Skip to content

Chapter 58

Chapter 58

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

lokacin ba wani k'arfi gare shi ba amma saboda wadatar zuci da kuma tausayi irin na sa ya taemaka masa, be tsaya iya nan ba ya taemakawa Abbun sa amma ace abinda Abbun sa yayi kenan? Ya zama dole ya bincika. .. Babu wanda yace uffan a cikin su sanda Yah Sadeeq d'in ya gama bada labarin, Ayrah na taya shi har lokacin tana share k'walla a idanun ta, Abba gaba d'aya bashi da abin cewa shiyasa ma yayi shiru yayin da Umma kuma mamaki gami da takaeci sune suka taru suka mata yawa yasa ta kasa cewa komae, a hankali ta shiga goge hawayen dake ta saukowa daga kan fuskar ta tana girgiza kae, se yanzu ta sake gane kuskuren da suka aekata na yankewa Ayrahn hukunci ba tare da sun yi bincike ba, hannu Umma ta mik'awa Ayrah bayan ta d'aga fuskar ta ta kalle ta, sannan ta mata alama da ta taho da kan ta, babu 6ata lokaci Ayrah ta k'arasa da sauri ta fad'a jikin Umman tana sakin wani irin kuka, itama Umma bata hana kan ta kukan ba ta rungume d'iyar ta ta sosae tana jin yadda ilahirin jikin Ayrahn ke rawa "Kiyi hak'uri Ayrah, don Allah ki yafe min, nice na fara d'arsawa Abban ku zargin guduwa kikayi daga gidan nan bayan tabbatar da ba zamu aura miki Raj ba, kiyi min afuwa Ayrah!" ta k'arasa fad'a tana sake jin wani irin takaeci, se da Ayrah ta sauke sheshshek'a sannan tace "Umma ni ba abinda kuka min, wannan dalilin ne ma yasa nake ta sauri in dawo gida dan nasan za'a iya tunanin hakan, Umma ba kuyi laefi ba dan kun yi tunanin hakan musamman daya kasance a washe garin ranar da kuka hanani auren sa ne kuka neme ni kuka rasa.. Umma ni baku min komae ba, nice ma zan baku hak'uri.." "Kuull..ki bar fad'in mu miki hak'uri Auta, babu abinda kika mana mu ma" Umma ta fad'a tana sakin Ayrahn, bata sake cewa komae ba se k'arasawa da tayi inda Abba ke zaune har lokacin, tsugunawa tayi tana kallan sa, dae_dae lokacin daya d'auke kae yana jin zuciyar sa na karyewa "Abba..!" ta fad'a har lokacin tana kallan sa "Ayrah je ki huta bazan iya cewa komae ba, kiyi hak'uri kawae.." Abban ya fad'a, wani irin sanyi taji yana ratsa kafatanin jikin ta, ko ba komae yau d'in gata ga iyayen ta kuma da alama sun yafe mata, gashi ma har neman yafiyar ta suke yi "Abba ni zan nemi yafiyar ku don Allah.." Abba be iya cewa komae ba se girgiza kae kawae da yake yana ajje numfashi a hankali, Yah Sadeeq kuwa da yake gefe murmushi ne kawae ke fita daga kan fuskar sa, tana shirin mik'ewa dan komawa d'aki Abba ya juyo kamar wanda ya tuna wani abu "Ayrah!" seta juyo a hankali tace "Na'am Abba.." "Kin san mutumin daya saka aka d'auke ki?" tsayawa tayi tayi shiru tana hasaso fuskar Alhaji Mato, kwata kwata ba zata iya cewa ga fuskar sa ba dan haka ta girgiza kae kamin tace "A'ah Abba bansan shi ba.." "Idan kika gan shi zaki gane shi?" shiru tayi tana nazari, ko da ta san shi ma bata tunanin zata iya gane shi ballantana bata san shi ba dan haka a nutse ta furta "A'ah Abba.." "Tashi kije Allah yayi miki albarka" lumshe idanu tayi kamin ta mik'e tare suka wuce cikin d'akin ta ita da Umma, shiru Abba yayi bayan barin su wajen yana nazari, ya zama dole ya gano mutumin daya d'auke masa yarinya ya kae ta wani waje dan a d'aura musu aure, idan kuma ya tuna da maganar auren Raj dake kan er tasa se ya sake jin jikin sa yayi sanyi, a yanzu be san wanene Raj d'in ba be san ko halin su d'aya da mahaefin sa ba, be san yadda za'ayi su kasance sirikae tsakanin sa da Kabeeru ba, abinda be ta6a tunanin ze kasance a rayuwar su ba, abinda ya guda tun farko, se dae gashi Allah yayi ikon sa akan su ta hanyar da basu ta6a zata ba, seya koma ya jingina bayan sa da jikin bango yana cigaba da sak'a da warwara. ... Da sallama ya shigo cikin d'akin hannun sa d'auke da envelope, Mummy dake zaune kan kujera ta mik'e tana fad'in "Alhaji sannu da zuwa" "Yawwah sannu kadae, ina Muneerahn? Na gan ki ke d'aya?" murmushi Umma tayi sannan tace "Toh Alhaji ae dole ka ganni ni d'aya a kwanakin nan, kasan sha'anin amarya fa yanzu haka tana wajen gyaran jiki" "Toh madallah, ga kati dae ya iso" ya fad'a yana mik'a mata envelope d'in hannun sa, da sauri ta sanya hannu ta kar6a da murmushi kan fuskar ta take fad'in "Kae toh Masha Allah.." ta fad'a tana k'arasawa ta zauna kan kujera ta fara fito da katinan masu kyau da k'ayatarwa, girgiza kae Daddy yayi yana murmushi ganin yadda Mummyn ta shagala da kallan kati, ko bi ta kansa ba tayi ba hakan ne ya sanya shi jan k'afafun sa ya bar d'akin. Be dad'e da fita ba Muneerah ta shigo cikin d'akin cikin hijab har k'asa hannun ta d'auke da jaka da had'ad'd'iyar wayar ta, k'arasawa tayi da sauri kan kujerar tana kallan Mummy kamin ta saka hannu ta tu6e hijab d'in jikin ta, nan take shigar dake jikin ta ta bayyana, gajeran wando tiet ne a jikin ta da vest irin me bin jikin nan hakan ne ya bayyana yanda ta cika daga sama ba kamar da ba wanda ke nuni da siyo shi ba natural bane, haka zalika hips d'in ta ma sun k'aru ba kamar da ba dake kamar 1, kan ta babu d'an kwali se dae kamar ko yaushe a kitse yake da kitson attachment daya zuba a gadon bayan ta, ta k'ara wani irin mahaukacin fari bauu, fatar nan ta sake d'ashewa, da alama ba mae ta shafa ba se dae ko k'waya ko kuma allura "Kin dawo?" "Ehh Mummy, na gaji wallahi" "Toh sannun ki, gashi nan kati ya iso" farr tayi da idanun ta kafin ta kalli katinan, seta saka hannu ta d'auki guda d'aya ta kalla ta shiga karantawa, sunan ta ne gashi nan ya fito 6aro 6aro dana Rk, wani murmushi ya k'wace mata tana jin ita kam burin ta ya gama cika daga lokacin data auri Rk d'in, ajiye katin tayi seta d'auki wayar data ajje a gefen ta kamar koda yaushe ta danno number sa, amsar d'aya ce dae kamar kullum baya kusa, bata gaji ba ta sake kira amma har ta katse be d'aga ba, a karo na 3 ta sake gwada kiran na sa cikin sa'a kuwa ya d'aga wayar se dae bece komae ba, daga inda take ta maraeraece fuska kamar za tayi kuka "Haba Baby, ina ta kiran ka amma kak'i d'agawa, na maka magana ta whatsApp kak'i kula ni, ya kake so nayi? Auren mu saura kwanaki amma kak'i tsayawa muyi magana ko da akan shirye_shiryen bikin ne" tsaki ya saki akan la66an sa, ya kasa gane wannan dalilin na had'a auren sa da Muneerah, idan so suke zumuncin su ya d'ore ae ba dole seta hakan zasu biyo ba, shi abinda ma yake

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70