Chapter 44
Chapter 44
Rk da tayi, shin ko dae mafarki take yi ne bata sani ba? Tabbas ma babu mamaki mafarkin take yi dan kuwa wannan dae yafi kama da mafarkin. Tana nan zaune bata umm bata umm umm tunda kuma ta zauna ta kasa koda kae ruwa bakin ta ne ballantana akae ga cin abincin da aka dinga dire mata, ita bata ta su take yi ba, abinda kawae take buk'ata yanzu shine ta samu waya ta kira Abban ta ko Yah Sadeeq amma har yanzu bata ga wanda zata iya samun waya a wajen sa ba "Ki zo ana neman ki" wata mata ta fad'a tana kallan ta, da mamaki ta d'aga kae ta kalle ta sannan cikin k'arfin hali ta furta "Don Allah zan iya samun waya a wajen ki?" da mamaki matar ta kalle ta cike da mamakin yadda taji tayi magana dan kuwa ta d'auka bebiya ce, se kawae ta girgiza kae tana cigaba da kallan kyawun Ayrahn da duk da yadda take a firgice hakan be hana shi fitowa ba "Muje koh?" matar ta fad'a tana cigaba da kallan ta, se kawae ta mik'e cikin rashin sanin abinyi tabi bayan matar kamar rak'umi da akala, a soron gidan suka tsaya sannan matar ta kalli Rk dake tsaye jikin bangon soron idanun sa a lumshe kamar me bacci "Don Allah kada ku dad'e, kaga dae da yadda akayi na barka ka shigo gidan nan, da Baba ma ya sani baze bari ba wallahi" "Nagode" ya fad'a yana bin ta da kallo sanda ta koma cikin gidan, wanda Ayrah ta gani ne ya sanya tayi kicin kicin da fuskar ta tana shirin komawa ciki yace a nutse "Batu ne akan auren ki da za'a gabatar gobe" kamar wadda aka tsaeda ta seta dakata tana jin bugun zuciyar ta na k'aruwa, murmushi yayi ganin yaci nasara tunda gashi har ta tsaya, kafin yace komae ta juyo tana kallan sa murya a raunane tace "Bana buk'atar taemakon ka, ban ce ka maeda ni gida ba dan bana buk'atar hakan daga gare ka, abinda nake so kawae shine ka bani aron wayar ka zan kira Abba na na sanar dashi inda nake zezo ya d'auke ni" kallan ta ya cigaba dayi yana jin muryar ta ta dake fita a raunane har cikin kwanyar sa, wani irin tausayin ta mara misaltuwa na ratsa shi amma yasan abinda zeyi, ya furta "Kada kiyi wannan kuskuren, kada ki sake ki kira Abban ki, dan kuwa babu wanda ze yadda dake akan ba guduwa kika yi da kan ki ba, shawara d'aya ni kae na ba dan wani abun zan taemake ki ba se dan kasancewar ki er uwa ta musulma" ya d'an tsagaeta yana jin wani irin ciwo a cikin zuciyar sa wanda har hakan seda ya bayyana a cikin muryar sa da kuma kan fuskar sa sannan ya cigaba da fad'in "Taemako d'aya zan miki shine zan kar6i auren ki a matsayin wadda muke soyayya, sannan a bani ke na tafi da ke zuwa Kano, tun kafin ma mu shiga cikin Kanon zan sawwak'e miki seki tafi gidan ku, kin ga babu wanda ze ji labarin auren idan bake kika fad'a ba.." "Ya ishe ni haka malam, babu ruwan ka da rayuwa ta, na fad'a maka ka fita a rayuwa ta ni da iyaye na, ka bar ni zan auri koma wanene tunda ba zaka bani wayar ta ka bana buk'atar wani taemakon" ta fad'a sanda wasu kyawawan hawaye suka shiga zarya akan kuncin ta, runtse idanun sa yayi daga inda yake tsaye, baya tunanin kome zata yi a yanzu kam ze bata wayar sa tayi kira da ita, bama shi ba koda wani yaga ze bata wayar tayi kira toh ze san yadda zeyi ya hana wannan abin faruwa, kenan a 6ata masa budget? Kae ina hakan baze ta6a faruwa ba "Kina tunanin mutumin daze aure kin ze sake ki kafin ya maeda ki gida? Yana son ki fa, idan da baya son ki baze kawo ki wata uwa duniya a d'aura muku aure ba, ni kuwa fa? Yanzu babu ko d'igon son ki a cikin zuciya ta, dan haka kawae zan aure ki ne dan na taemaka miki ki fita daga hannun wannan mutumin, muna barin k'auyen nan kuma zan rubuta miki takaddar ki da sharad'in ba zaki sake neman inda nake ba" ya k'arasa maganar yana kafe ta da idanun sa masu kyau da kwarjini "Waye ze ne me ka? Tirrr!" ta fad'a tana sake tuna halin mahaefin sa, so take ta tambaye shi toh shi meya kawo shi nan d'in? Amma tasan idan tayi tambayar ze iya tunanin wani abun dan haka tayi shiru tana cigaba da kallan wani wajen, jin da yayi bata sake cewa komae akan zancen sa ba hakan ya alamta masa zata iya amincewa kenan da maganar tasa, lallae ya sake yadda Ayrahn har yanzu yarinya ce, seya saki wani shu'umin murmushi yana shafa bak'in sumar dake shimfid'e akan farar fatar sa da hannun sa kana yace cikin sake karantar yanayin kyakykyawar ta sa "Idan kin amince zamu iya yin hakan a rubuce saboda ki tabbatar da abinda na fad'a gaskiya ne, wato dae ina nufin zamu yi auren yarjejeniyar yini d'aya ne!!" ya fad'a dan cikin ran sa ya shiryawa kowanne irin k'alubale daze biyo bayan auren ta da yayi, baya jin ko d'arr akan abinda ya aekata d'in ko da zasu dawwama ne cikin auren sirri hakan ba damuwar sa bace, dan kuwa daya rasa ta gwara ya jurewa kowanne kalar abu daze tunkaro shi komae zafin sa kuwa... End of ZAZZAFAR KAUNA (CHAPTER ONE) In Sha Allah zamu d'ora da ZAZZAFAR KAUNA (CHAPTER TWO) nan da kwana 2 idan na huta, shima FREE ne duk dan jin dad'in ku 🤗😍 Dan neman qarin bayani se a tuntu6e ni ta 08124818273 https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 031 ___Manyan fararen idanun ta da colour d'in su ya sauya ta d'aga ta zube su a kan sa sanda yake maganar, ta cigaba da saurarar sa tana nazarin kowacce kalma da yake fad'a, sosae k'irjin ta ke mata wani irin suya yana zafi, seta shiga jera ajiyar zuciya kafin ta durk'ushe a wajen tana sakin wani marayan kuka na rashin sanin abinyi, a hankali kukan da take yake fita idanun ta a lumshe haka zalika zuciyar ta na cigaba da zafi, daga inda yake ya runtse idanun sa yana jin kukan nata har cikin jikin sa, seya sauke wata ajiyar zuciya yana d'auke kae daga inda take durk'ushe, ya zama dole ya koyi wofantar da al'amuran ta ko dan saboda wannan kasadar da yake neman aekatawa, idan ba haka ba tabbas ze koma shine me laefin ba wasu ba, duk da yadda kukan nata ke ratsa shi hakan be hana shi sake kicin kicin da fuskar sa ba, ba zaka ta6a gane menene a cikin zuciyar sa ba yadda kyakykyawar fuskar sa take babu annuri se ka d'auka haka ne a cikin ran sa ma, hannayen sa ya d'auka duka ya sak'ale su a k'irjin sa kafin ya d'an lumshe idanun sa kana ya bud'e su yace a hankali "Kuka bashi da amfani, ina ga gwara ki mik'e mu ida wannan aekin" ya d'an
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70