tayi hanzarin katseshi ''ashe baka da hankali?,waye ya gyamaka kashe mutum kamar abdalla abune da yaje da sauqi har haka?,ka manta matsayinshi?,ka manta wayeshi a nijeria,bama haka ba,ka mance qirar qarfin da abdallah ke da ita,wanda na tabbatar idan aka barka da shi naushi daya zai maka saidai mu dauki gawarka ba kai din ba''shiru adnan din yayi don yasan haka maganar maman tashi take zahariyya ta furzar da wani rin huci ''tsinanne matsiyaci,ni da zai amince ya auri waccar yarinyar zubaida ai da kinga komai yazo mana da sauqi,mu kasheahi hankali kwance,idan da rabo ma har sai ta haihu kinga tuwo namu miya ma tamu,to amma shegen girman kai da jin ajinsa bazai barshi yaso zubaida ba,to amma nene mai zai hana mu nemi hadin akn ita kukun tashi ko zata amince kamar yadda na baya suka amince,idan yaso itama musa a mata daurin baki idan ta amshi kwangilar ta yadda koda lamari ya baci zata gaza ambato sunansu kamar wadancan kukun'' ajiyar zuciya nenen ta saki ''hmmm,yaro yaro ne,duka tunaninku babu wanda ya kwanta min,wannan yarinyar tasha banban da wadancan kukun nasu na baya kallo daya na mata jiki na ya gaya min haka,abunda zai faru shine ni da kaina nake so ku bani lokaci zanyi tunanin mafita,na rantse da Allah wannan karon ko bata hanyar guba ba *SAI NA SALWANTAR DA ABDALLAH* _TOH FA_🤔 📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻 [9/17, 12:52 PM] 80k: *ABADAN* *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *_daga abu hurairah yardar Allah ta qara tabbata a gareshi yace:manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gareshi yace:ba zaku shiga aljanna ba har sai kunyi imani,ba zakuyi imani ba har sai kunso junanku,shin bana nuna muku abunda idan kuna aikatashi zaku so junanku ba?KU YADA SALLAMA A TSAKANINKU_* cikin kwana ukun mami ta hana gidan sakat da shirye shiryen tarbar abida,ragowar daki biyun dake maqotaka da nata aka bude,kusan komai irin na nata dakin ne sai dan bambancin abunda ba'a rasa ba,ganin yadda mamin ta dauki zuwan abida da muhimmanci ya sanya maryam itama sake shirya kitchen Ranar da zata iso din jirgin da yake sauka sha biyu na rana ne zai sauka da ita,tana jin mami na sanar da abdallah ya,haqura da fitar yau yaje a taro abidan da shi ''kai mami barta kawai,fita ta ta yau mai muhimmanci ce,driver yaje kawai ya daukota,ba dai tana gidan ba almost two to three months fa zatayi tare da mu'' qarfe sha daya maryam ta gama kintsa dining da kalolin abincin nijeria africa da kuma qasar da abidan ta baro wato turkiya,dakinta ta shige tayi wanka,don aikin bai barta tayi wankan ba,riga da zani ta zaba ta shirya cikinsu dukkansu normal dinki ne irin na riga da zani plain na asali,ba qaramin fidda sigarta yayi ba yanayin dakin akwai fidda shape din mu ba irin dinkin mu na yanzu ba mai tattara dake cika mace ya badda shape dinki,bata fito a dakin ba sai da ta jiyo surutu sama sama cikim parlour din mami qarfe daya saura kwata na rana mutum uku ne cikin parlour din harda mami ta hudu,tashin farko zuciyarta ta bada abida cikin su ukun,sanye take da doguwar riga baqa mai azabar kyau da tsada irin mai robar nan dake bin jikin mutum,fara ce qal don har tafi maryam fari duk da dai akwai bambanci,farinta mai dau ne babu sirkin ja aciki ko kadan,zaka iya kiranta gajeriya don bata cika tsawo ba,tana da kyau kam ba laifi don kallon farko zaka kirata kyakkyawa,bata da qiba da yawa saidai jikinta acike yake babu lobawar rama mami ce ta soma ganinta fitowarta ''yauwa maryam kin fito?'' ''eh mami na fito baqin sun qaraso,sannunku da zuwa'' ta fada tana dubansu,daya ce kadai ta amsa sabanin biyun ciki harda abidar wadda ta dago kai ta dubeta,kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace ''nidai kam ba baqiwa bace ina tsammanin kece baquwar'' murmusho maryam din ta danyi ''eh to,kusan haka dinne''ta bata amsa tana kallon fuskarta wanda take bisa screen din tsadaddar wayarta ''maryam kuje da ita ki nuna mata dakinta'' ''to mami''ta fadi tana yin gaba ''wa zai daukar miki trolly din?''abida ta ce tana hakimce a zaune tamkar ba ita za'a nunawa dakin ba bata ce komai ba ta dawo,ta dubi akwatinan da kallo,qwaya biyu ne masu azabar kyau wanda ko ba'a fadi maka ba kasan cewa ba na talaka bane,ta daga dogon sandan dake jikin akwatin wanda zai bata damar janshi akan tayoyinshi ta kwantar da ita ta jata zuwa ciki ta sake dawowa don daukar dayar,saura mami da abidar kawai yanzun cikin falon still abidan na hakimce,nuni ta mata da handbag dinta big mama tace ''shigarmin da wannan ma'' ''barshi,maryam bari baba uwani tazo zata shigar miki da su,aikin maryam a gidan nan girki ne kawai''mami tace da abida,sai ta bar abinda take yi din ta dubi maryam sannan ta dubi mami ''ok,ai duka daya ne mami,dan aiki dan aiki ne da mai girki da mai shara duka 'yan aiki ne'' ''to kam anan gidan akwai banbanci,kowa matsayinshi daban'' dan tabe baki tayi sannan ta saki murmushi kana ta canza topic din ''gaskiya mami abdallah bai kyauta min ba,yaushe rabona da nijeria ammayau kawai ya gaza kashe aikin gabansa yaje ya dauko ni'' ''kinsan dai halin abdallah sarai tun ba yau ba,aikinshi na da muhimmanci matuqa a gunshi,ba dan qaramin abu bane zai sanya shi qin fita aiki ranakun ayyuka ba'' maryam dake tsaye tana jiran tasowar abida duk ta qosa,ta dan gyara tsaiwarta ''mu qarasa na nuna miki dakin'' ''jeki kawai gidan ba baqona bane'' bata kuma tanka ta ba tayi komawarta daki,saida da ta dqidaici lokacin da ya kamata tayi serving nasu sannan ta fito,saita taddasu tuni sunyi nisa da fara cin abincin,son haka ta qarsa ficewa daga bangaren gaba daya,boys quaters ta zagaya inda anan gidan baba uwani yake da fara'a ta tarbeta ''maraba da maryamu,sai yau Allah yayi za'a zo mana''murmushi tayi har fararen jerarrun haqwaranta suka bayyana ta gaida baba uwanin da baquwar da ta taras tayi hirarsu suka sha sosai don bata baro bangaren ba sai da akayi sallar isha'i sukaci tuwon dawar da baban ta girka,don dama tana kewarsa matsalar su mutanen cikin gidan basa cinsa shi yasa ma bata girkashi ita daya ta taho iskar damuna na kadata,cikin parking space ta jiyo motsi,ta dan juya kadan hisham ne abokin abdallah,a tunaninta basu ganta ba don haka ta kau da kai tayi gaba ''haba 'yan mata irin wannan shan qamshi haka?,a qalla dai ai ko gaisawa kya tsaya muyi ko?,duk da cewa ma zuwan don ke nayi shi''inji hisham wanda ya sha gabanta,qirjnta ne ya shiga dukan uku uku,fatan ta kada Allah yasa ya furta mata kalmar so,don ita tsoro ma take bata,ta jita daga bakunan maza da yawa saidai babu abunda ta tsinana mata a qagauce ta ce masa ''ina wuni'' ''lafiya qalau maryam diya na ya gida ya aiki?'' kai ta dago ta kalleshi jin ya ambaceta da sunan da schoolmate da classmate dinta zuwa friends ke kiranta da shi ''lafiya qalau,ina son ganinki amma bari idan

Table of Contents

Chapters

138 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138