Chapter 65
Chapter 65
seta shiga sauke ajiyar zuciya a nutse, se a lokacin ya sauke ajiyar zuciya kamin a hankali ya furta "Rigimammiyar mata ta.." k'arar da wayar sa tayi ne ya sanya shi kallan inda take, be san me kiran nasa ba, kamar ze share se kuma ya kalli Ayrahn dake baccin ta hankali kwance kamar bata da damuwa, ya lumshe idanun sa wata matsananciyar k'aunar ta na sake ratsa shi, cikin dabara yanda ba zata farka ba ya shiga zame ta daga jikin sa har zuwa sanda ya k'arasa zame ta gaba d'aya, ya kwantar da ita kan gadon sannan ya lullu6a mata blanket kana ya sake kallan ta, ji yake kamar ya sake kissing nata se dae baya so ya 6allowa kan sa ruwa dan haka kawae ya k'arasa inda wayar tasa take dae_dae lokacin da ta sake yin ringing "Muneerah!" shine dae sunan daya sake bayyana akan screen d'in, tsaki yaja akan la66an sa dan har ga Allah ya manta da wata Muneerah musamman a yanzu da yake tare da Ayrah "Itama matar ka ce, at least yaci ace ka san a wane hali take" shine abinda zuciyar sa ta raya masa, ya sake jan wani gajeran tsakin yana maeda duban sa kan er rigimar tasa, yanzu taya ze fita ya bar ta cikin d'akin nan ita kad'ae? Idan kuma ya fita kafin ta tashi in ta tashi taga baya nan fa meze faru? Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 039 ___A hankali ya maeda duban sa kan gadon yana kallan ta duk da fuskar ta ce kad'ae ake iya gani gaba d'aya jikin ta na lullu6e ne da blanket, ajiye wayar yayi kan kujerar kafin ya k'arasa a nutse zuwa wajen gadon, hannu ya saka ya janyo side drawer dake gefe ya matso da ita dab da gadon sannan ya zauna akae, murmushi ne ya su6uce a kyakykyawar fuskar sa sanda yaga tayi juyi seya kasance ta koma kallan inda ya zauna d'in, a hankali ya d'an lumshe idanun sa sannan ya kafe kyakykyawar fuskar ta da kallo, sosae kyawun ta ya sake bayyana da tana baccin, dogayen lashes d'in ta sun kwanta luff luff akan idanun ta, ya shafe wajen minti 3 a haka yana kallan nata sannan ya sake lumshe idanun sa kana ya kwantar da kan sa a gefen gadon. A hankali ya k'arasa kan gadon sannan ya d'an rank'wafa kad'an kana ya shiga hura mata sassanyar iska daga cikin bakin sa akan fuskar ta, dan baya so yayi wani abun daze zama takura a gare ta, a nutse ta shiga bud'e manyan idanun ta sanda taji iskar akan fuskar ta, seda ta gama bud'e idanun nata dae_dae lokacin da ta sauke idanun na ta akan sa, da sauri ta tashi zaune ganin yadda fuskar sa take a dab da ta ta, seda ta tashin sannan ya matsa daga kan gadon, ita kuma taja bargon da take ciki ta sake rufe jikin ta gaba d'aya, murmushin gefen baki ya saki lokaci d'aya yana kae hannun sa kan kwantacciyar sumar kan sa ya shafa, ya lumshe idanun sa yana taune gefen lips d'in sa na k'asa "La'asar tayi.." ya fad'a a hankali bayan ya maeda duban sa kan ta "D'an mik'o min hijab d'ina" ta fad'a ba tare data kalle shi ba tana d'an tura baki, bin inda hijab d'in nata yake yayi da kallo, seya saka hannun sa a hankali ya d'auka sannan ya jefa shi kan kujerar daya ajje wayar sa, itama hijab d'in tabi da kallo kafin ta dawo da kallan ta kan sa idanun ta sunyi rau rau "Don Allah ka bani" ta fad'a har lokacin bata sakko daga kan gadon ba kuma bata cika blanket d'in data rik'e ba, seda ya lumshe ido sannan ya sake zuba mata idanun sa kana yace "Ko inzo in sauko dake ne?" yayi maganar calmly, harara ta jefa masa kamar idanun ta zasu fad'o har seda hakan ya sanya shi yin murmushi me k'ayatarwa, kamar zata yi kuka tace "Ni dae Allah ka bani hijab d'ina sallah fa zan yi" seda ya soma takawa kamar ze hau kan gadon sannan yace "Bari kiga abinda za'ayi.." ya fad'a kamar ze d'aga ta, babu shiri ta saki bargon da sauri ta dirga ta d'ayan 6angaren ta fad'a toilet bayan ta sake murgud'a baki, lumshe idanun sa yayi bayan ta shige band'akin, seya samu kan sa da tuna yadda yaga rigar jikin ta tabi jikin ta ta kwanta sosae ta matuk'ar yi mata kyau, bud'e idanun sa yayi kamin ya fesar da iska daga bakin sa kana ya fice daga d'akin. Be dad'e ba ya dawo dan yana idar da sallah ya taho, sanda ya dawo yayi dae_dae da lokacin da take k'ok'arin fitowa daga cikin toilet d'in, akan sa idanun ta ya fara sauka, da sauri tayi maza taja k'ofar ta koma ciki tana ji kamar ta fasa ihu, kallan inda hijab d'in ta ke ajiye yayi da alama bata d'auka ba, yayi wani murmushi kana ya d'auki hijab d'in ya k'arasa bakin toilet d'in, bece komae ba yayi shiru yana jiran jin ko za tace wani abu, kamar kuwa tasan jira yake se yaji tace cikin er k'aramar muryar ta "D'an ban hijab d'in nan don girman Allah" ta fad'a a shagwa6e tana kwa6e fuska "Gashi" ya fad'a bayan ya matsa jikin k'ofar sosae, seda ta d'an yi jimm kad'an kafin a hankali ta saka hannun ta kan hannun k'ofar ta d'an bud'e ta kad'an, shi kuma ya mik'a mata hijab d'in, seda ta sauke ajiyar zuciya sannan ta saka hannu ta kar6a, kafin ta gama kar6ar ya saka hannun sa d'aya ya tura k'ofar se ganin shi tayi cikin toilet d'in, k'ara ta saki lokaci d'aya tana wara manyan idanun ta, ganin sa da tayi cikin toilet d'in, cikin rashin sanin abin yi kawae ta rungume shi gudun kada ya ganta a yadda take d'aure da d'an k'aramin towel tana fashewa da kuka kawae, wata k'atuwar ajiyar zuciya ya sauke sanda ta fad'a jikin sa d'in, seda ya tafi hutun tak'aetaccen lokaci sannan ya fizgo numfashin sa kana ya sake lumshe idanun sa, a hankali ya fesar da iska daga bakin sa yana shak'ar daddadan k'amshin dake tashi daga jikin ta wanda ya had'u da k'amshin sabulu suka had'u suke bada wani sassanyan k'amshi me dad'in shak'a, hannun sa ya d'aga da nufin d'orawa akan farin gadon bayan ta dan bata damar sake kwanciya cikin jikin sa bayan uwar rungumar data masa, seya jiyo muryar ta cikin rauni tana furta "Ka fita don Allah, ka fita don Allah.." abinda take fad'a kenan ilahirin jikin ta na rawa, bugun da zuciyar ta keyi yana iya jiyo shi saboda yadda jikin ta ke manne da na shi, ba k'aramin gudu yake yi ba, wanda ya had'u da nasa bugun zuciyar da ya chanja tun lokacin da ta rungume shi, sheshshek'ar data cigaba dayi har kuma lokacin tak'i sakin sa kamar ma sake shigewa cikin jikin nasa take yi duk dan kada ya gan ta shine ya sanya shi sakin ajiyar zuciya sannan yace cikin wata shak'ak'k'iyar murya kamar ba tasa ba "Zan fita.." ya fad'a yana k'ok'arin kae hannun sa kan ta, se
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70