Chapter 9
Chapter 9
Allah ya taemaka. Washe gari kuwa kamar yadda Abban ya fad'awa Abbu se gashi da wurwuri a gidan, daga nan babu 6ata lokaci suka tafi kasuwar zuwa shagon da aka bawa Abba hayar sa, dama ba tun yanzu yake da burin bud'e shago ba amma be bawa abin muhimmaci ba seda wannan abin ya faru dan haka kayan da yake d'an siya yana ajjewa su yayi amfani dasu ya zuba a cikin shagon, sannan yayi amfani da ragowar kud'in da yake dashi ya k'aro wasu kayan ya zuba zuwa lokacin da Allah ze hore ya zuba wasu masu yawa, duk da shagon yafi k'arfin kayan daya zuba a ciki amma haka yake jin sa cikin farin ciki mara misaltuwa, haka suka isa shagon Abba ya bud'e bayan sunyi addu'o'i sosae, tare suka zauna cikin shagon shi da Abbu, Abbu ke kula da harkokin kayan siyarwar yayin da Abba ke kula da harkar kud'i, cikin ikon Allah a ranar kawae sunyi ciniki sosae musamman daya kasance ranar farko ce se Abba yayi discount akan duk wani abu da mutum ze siya, hakan yasa mutane da dama suka dinga zuwa suna siyar kayayyakin, basu suka tashi ba se dab da maghrib sannan suka tashi, Abba ya d'auki kud'i masu d'an dama a cikin cinikin da suka yi ya bawa Abbu, Abbu yayi ta godiya ya tafi gida cikin farin ciki, yau beyi wahala ya nemo kud'in da zasu samu suci abinci ba yana zaune kawae cikin shago babu rana kuma gashi an bashi abinda ko buga bugar yayi baze samu ba, hakan yasa farin cikin nasa ya sake ri6anyuwa. Tun daga wannan ranar ya kasance kullum Abba da Abbu zasu fita kasuwa da safe basa tashi se dab da maghrib, sosae Abba ya sanya idanu akan Abbu da al'amarin sa, cikin k'ank'anin lokaci Abba ya fahimci Abbu mutum ne me rik'on amana da kirki, babu 6ata lokaci ya shiga gwada shi lokacin da harkar ta bud'e dan yana so ne ya d'an dinga sakar masa abubuwa ba tare da wani tunani ba, sau da dama yasha gwada shi seya same shi da rik'on amana lamarin sa babu ha'inci a ciki, cikin ikon Allah da yaddar Allah sana'ar tasa ta samu kar6uwa a wajen mutane, sosae ake zuwa a siyi kayan da yake siyarwa saboda haka a hankali ya d'an fara sakarwa da Abba wasu abubuwa da dama saboda shima ya d'an samu sassauci. A 6angare guda kuwa ya sanya Raj a makarantar su Ayrah, an saka shi a Junior class saboda yanayin shekarun sa, ba laefi sun d'an fara sabo shi da Yah Sadeeq amma ba wani sosae ba, yayin da a tsakanin sa da Ayrah kuwa kullum wata sabuwar shak'uwa ke k'ara ninkuwa a tare dasu kamar wad'anda suka yi shekara da shekaru a tare, kamar kuma wad'anda suka fito ciki d'aya haka suke al'amuran su, kowanne najin d'an uwan sa a cikin ransa, a tsakanin su babu wanda ke son ganin d'aya yana cikin 6acin rae, sau da dama Umma kanyi mamaki na shak'uwar ta su amma idan ta tuna komae daga Allah ne seta dena mamakin, daga k'arshe ma gaba d'aya Raj ya dawo gidan su Ayrah da zama, idan Abba ya d'auko su daga makaranta seya wuce dasu dukkan su har Raj d'in gida, su tafi Islamiyya sannan idan suka dawo suci abinci kana Raj ya tafi gida, wata ran da k'yar yake tafiya d'in idan Ayrah ta saka rigimar seta bishi, da k'yar take hak'ura idan Umman dashi kansa Raj d'in suka rarrashe ta kana take hak'ura amma fa ta dinga nunk'ufurci kenan kamar wata babba, tayi ta bin kujera tana kwanciya kamar zata yi kuka, idan kuwa da rana ne ko a makaranta in dae basa cikin aji toh zaka same su ne kullum tare da juna, wata iriyar shak'uwa suka yi mara misaltuwa ko iyayen Raj d'in ma abin har mamaki yake basu, sunan Raj kuwa seda Ayrah ta lak'abawa kowa, daga zarar kace masa Suraj za tace ba Suraj ba Raj, kuma in zaka kwana kana fad'ar Suraj itama zata kwana tana gyara maka, dan haka yanzu en gidan su ma kwata kwata Raj d'in suke ce masa, Iyayen sa ne dae suke k'ok'arin ce masa Raj d'in ko dan Ayrahn musamman idan a gaban tane, shi kansa yanzun yafi jin dad'in Raj d'in kuma babban dalili daya kasance Ayrah ce ta saka masa sunan. A cikin shekarar da taemakon Allah komae ya cigaba da bud'ewa Abba, seya kasance ma yanzun ya zuba atamfofi ne kala kala kuma masu yawa, sosae Abbu ke taemaka masa ta hanyoyi da dama, dan yanzun ya gama sakar masa komae, ko menene in dae shi da kansa ze iya yi toh fa ze iya d'ora Abbu akae saboda yadda yayi na'am dashi, haka suka cigaba da tafiyar da shagon su 2, sosae abubuwa da dama na Abban suka chanja ciki kuwa hadda cimar gidan sa da suturun da shi kansa da iyalan sa kan saka da kuma sauran abubuwa makaman tan wannan, shi kansa Abbu ba'a barshi a baya ba dan kuwa yanzun rayuwa suke cikin kwanciyar hankali babu yunwa babu komae, dan a lokacin ma seda ya nemi Abba ya sakar masa harkar makarantar Raj amma Abba yace a'ah tunda ya fara shi ze k'arasa In Sha Allah, beyi musu ba se k'ara godiya da yayi, godiyar da kusan kullum se yayi ta baya gajiya da ita. _*MAFARI*_ ... Da sallama Abba ya shigo gidan kamar koda yaushe hannun sa d'auke da ledar daya saba shigo da ita kusan kullum wanda hakan ma ya riga ya zame masa jiki, in dae ze dawo gidan toh In Sha Allah ze siyo wani abun ya tahowa da iyalin nasa shi, da gudu ta sauko daga kan kujerar ta k'arasa ta rungume Abban tana fad'in "Abba Sannu da zuwa" "Yawwah an baby.." "Abba meka siyo min?" ta fad'a tana murmurshi, shima murmurshin yayi sannan yace "Kar6i maza ki kaewa Umman ku, ina take?" seda ta sanya hannu ta kar6a sannan tace "Tana kitchen" daga haka tayi hanyar kitchen d'in tana kiran sunan Umma, Raj dake zaune kan kujera ya sakko a hankali ya furta "Abba sannu da zuwa" "Yawwah sannun kadae" Abban ya fad'a yana wucewa d'akin sa... Seda ya samu yaci abinci a cikin parlourn sannan Umma ta gabatar masa da ruwa ya sha kana yace "Dama akwae maganar dana ke so muyi" gyara zama Umma tayi kana ta kalli Ayrah dake shirin fita daga d'akin saboda Raj daya shigo yanzun kuma ya fita "Ina kuma zaki je?" Umman ta fad'a, turo d'an k'aramin bakin ta tayi sannan tace "Umma Raj zan bi" "Ina ze je?" "Wajen Yah Sadeeq.." ta fad'a tana kallan Umman, Abba ne yanzu kuma yace "Toh shikenan, amma banda shiga ball ta maza ce" jinjina kae tayi tana murmurshi ta fice daga d'akin, Umma ta juyo da kanta wajen Abba tace "Abban su ina jin ka" seda Abban ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Wato Alhaji Mato ne yazo min da wata shawara..toh yanzu dae so nake nayi shawarar dake inji me kikace, wato ba wani abu bane ya bani shawara ne wadda In Sha Allah akwae cigaba a cikin ta, cemin yayi meze hana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70