Chapter 1
Chapter 1
https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* Page_001 ___K'arfe 7pm ne na daren ranar juma'a, tana zaune kan er kujerar dake gaban mudubin ta hannun ta rik'e da waya er k'arama wadda wasu ke kira da rakani kashi, sassanyan murmushi ke tashi daga kyakykyawar doguwar farar fuskar ta, tana nan zaune har zuwa lokacin da wata mata wadda kana ganin ta kasan mahaefiyar tace, saboda tsananin kama da suke yi, ta yaye labulen d'akin ta lek'o tana kallan ta "AYRAH wae har yanzu jiran Abban kike?" Murmushi ne ya sake wanzuwa akan fuskar wadda aka kira da Ayrahn wanda hakan ya bawa dimple d'in dake gefen kowanne kumatun ta lotsawa sosae sannan tace cikin muryar ta me dad'in saurare "Ehh Umma.." ta6e baki Umma tayi tace "Ae se kiyi ta jira.." daga haka ta saki labulen ta koma tsakar gida. Tana nan zaune bayan wajen minti 10 ta jiyo sallamar mahaefin nata daga tsakar gidan su, seta ajjiye wayar da sauri akan gadon sannan ta mik'e ta yaye labulen d'akin ta fito, hasken farin wata da kuma na k'wan fitilar da suka kunna ya sanya ni ganin kyakykyawar fuskar ta da har zan iya kwatanta muku ita, matsashiya ce er kimanin shekaru 19 doguwa ce fara sosae, me idanu manya manya da dogon siririn hanci, se d'an k'aramin red lips d'in ta, sanye take cikin doguwar riga bak'a babu d'an kwali a kanta dan haka ta yafa mayafin doguwar rigar akan ta "Abba sannu da zuwa.." ta fad'a tana neman waje ta zauna "Yawwah Ayrah" Abban ya fad'a yana neman waje ya zauna sannan da murmushi kan fuskar sa ya sake kallan Ayrahn bayan ya amsa sannu da zuwan da Umma ke masa "Toh in gyara zama dae in sha labarin karatun kin nan, dan da alama akwae magana a bakin ki" murmushi ta sake yi sannan tace "Abba ae tun d'azu kae nake jira nazo muku da wani babban albishir" Umma ta kalli Abba tace "Ahh toh, tun d'azu tak'i fad'a min abinda yake ta sanya ta murmushi tace seka dawo.." Abba ya maeda duban sa kan Ayrah yace "Toh muna jin ki, Allah yasa alkhaeri ne" gyara zama tayi daga inda take zaune sannan ta fara magana har lokacin murmushi yak'i barin kyakykyawar fuskar ta "Abba na had'u da RAJ.." ta fad'a da mad'aukakin murmushi akan fuskar ta, cikin rashin fahimta dukkan su suka kalle ta, seta d'an tsaya itama tana kallan su kafin tace "Raj fa nake nufi, Umma Raj d'ina fa, kun tuna?" ta fad'a tana d'an murmushi dan ita in dae akan Raj ne bata da wata kunya, kallan juna Umma da Abba suka yi kafin Abba ya runtse idanun sa sannan ya fara k'ok'arin magana "Umma cewa yayi ma na fad'a tun wuri Abbun sa zasu zo wajen Abba" Ayrah ta fad'a kafin Abban ya fara magana, Umma dake lura da yanayin Abba ta furta a hankali tana kallan sa sosae "Abban su lafiya dae koh?" jinjina kae yayi kafin cikin er dakiya ya furta "Kina nufin Raj d'an gidan Kabeeru..?" seta jinjina kae cikin jin dad'in yadda Abban ya gane maganar ta ta tace "Ehh Abba, bama mu ta6a tunanin.." d'aga mata hannun da Abba yayi ne ya sanya ta dakatawa daga fad'in maganar da take k'ok'arin fad'a, ta cigaba da kallan yadda lokaci guda k'wayar idanun sa ta sauya, haka zalika Umma ma tak'i kallan ta, seda Abban ya sake runtse idanun sa sannan ya bud'e ya fara fad'in "Kar ki sake min maganar sa ko maganar wanda ya shafi ahalin su gaba d'aya.." Abba ya k'arasa maganar idanun sa na sake yin jawur, cikin rashin fahimta take kallan Abban nasu, ta kuma kalli Umma sannan tace a d'an rud'e "Abba ko dae ka bayar dani ne ga wani bansani ba? Abba cewa nayi fa Raj ke so azo a nemar masa aure na.." "Ayrah..ki tashi ki bar wajen nan idan baso kike zuciya ta ta buga ba" Fararen idanun ta dake d'auke da bak'a sid'ik d'in k'wayar idanu ta d'aga ta sake duban mahaefin nata, take wasu k'walla suka tarar mata tana jin yadda k'irjin ta ke bugawa da k'arfin gaske, "me yake faruwa ne?" ta tambayi kanta "Abba Raj ne fa, Abba Raj dae wanda ka sani fa, akan sa nake magana.." Abba ya runtse idanun sa yana jin wani irin zafi a cikin ransa cikin 6acin rae ya furta "Ki saka a ranki in dae ina raye, har abada ba zaki ta6a auren Suraj ba" da wani irin razana ta d'aga ido ta kalli mahaefin nata, tana jin yadda kalaman nasa ke sauka a cikin kunnuwan ta kamar saukar mashi, kafin takae ga cewa komae ta sake jiyo Abban nata yana fad'in "Ki kawo koma waye a fad'in garin nan gaba d'aya amma dae_dae da minti d'aya kada ki sake ki yaudari kanki kiyi tunanin zan aura miki Raj, bama Raj ba duk wani daya dangance su bazan ta6a aura miki shi ba" kuka ne ya k'wace mata babu k'ak'k'autawa tana jin wani iri a rae da zuciya har ma da gangar jikin ta, a hankali taja k'afafun ta da rarrafe ta k'arasa gaban mahaefin nata ta rik'o k'afafun sa sannan ta fara magana cikin kuka, kyakykyawar fuskar nan ta ta tayi jajir "Abba..ka tausaya min, Abba ka taemakawa zuciya ta, Abba ko da wannan ce zata zama alfarma ta k'arshe da zaka iya yi min a rayuwa Abba kayi min ita don Allah" ta k'arasa fad'a tana sake fashewa da wani sabon kuka, a hankali Abba ya zame k'afafun sa bugun zuciyar sa na k'aruwa ko ba'a gwada shi ba tabbas yasan ciwon sa na dab da tashi, ya d'an runtse idanun sa kad'an sannan ya fara k'ok'arin tafiya, ta sake rik'o k'afafun nasa tana kuka kamar wadda ranta ze fita "Abba ina k'aunar Raj, zuciya ta zata iya bugawa idan kace zaka rabani da shi, Abba kace wani abu don Allah" juyowa Abba yayi yana kallan ta kana a fusace yace "Ko mutuwa zaki yi ba zaki ta6a auren Raj ba.." daga haka ya wuce d'akin sa, mik'ewar da Umma tayi ne ya sanya ta d'ago fuskar ta da tayi jajir tace "Umma ya zaki tafi ki barni cikin duhu, Umma me Raj ya muku da Abba zece bazan aure shi ba, Umma Raj fa ko har yanzu baku gane wanda nake magana akansa ba.. Umma kiyi wa Abba bayani don Allah" ta k'arasa maganar sanda wani kukan yaci k'arfin ta, ko kallan inda take Umma ba tayi ba ta wuce cikin d'akin da Abba ya shiga.. A hankali ta cigaba da rera kukan ta, seda tayi me isarta sannan taja k'afafun ta zuwa cikin d'akin ta har lokacin hawaye yak'i dena sintiri akan kuncin ta, wayar ta dake ajje ta d'akko ta danno wata number ta kira... ... A hankali ya sako k'afafun sa farare tass dake cikin takalmin wanka, seda ya cire su daga k'ofar toilet d'in sannan ya sako kansa zuwa cikin kyakykyawan bedroom d'in, k'arasawa yayi bakin k'aton mudubin sa ya sanya hannu ya d'auki comb ya fara taje sumar kansa data sha gyara sosae, banda ruwan daya ta6a ta a gyara take tsaf se tashin k'amshi me dad'i da take yi, yanayin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70