Chapter 41
Chapter 41
cikin motar ya bud'e k'ofa ya fita yayin da Muttala ya koma mazaunin driver, seda ya kalli cikin layin ya tabbatar babu kowa sannan ya k'arasa inda Ayrah take, ita sam hankalin ta be kae kan sa ba yana kan motar Rk da take kalla dan tabbatar da tasan ce, beyi wata wata ba ya matsa bayan ta ya shak'a mata wani abu dake jikin handkerchief d'in hannun sa, lumshe idanun ta tayi tana jin wani irin yanayi cikin kan ta kafin a hankali ta kae hannun ta tana shirin dafe kan ta, take wani jiri ya d'ebe ta cikin sakannin da basu wuce 10 ba ta fice a hayyacin ta se kawae tayi baya zata fad'i mutumin ya saka hannun sa ya tare ta ya jata zuwa cikin motar har lokacin yana d'an juyawa bayan sa dan tabbatar da babu wanda ya gan shi, dae_dae lokacin da yake k'ok'arin k'arasa shigewa da ita cikin motar Rk ya bud'e idanun sa daga lumshe sun da yayi tun d'azun, kamar ance ya kalli wajen se kawae ya hange ta jikin wani mutum yana cusa ta cikin mota, seya sake rufe idon ya bud'e dan tabbatar da abinda ya gani d'in gaskiya ne ko kuwa idanun sa ke masa gizo, cikin wani irin zafin nama ya tura k'ofar side d'in da yake yana shirin fita zuciyar sa na wani irin zafi tana cigaba da harbawa kamar zata faso k'irjin sa, Muttala yaja motar da k'arfin gaske tun kafin ma mutumin ya gama saka Ayrahn cikin motar, seya koma da sauri zuciyar sa na bugawa yama kasa tunanin komae kawae ya figi motar da wani irin gudun da tunda yake ze iya cewa be ta6a yin irin sa ba, sosae su Muttala suke gudu kamar zasu tashi sama yayin da shima ya cigaba da bin su, kawae burin sa ya san inda zasu je, ina zasu kae ta? Me zasu mata? Meyasa suka d'auke ta? Kwata kwata tunanin sa be kae ya kira police ya sanar dasu ba kawae shi dae burin sa ya cim masu. Sosae suka cigaba da tafiya kuma inda Allah ya taemake su kwata kwata basu samu traffic jam ba, mamaki ya sake kama shi ganin se tafiya suke yi kamar baza su dena ba, har lokacin kuma bugun da zuciyar sa take be ragu ba, haka ya cigaba da bin su zuwa lokacin da yaga sun fara barin gari suna shiga cikin wani waje daya fi masa kama da k'auye, mamaki ya sake kama shi amma da yake baya so su gane akwae wanda ke bin su seya dakata har zuwa sanda suka masa nisa sannan ya cigaba da bin su a nutse yana yi yana lumshe idanun sa saboda yadda yake jin jikin sa ya masa wani iri ga yadda bugun zuciyar sa ke ta k'aruwa. Dae-dae wani madaedaecin gida ya hango su sun yi parking d'in motar su, ze iya cewa tunda suka shigo k'auyen bega gida me kyan sa ba dan kuwa duk gidajen k'asa ne yayin da wannan d'in ya kasance ginin bulo ne, Muttala ya fita ya bud'e k'ofar gidan da mukullin hannun sa sannan ya dawo ya tashi motar zuwa cikin gidan kana ya saka mukulli jikin gate d'in sannan ya sauke ajiyar zuciya "Da alama mun tsira fa" ya fad'a yana fesar da iska daga bakin sa, mutumin da shima ya fito daga cikin motar yace "Wallahi kuwa, kayi maza ka kira mana Alhaji ka sanar dashi mun gama aekin mu" murmushi Muttala yayi kana ya fito da wayar sa ya lalubo number Alhaji Mato, tun kafin Alhaji Mato yace komae Muttala yace "Yalla6ae albishirin ka?" daga inda Alhaji Mato yake ya saki wani murmushin jin dad'i yana shafa tumbin sa, ko Muttalan be fad'a ba yasan sun yi nasara, amma saboda ya sake tabbatar wa ya sanya shi fad'in "Goro.." "Mun gama aekin mu, yanzu haka gamu a cikin gidan yalla6ae" "Weldone, ku jira ni yanzu zan taho.." Alhaji Mato ya fad'a yana jin wani irin dad'i na ratsa shi, yasan tabbas yau d'in Ayrah zata kwana ne a matsayin matar sa, baya shakkar wannan tunda dae an riga da an samo masa ita. .... A 6angaren Ummee kuwa ganin har bayan wajen awa d'aya Ayrahn bata fito ba seta mik'e ta sake komawa d'akin nata, gwara ta rarrashe tan kawae ko zata samu ta saki ran ta ta cigaba da harkokin ta, a hankali ta yaye labulen d'akin idanun ta kan gadon data san akae zata sami Ayrahn, se dae ga mamakin ta babu kowa kan gadon babu ma alamar akwae mutum cikin d'akin, sauke labulen tayi a ran ta tana ayyana babu mamaki tana cikin toilet, se kuma kwanyar ta ta tuna mata ae yanzun ta fito daga ban d'akin, dan saboda ta tabbatar da gasken bata cikin band'akin ya sanya ta k'arasa toilet d'in, k'ofar sa a bud'e take amma duk da haka seda ta shiga ta duba bata ga kowa ba, k'irjin ta ya buga tana tuna yadda suka rabu da Ayrahn jiya, kada dae halin en yau zata nuna musu? Kada dae ace d'iyar ta ta ta chanja hali bata sani ba? Kada dae ace d'iyar ta ta ta za6i d'a namiji akan su? Tsara hakan cikin ran ta yasa ta sake jin jikin ta yayi mugun sanyi, a hankali taja k'afafun ta zuwa d'akin Abba, Abba ya kalle ta da mamaki ganin yanayin ta yace a hankali "Lafiya kuwa Ruk'ayyah?" "Bana tunanin haka" Umma ta fad'a tana jin wasu zafafan k'walla na zubo mata "Subhanallahi, meya faru?" Umma bata tabbatar ba dan haka a ran ta taji gwara ta bari ta sake tabbatarwa ko fita tayi ta siyo wani abun dan haka seta furta "Babu komae" "Ya zaki ce babu komae kuma? Bayan kin fita lafiya, yanzu kuma kin dawo kina kuka?" "Babu komae" ta sake fad'a tana cigaba da share k'wallar dake ta zubar mata. Wasa_wasa se gashi Ayrah har wajen azahar babu ita babu labarin ta zuwa lokacin tuni Umma ta gama na'am da abinda take zargi "Ina yarinyar nan ne? Ko har yanzu baccin take?" Abba ya fad'a yana kallan Umma, kawae seta fashe da kuka tana jin wani iri a cikin zuciyar ta, a yau d'aya tana jin kamar tayi danasanin haehuwar Ayrah amma ta kasa, amma duk da haka yarinyar ta shammace ta, ta shammace ta aenun, bata ta6a tunanin hakan daga gare ta ba "Abban su yarinyar nan ina tunanin ta gudu da wancan yaron, ashe shiyasa ta kasa ce min komae tunda taji abinda ya faru, ashe tace kya yi kya gama bazan rabu da shi ba, Abban su yarinyar nan ta bani mamaki" dafe saetin zuciyar sa Abba yayi yadda yaji ya wani irin buga, seya shiga tari, saboda tsananin tashin hankali babu wanda ya iya kula shi, seda Yah Sadeeq ya dawo daga shocking d'in da maganar Umman ta shigar dashi sannan ya d'auki ruwan gaban sa ya mik'awa Abba, kar6a Abba yayi ya sha kana ya koma sauke ajiyar zuciya, kafin ya d'ago ya kalli Umma da har lokacin take share hawaye a fuskar ta "Waye ya fad'a miki hakan?" "Tun d'azu na neme ta na rasa cikin gidan nan Abban su, ko ka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70