Skip to content

Chapter 49

Chapter 49

Abadan Book One Complete Hausa Novel 1,268 words 0 views Progress saved
Download Book

biyar,kudin sun bawa maryam din mamaki,murmushi abdur rahim din yayo yace ''ko nawa na bada kudin aurenki yayi kadan maryam,kinfi qarfin haka,me din mai tsada ce''murmishi kawai tayi tana sake ganin qima da darajar son da yake mata duk abin nan da ake jama'ar gidan basu da masaniya,kusan duk ranar da za'azo din basu gidan suna yawon asara yawon bidar asiri,asara goma da ashirin babu kudinsu ba imani *mrs muhammad ce*πŸ‘‘ πŸ“šπŸ“šπŸ“šβœπŸ½βœπŸ½βœπŸ½ [9/17, 12:54 PM] 80k: πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’– 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺 πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’– 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 πŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ πŸ’–πŸŒΊπŸ’– πŸŒΊπŸ’– πŸ’– *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’– πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’– πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ πŸ’–πŸŒΊ πŸ’– Β© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*πŸ’‘ *_home of expert and perfect writers_* β–Ά3⃣5⃣ πŸ‘‡πŸΎ *wannan page naku ne* πŸ‘‰πŸΎ *_haske writers asso_* πŸ‘‰πŸΎ *huguma conversation and novels rooms_* πŸ‘‡πŸΎ *da kuma* πŸ‘‰πŸΎ *Zauren biebie isah* *Allah ya bar qauna*πŸ‘πŸ½β€πŸ€˜πŸ½ *_Ankarbo daga imam bukhari r.a,manzan Allah s.a.w yace_* *_(qarami ya yiwa babba sallama,matafiyi ya yiwa wanda ya taras,jama'a 'yan kadan su za suyi yawa masu yawa)_* *_a wani hadisin da imamu muslim ya rawaito daga annabin rahama s a w yace(wanda a zuciyarshi akwai girman kai daidai da qwayar zarra bazai shiga aljanna ba)_* *Allah kayi mana tsari kada ka haramta mana aljannarka,ka hanamu dukkan wata baiwa ko ni'ima taka da zata yi sanadin zamowa masu girman kai* Fadar irin farincikin da mama da iyalinta ke ciki ma bata baki ne,sunyi amanna cewa wannan ce shekarar farincikinsu,addu'o'in da suka dade suna qwanqwasawa qofa yau kam an bude musu dukkan qofofin,duk wani tsohuwar ajiya ta mama data jibanci kadara ta daga ta saida,ta yiwa bikin shiri matuqa da gaske,ga dangi masu zuciyar yi mata da Allah ya hadata da su takanas suka ziyarci gaya ta saida manyan gonakinta na gado guda biyu,ba qaramin kudi ta samu da su ba kasancewar yadda a yanzu kowa ya koma noma gonakin daraja suke,tuni ta fidda kudin kayan gado kayan kitchen da sauran tarkace na hindatu,maryam kam dama da yan kudadenta da take sa ka ran zasu isheta sayan kayan gado,ga mamakinsu saiga kudade baban su ya damqa masu a boye yace sukaje su zabi kayan gadon da suke so,shi din ma gonakinsa biyu ya siyar dake gayan,dama bashi yake amfana da su ba yan uwansa ne,cikin rufin aairi, Allah sai gasu sun tashi da kayan gado na kere sa'a masu kyau tsada da aminci bata sake shiga farinciki matsananci ba sai da mami ta damqa mata passport dauke da visa ta qasashe biyu saudiyya da china ''maryam,inason inje siyayyar lefen abdallah ne,sannan ke kanki ina son in miki siyayya irin wadda uwa take wa diyarta,naso 'ya mace amma Allah bai bani ba,to a yanzun kuma sai Allah ya bani ke,naso ace lokacin bikinki da abdallah bai hade ba da ina mai tabbatar miki anan gidan zaki zauna har akammala taro a miqa ki gidanki,saidai duk da haka bikin magaji ai bazai hana na magajiya ba,zamu fara zuwa china muyi siyayya sanan mu dawo saudiyya muyi umara,kuyi addu'a kowannanku ya roqawa kanshi alkhairi kan sabuwar rayuwar da zaya shiga,ni da ke ne da abdallah'' rasa bakin da zata gode mata tayi saidai ta tsinci kanta cikin zubda qwallar farinciki,tabbas uwa ce,mami uwa ce wadda tasan ciwo da darajar 'ya'ya,babu shakka ko ita ta tsugunna ta haifeta iyakacina binda zata mata kenan,haduwars ta tabbatar daga Allah yake,bata manta yadda taqi taji batason aikin gidan mamin ashe alkhairi ne Allah yake nufinta da shi,gaskiya ne maganar Allah haka take da yake cewa cikin alqur'a ninshi mai girma (zaku iya qin abu kuma alkhairi ne agareku,sannan zaku iya son abu kuma sharri ne a gareku,Allah shine ya sani ku baku sani ba) mama kam rasa mai zata fada tayi,babu shakka duk yadda kaga Allah yayi da rayuwarka baiyi don zalunci a gareka ba,yayi ne saboda shi ne mafi sani ga abinda ya dace ga bawansa raliya har da hawayen farinciki ''damuwarki tazo qarshe diyana,Allah ya yanke miki,maqiya kuma sai su kashe kansu don baqinciki''abinda ta dinga fadi kenan fuskarta qunshe da murmushi hindatu kam buri ya cika,don tace ko iya haka Allah ya barsu sun gode masa,Allah ya nuna isa da buwayarshi,itama tata visa din umarar na nan jabir ya tanadar mata bayan sun angwance da wata daya πŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒ qarfe biyu na azahar jirgin ethopian airline zai debe su zuwa ethopia inda anan zasu fara yada zango kafin su isa qasar sin,cikin masu rakiyar tasu harda jabir da hindatunshi,abdulrahim sai zubaida,raliya da yaronta fadil, ranan ne abdulrahim suka fara haduwa da jabir,tuni ya dade da sanin waye jabir din da kuma matsayin da yake kai a yanzu a gun maryam din,don haka gaisuwar mutunci sukayi tamkar sun jima da sanin juna,kusan dukkansu sama sama suka gaisa da abdallah yaja gefe yana faman cin magani tamkar wanda aka yiwa dolen tafiyar,ita kuwa zubaidan bata damu da ta qyaleshi ba ganin yadda yake faman fuskewa ba tana liqe da shi tana zuba rawar kai yayin da shi kuma yayi mata dif ko kanzil yaqi tanka mata da ita cikin hirarta cike da bege da qaunar juna suka yi sallama lokacin da aka soma neman matafiyan maryam ce qarshe saboda tsayawan da sukayi da abdulrahim ''abun mamaki banga irin sallmar nan da masoua kanyi ba yayin rabuwa da juna abdulrahim meke faruwa?'' murmushi ya saki yace ''me kika gani maryam?,kina tuhumata ne kan rashin damuwa da tafiyar da zakigi ki barni?'' ''dole in tuhumeka mana abdulrahim,ba sau daya ba basau biyu nasha kamaka da laifin qin sakin jikinka idan muna tare matuqar abdallah na agun,wai shin tsoronshi kake ne ko meye?,aure fa zamuyi nan da sati uku kowa yasan da zamanka,ko wata barazana yake maka aboue wadda mu bamu san da ita ba'' sai taga ya tuntsire da dariyar har yana dan duqawa ''babu tsoro balle barazana tsakanina da shi,ke kika dai fuskanci hakan,hasalima abinda kike zaton ba haka bane,Allah shine mafi sani ga abinda yake cikin zukatan bayinshi,Allah ya kaimun ke lpy ya dawo min da me lpy,ki kula min da kanki matuqa,ki yiwa kanki addu'a mai yawa maryam,kada ki kashe wayarki da wuri zan kiraki kafin ku tashi''sallamar da sukayi kenan koda ta shiga gurin tayi tsammanin ya dade da wucewa tunda sun rigata shigowa da wajen minti goma sha biyar,sai gashi tana gaba gun screening shi kuma yana tsaye a bayanta,gaba daya sai ta takura,tana ji a jikinta tamkar yana qare mata kallo ne kawai,gashi doguwar riga ta saka sai rolling da tayi wanda iyakacinsa kafada,hill shoes ta saka wanda sanadiyyar hakan yasa ta kusa kama abdallan a tsawon ko cikin jirgi ma number din sit din nasu daga shi sai ita,mami na a sit din bayansu,tamkar ta zura a guje ta bar sit din haka ta dinga ji,tunda take basu taba zaman kusanci na tsawon lokacin da zasuyi yanzu ba,ta njtsu tsaf tamkar ace ket!ta zura aguje wayarta tayi tsuwwa ta duba saiga kiran abdur rahim,tamkar ance mata ta kalli gefanshi sai ta tsinci idanunshi a kanta,wani irin kallo yake mata da ta kasa fassara ma'anarsa,shi ba harara ba ba kuma normal kallo ba,ya kafeta da mayun idanunshi masu cike da kwarjini,sai ta tainci kanta da kasa dagawa har wayar ta tsinke,gani tayi ya ciro tashi wayar ya fara danne danne hakan ne yasa tayi saurin jan tata wayar ta soma dubutawa abdulrahim

Table of Contents

Chapters

138 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138