Skip to content

Chapter 56

Chapter 56

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

Sadeeq ya lumshe idanun sa sannan ya fara magana a nutse "Abba, Umma kada 6acin rae yasa ku man ta wacece Ayrah, Abba kada 6acin rae yasa ku aebata d'iyar da kuka haefa, Abba ina ji a jiki na akwae wani 6oyayyen al'amari dake faruwa wanda da zamu bawa Ayrah dama zata fad'e shi, amma Abba bamu bata ba, mun k'i bata wannan damar data nema, Abba Ayrah bata da wayo ko bud'ewar idon da zesa ta bi saurayi!" tashi zaune Abba yayi har lokacin hannun sa na d'ore akan k'irjin sa yace bayan ya girgiza kae "Shin baka ji abinda ta fad'a bane Sadeeq? Tun ina k'ok'arin k'arya ta abinda muke zargi yau Ayrah da kan ta tazo ta tabbatar mana harda k'arin wani abun ma" Abban ya k'arasa fad'a yana kallan Yah Sadeeq "Umma, Abba Ayrah ce fa, Umma Ayrah ce fa, kuna tunanin zata iya zuwa can wani waje tayi aure da wanda bakwa so? Ayrahn da kullum cikin son farin cikin ku take Umma?" shiru dukan su suka yi cikin nazarin abinda Yah Sadeeq d'in ya fad'a, kamar babu wanda ze tanka a cikin su se kuma Umma tace "Ya akayi hakan ta faru kenan Sadeeq? Me kake so ka ce mana? Dukan mu ba'a son ran mu muke zargin Ayrah ba Sadeeq, babu yadda zamu yi ne, mu iyaye ne ta yaya zamu aebata d'iyar mu? Abinda take fad'a yanzu ya zama dole mu shiga rud'ani, ta bar gida bayan maganar hana ta auren yaron nan, yanzu kuma ta dawo tace tana d'auke da auren sa, Sadeeq ya kake so muyi?" seda yaja ajiyar zuciya sannan yace "Umma, Abba don Allah mu bari naje na kira Ayrah tazo ta mana bayani, inaji a jiki na akwae wani abun.." ya fad'a har cikin ran sa yana jin abinda ya fad'a d'in, shiru na wajen minti 2 ya wanzu a wajen kowanne da abinda yake sak'awa a ran sa, se dae dukan su sun gamsu da zancen d'an nasu, a gefe guda kuma dukan su sun so su fahimci kamar sun yi laefi, k'in tsayawa suji abinda ze fito daga bakin Ayrahn, yanke mata hukunci tun kafin su san aenahin abinda ya faru, koma menene ya faru 6acin rae ne "Je ka kira min d'iya ta!" Umma ta fad'a tana kallan Yah Sadeeq lokaci guda kuma tana jin yadda wani nauyi dake k'irjin ta ya d'an ragu, seta saka hannu ta goge hawayen fuskar ta dae_dae lokacin da Yah Sadeeq ya saki murmushi kana ya mik'e yana kallan Abba yace a hankali "Abba in kira ta?" seda Abba ya runtse idanun sa sannan ya bud'e kawae ya jinjina kae, cike da farin ciki ya sanya k'afa ya fice daga cikin gidan yana d'an d'ingishi dan har lokacin k'afar ta sa bata ida warkewa ba. ... Dae_dae lokacin daya fito titi yayi dae_dae da lokacin daya hango Ayrahn cikin motar Rk, yana k'ok'arin k'arasawa wajen motar Rk ya tashi motar ya bar wajen, se yayi sauri ya tsaeda Napep ya sanar dashi yabi masa motar Rk d'in, babu musu me Napep d'in ya bi shi, dae_dae wani waje motar Rk d'in ta dakata wanda yafi kama da Hotel, Yah Sadeeq ya sauka ya biya me Napep d'in kud'in sa sannan ya cigaba da tafiya zuwa wajen motar. Saukowa Rk yayi daga driver seat ya zagaya zuwa wajen me zaman banza ya bud'e k'ofar yana kallan yanda take a cure waje d'aya, yanzu ta dena kukan se dae ita kad'ae tasan abinda take sak'awa a cikin zuciyar ta "Don Allah ki fito!" ya fad'a cikin rarrashi, idan motar da take ciki ta d'aga kae ta kalle shi toh itama ta kalle shi "Ayrah!" Yah Sadeeq ya fad'a sanda ya k'araso dab da motar, da wani irin sauri ta d'aga kan ta ba tare data shirya ba, nan take idanun ta suka sauka akan Yah Sadeeq, seda ta d'an lumshe idanun ta sannan ta bud'e dan tabbatar da Yah Sadeeq d'in ne ba gizo yake mata ba sannan ta sauko daga cikin motar a million ta k'arasa ta fad'a jikin Yah Sadeeq d'in tana sakin wani irin kuka, a hanzarce ya d'aga kan sa ya kalli wanda ta rungume d'in, ko wani be masa bayani ba ya fahimci wanene shi, amma me kuma ya kawo shi nan d'in? Shima Yah Sadeeq d'in rungume ta yayi yana jin yanda take kuka sosae, tana shirin fara magana duk dae cikin kukan yace "Ya isa! Ki bari mu zauna, ina buk'atar jin gaskiyar al'amari, bana son k'arya Ayrah.." kamar wata k'adangaruwa ta shiga jinjina kae har lokacin tak'i sakin sa, d'aga idanun sa yayi ya kalli Rk da har lokacin yake tsaye se dae basu yake kalla ba yace "Raj?" se a lokacin ya juyo ya kalle shi cike da mamakin yadda ya kama sunan sa, seya jinjina kae yana lumshe idanun sa, d'an murmushi kad'an Yah Sadeeq yayi kana ya furta "Sad..." "Sadeeq!" Rk ya k'arasa sunan yana nuna Yah Sadeeq "Ehh" shine abinda Yah Sadeeq ya furta sannan ya d'ago Ayrah dake jikin sa ya rik'e hannayen ta kana yace "Ina son magana da kae idan babu damuwa" "Why not?" Rk ga fad'a bayan ya d'aga kafad'a "Mu k'arasa can.." Rk ya fad'a yana nuna wani d'an madaedaecin waje dake d'auke da wasu kujeru masu kyau, babu wanda ya sake cewa komae cikin su Rk na gaba yayin da Yah Sadeeq ke a bayan sa suka cigaba da tafiya zuwa wajen, ita dae Ayrah babu abinda tace ta cigaba da rik'e hannun yayan ta dan tana ji kamar idan ta sake shi zata bud'e ido taga baya nan, a haka suka k'arasa wajen, Rk ne ya fara neman waje ya zauna sannan Yah Sadeeq ya zauna, ita dae Ayrah ko zaman ma kasawa tayi seda Yah Sadeeq ya kalle ta yace a hankali "Ki zauna kin ji?" kamar bata san da wata halittar a wajen ba taja kujera ta zauna har lokacin idanun ta na kan Yah Sadeeq, shiru Rk yayi kawae yana jiran jin abinda Yah Sadeeq d'in zece, kamar ya sani kuwa seya sauke ajiyar zuciya sannan ya furta "Menene gaskiyar barin Ayrah gida don Allah? Menene gaskiyar auren ka da tace tana d'auke da shi a kan ta?" shiru ya d'an yi yana nazarin tambayar Yah Sadeeq d'in, kamar ba zece komae ba se kuma ya d'an lumshe manyan idanun sa sannan ya bud'e yana tunanin tsayin adadin maganar da zeyi, amma ya zama dole yayi ko dan hakan ze wanke Ayrah daga wajen iyayen ta, sannan kuma su yafe mata koda ze samu kan ta ta dawo asalin Ayrahn sa, a hankali ya shiga labartawa Yah Sadeeq abinda ya faru, duk wani abu daya sani seda ya fad'a masa, yana kaewa k'arshe yayi shiru yana d'an aje numfashi kad'an, shiru Yah Sadeeq yayi tun lokacin da Rk d'in ya fara bashi labari, mamaki, tsoro gami da al'ajabin wannan al'amari yak'i barin sa, ya rasa ma me zece kwata kwata, ya rasa ma wane tunani ya kamata yayi, abin ya bashi tsoro da mamaki aenun, a hankali ya dubi inda Ayrah take zaune duk tayi wani iri da ita kamar ba Ayrah ta asali ba, se yaji wani

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70