Skip to content

Chapter 107

Chapter 107

Abadan Book One Complete Hausa Novel 1,296 words 0 views Progress saved
Download Book

shigarta kamar wadda aka cirewa wani muhimmin abu daga sassannin jikinta Dakin ta ta wuce kai tsaye ta fada gado tayi ruf da ciki,kasala take ji da canjin yaynayi cikin jikinta,sai taji gidan ya mata fayau kamar ita daya ce a ciki,ganin matuqar taci gaba da zaman a haka kasalar zata rufeta da gasken ya sanyata miqewa ta fito kai tsaye tayi sashen baaba uwani A tsakar gidacta tatar da ita kan tabarma tana gyara zogale,kan tabqrmar ta isa itama tasa hannu tana tayata suna hirarsu,qarar wayarta ya katse musu hiran kiran raliya ne,tana murmushi ta daga sanan ta mata sallama ''maraaba da dawowan diyana''cikin sauti mai dauke da farinciki ta maida mata amsa ''uwar gida kuma amaraya agidan muhammad nasir'' dariya itam tayi cike da nishadi ''a wannan kirarin ai sai ku,ku da ludayinku ke kan dawo'' sai da suka gama zolayar juna kamar yadda suka saba sannan suka fara gaisawa Hira sukayi mai tsawo wadda har baaba uwani ta kammala gyaran zogalen ta kwadanta basu gama ba Har bayan magariba tana gun baban suna hirarsu,sai sallamar mami kawai sukaji ''zuwa nayi na duba dama,nayi zaton bai dawomin da ke ba'' kunya ta kamq maryam din ta sunkuyar da kai tana murmushi,tana idar da sallar isha'i ta yiwa baba sallama ta koma bangarensu Ta kammala shirin naccinta tsaf ta haye gadonta,saidai ko guda baccin da take da muradin yi bata ji alamunsa,wata iriyar kewa da madaici na daban take ji na damunta,juyi take tun daga farkon gadon zuwa qarshensa,tayi hakan yafi sau a qirga,tana son qaryata kanta kewar abdallah take saidai ta gaza,sai ta tsinci kanta da muradin jin muruarsa saidai ko kadan ba zata iya kiransa ba,hasalima bata tunanin akwai lambar wayarsa cikin wayarta,ta miqe a hankali ta jawo side drower ta ciro envalope din da ya bata dazun,dawowa tayi kan gadon ta kwanta ruf da ciki,a hankali ta farketa,kudi ne sababbi fil a miqe yan dubu dubu masu yawa suka fado,yar qaramar takarda ce maqale jikin bandir na kudin,ta cirota ta budeta,karo na farko da idaninta suka ci karo da kyakkyawan rubutu wanda bata yaba ganin kamarsa ba ''kiyi amfani da su idan buqata ta taso miki,love you so much my sugar'' dunqule takardan tayi ta dorata saman kudin Ta sake bude cikin envalope din take taci karo da wata takardar fara qal mai adon furanni wadda ba shakka itake tashin qamshin nan,ajjiye envalope din tayi kana tasa hannu biyu ta ware nadin da aka yiwa takardar,sallama ce a farkon takardar cikin kyakkyawan rubutu da harshen larabci _qoqarin mantawa da wanda kake so is like trying to remember some one you never meet,i know we feel d same baby saidai bansan me ke yawo cikin zuciya da ruhinki ba,dont let your ego stop u from doing whats right,duk abinda nayi nayi ne saboda ke,duk abinda kike gani na miki laifi a akansa saboda ke na aikata,sonki ne sanadi baby,i cant express my feelings a kanki baby,ban taba sanin haka so yake na sai a kanki,zan iya cewa kai tsaye ke kika koya min so,nasan kina tunanin na auroki ne kan tilas,ba haka bane na aureki saboda sonki da qaunarki da nake,nayi tsammani zaki qini zaki qi sona hakan ne yasa ban nemiki kai tsaye ba,but sorry for hurting u baby_ _kalmomi na sun bata ranki hakan ya sa kika riqeni,na sani na kuma san na fada,but banda ke baby baki ciki amma duk da haka am sorry again for my words and action last time,ina sonki baby ina sonki,am not with you to play games,ina fatan komai zai gyaru kafin dawowata,bazan iya jurar rasaki ba bazan iya ba,zanso ace ko yaushe kina tare da ni,baby ina da qarfin buqata tun ba yau na na sani,idan kika qi ni bazan iya sakinki ba duk tsanani matuqar ina raye amma ina fatan bani dama nayi aure,koda babu komai tsakaninmu ganinki da zamanki a matsayin matata kawai ya wadatar da ni,ke ta dabance baby ki yarda,inajin komai nawa daban duk lokacin da muke tare,am feeling safer when iam wrapped up in your arms then ever before,duk lokacin da nake kusa dake baby am overwhelmed with happiness,kin soni kin ceceni kin kubutar da ni kin kuma tserar dani,shin wannan ba so ne ba baby?bai isa a kira waannan so ba?,so mai ma kuwa mai tsada,so mai cike da sadaukarwa da fansa?,kin min abinda 'yammata da yawa suka kasa min,na haqiqance u are what i have been waiting for my whole life,so na haqiqa so na gaskiya,kina sona ba tare da kinsan ma kina sona din ba baby_ _alhamdulillah finally a found someone who loves me just for me,ba don wani abu da nake da shi ba,but ban manta ba i promise sai na ninka sona cikin zuciyarki fiye da da,nasan nayi nasara duk yadda kika kai ga boye hakan alredy na ganahi cikin idanuwanki koda zaki qaryata ni,abu na gaba shine ki fadamin shima na tabbatar miki cewa sai nayi nasara nayi alqawari,TO THE MOST BEAUTIFUL GIRL IN D WORLD,AM SORRY BABY,_ Lumshe idanunta tayi tana jin wani abu da bata taba jin irinsa ba na ratsata,gaba daya abdallah ya gama kasheta,muguwar kasala ce ta lullubeta,sai ta ninke takardar ta lalubo jakarta da take ajjiye muhimman abubuwanta zata jefa ciki idanunta suka sauka kan takardar,takarda ce data dauketa washegarin daren da abdallah ya fara cuta,sam ta mance da ita,da sauri ta daukota ta bude ninkin da tayi mata,rubutune mai kyau kamar wancan saidai bai kai yawan wancan ba _idan da kina da masaniyar tun yaushe na fara sanki ba zaki nemi abdallah ya rabu da ke ba,na soki a lokacin da bakisan akwai mai sonki ba cikin duniya,maryam tun kina 'yar secondry school na fara sonki,cikin kulawaata da sa idona kika kammala universty dinki,can you remember sau nawa kike zuwa registration ace miki an dau nauyinki saboda hazaqarki cikin dalibai?,zaki iya tuna samari nawa kika yi suka tafi basu sake dawowa ba?,har kina tsammani ko matsala ce daga gareki,kin kusa auren jabir a lokacin bani qasar nan ban sani ba na tafi jinya na gubar da naci london,cikin qurarren lokaci na samu labarin hakan ina can,sauran qiris na rasa raina san da na samu labarin zakiyi aure amma da yake Allah na sona ya tsinke lamarin,dalili kenan da na nemi sabon mai dafa min a binci saboda na sani bangarenki ne........._ Iyakar rubutun dake ciki kenan saidai tasirin da ta yuwa zuciya da gangar jikinta mai yawa ne har ta kasa zama ta miqe tsaye,da gaske abdallah yake?shekaru nawa nufinsa yana tare da sonta,abdallah ya dade tare da ita ba tare data sani ba A hankaki wasu abubuwan da suka dinga faruwa da ita a baya suka dinga fado mata,sautari akan tsaya da mota ta alfarma da niyyar rage mata hanya,a lokacin haushi da takaici na kamata ne don tana tsammanin 'yan kama wuri zauna ne kawai wadandq suke barewa duniya gyada taci keson hilatarta,saidai bata taba katarin ganin fuskar abdallah cikinsu ba,duk cikin nashi salon game din ne kamar yadda ya mata kan ABDUR RAHIM?. sai kawai taji murmushi ya subuce mata abdallah? abdallah?,wanne irin mutum ne kai abdallah,basira da wayinka sun isa,you have play good game with me''ta samu kanta tana fada cikin zuciyarta,sai ta koma bakin gado ta

Table of Contents

Chapters

138 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138