Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

tunda Allah yasa min albarka a wannan harkar na koma cikin kano ko da zama ko da sana'a, kin san kano cibiyar kasuwanci ce.." d'an shiru Umma tayi tana nazarin maganar Abban se kuma can tace "Hakan ma yayi Abban su, me son cigaban ka ae me k'aunar ka ne, ni ina ganin kawae ka amince da shawarar tasa.." "Toh shikenan amma batun zama fa? Acan d'in zamu zauna ko kuma dae in fara maganar ni kad'ae na tafi can sena dinga zuwa?" Abba ya fad'a yana Kallan Umma, murmurshi Umma tayi kana tace "Abban su ni bana tunanin wannan mafita ce, ni a gani na gwara ka tsayar da hankalin ka kan abu guda d'aya, ba kae kana can mu muna nan ba hankalin ka ze rabu gida biyu, ni a gani na kawae muma mu tafi tare da kae.." "Shikenan toh Allah ya taemake mu" Abba ya fad'a yana murmurshi. Be hak'ura haka ba seda ya nemi Abbu yayi shawara dashi, cikin ikon Allah kuma shima ya bashi goyon baya d'ari bisa d'ari, dan haka Abba ya sake jin nutsuwa a lamarin, saboda haka babu 6ata lokaci ya fara shirye shiryen tafiya kanon, ita kanta Umma ma ba'a barta a baya ba, shiri take yi na tafiyar ta su, dan haka babu 6ata lokaci Abban ya kusa gama komae, da yake Alhaji Mato yafi zama a kano ya saka shi ya nemar masa gida a cikin garin na Kano d'an madaedaeci haka me kyau, beyi k'asa a gwuiwa ba wajen tambayar Abbu yadda za'ayi, ze bishi can garin kanon ne ko kuwa anan ze zauna se Abban ya dinga yi masa aeke, girgiza kae yayi a lokacin da Abban ke masa maganar yace "Ayyah Abban Sadeeq, ya za'ayi in zauna anan kae kana can wani gari? In Sha Allah zan bika can d'in idan yaso sena dinga dawowa nan d'in wajen iyali na" Take Abba yayi na'am da maganar Abbun, dan haka yace "Toh shikenan, Allah ya taemake mu" "Ameen Ameen" Abbu ya fad'a.. Rana ku suka cigaba da tafiya babu tsayawa, har zuwa sanda Abba ya k'arasa abinda be gama ba, yanzu haka ya siyar da kayayyakin da yake siyarwa anan d'in ya had'e kud'ad'en nasa waje guda, be sanya su a banki ba saboda matsalar da account d'in sa ya samu, hakan ne yasa ya had'a su cikin wata jaka daban wadda yake ajje muhimman takardun sa masu matuk'ar amfani, duk wani abu da yasan yana da amfani a wajen sa ya had'e su duka cikin wannan jakar sannan ya had'a ragowar kayan sa cikin wata, haka zalika Umma ma tayi sallama da mak'ota en uwa da abokan arzik'i, ranar da zasu koma zuwa garin kano tazo... Tun safe Umma ta gama shiryawa tsaff cikin atamfa riga da zani da hijab dogo, ta shirya Ayrah cikin doguwar rigar en kanti da baby hijab suka fito parlour, tun d'azu Ayrahn ke ta 6ata rae da alama k'iris take jira ta fashe da kuka dan haka Umman na kallan ta tak'i kula ta ballantana ma ta sakar mata kukan shagwa6ar ta ta, tana zaune kan kujerar ta kwantar da kanta akan wata leda dake d'auke da kaya, Yah Sadeeq ne ya shigo cikin d'akin idanun sa akan ta ya fara sauka, shima yana ganin ta yasan yau da rigima ta tashi "Auta meya faru?" ya fad'a yana kallan ta, manyan idanun ta ta d'aga ta kalle shi amma ba tace komae ba, Umma dake kallan su tace k'asa k'asa "Ka rabu da ita don Allah, kar kasa ta mana kuka kuma" yaji abinda Umman ta fad'a dan haka kawae seya koma kusa da Ayrahn ya zauna, seta maeda kanta ta kwantar akan cinyar sa tana cigaba da kallan k'ofa.. Basufi mintuna 2 da zama ba sega sallama daga k'ofar d'akin, Umma da Yah Sadeeq suka amsa sallamar, yana sanye cikin riga da wando na wani yadi me kyau kasancewar sa me tsafta ya sanya kayan nasa a goge suke tsaff tsaff yayi matuk'ar kyau, da gudu ta mik'e ta k'arasa bakin k'ofar da suke k'ok'arin shigowa ta rungume shi tana sakin dariya kamar ba itace yanzu zaune kamar zata yi kuka ba, shima dariyar yayi yana fad'in "Oyoyo Ayrah" ta sake yin dariya kana tace "Ina ta jiran ka, shine ba kazo ba" dukka en d'akin binsu suke da kallo, ya rik'o mata hannu zuwa cikin d'akin yace "Gani fa nazo" "Zo kaji" ta fad'a tana janyo shi k'asa, seya d'an yo k'asan, ta sake jan shi ya tsuguna a k'asan sannan ta kae bakin ta kunnen sa tace k'asa k'asa "Jiya wata tace suna da mangoro a gidan su, zaka ciro min?" bud'e idanu yayi yana sake kallan en d'akin sannan ya mik'e ya sake kama hannun ta zuwa cikin d'akin, ita kuma ta tura d'an k'aramin bakin ta gaba, seda suka k'arasa ya zauna sannan ya gaeda Umma da suke gaesawa da Ummee sannan ya kalli Ayrah dake zaune dab dashi ta rik'o hannun sa kamar wanda ze gudu yace "Toh zan raka ki yi murmurshi" se a lokacin ta saki fuskar ta tana jin dad'i har cikin ranta. Basu dad'e da zama ba Yah Sadeeq daya fita d'azun yazo yace Umma su fito, har lokacin hannun ta na cikin na Raj sanda suka fito d'in, Ummee ta kalli Abba tace "Toh Alhaji mun gode Allah ya saka da alkhaeri, ya tsare ya bada sa'a" "Ameen Ameen" Abba ya fad'a yana shirin d'aukar jakar da Yah Sadeeq ya fito da ita a hannun sa, Abbu yayi murmurshi yana kallan Abba yace "Haba haba Alhaji ina wajen sannan zaka d'auki kaya?" shima Abban murmurshi yayi sannan yace "A'ah toh ka bar Sadeeq ya d'auka.." "Babu komae muje kawae" ya fad'a yana rik'e wata akwati kuma a hannun sa, Abba be sake cewa komae ba se kallan Ayrah da yayi wadda ta kwantar da kanta a hannun Raj yace "Toh taho koh?" mak'ale kafad'a tayi tana sake cuno baki gami da sake rik'e hannun Raj, Abba ya sauke ajiyar zuciya sannan yace cikin rarrashi bayan ya matsa dab da ita ya kamo d'ayan hannun ta "Ki taho mu tafi kinji, zamu dawo ae" "A'ah" ta sake fad'a tana kuma mak'ale kafad'a, Umma dake gefe ta d'an lumshe idanun ta kad'an ta bud'e kana ta matsa kusa da Ayrahn tace "Taho kinji, ae zaki dinga zuwa Uhmm?" girgiza kae ta shiga yi sosae k'wallar data dad'e a idanun ta ta shiga sakkowa babu k'ak'k'autawa, shi kam Raj gaba d'aya ma ya kasa kallan ta dan zuciyar sa ta riga ta dad'e da gama karyewa, Yah Sadeeq ne ya k'araso a hankali ya rik'o hannun Ayrahn dake cigaba da girgiza kae yace cikin rarrashi "Ki taho mana kinji" ya fad'a yana janyo ta, a hankali hannun nata dake rik'e da nasa ya shiga zamowa daga sama zuwa k'asa har zuwa sanda ya zama tafin hannun su ne kawae cikin na juna, Raj ya rik'e hannun nata sosae yana kallan k'wayar idanun ta dake cigaba da zubar da hawaye, Yah Sadeeq be kalle su ba ya jata ya d'auke ta kawae a hannun sa, abinda ya sanya hannun su rabuwa dana juna kenan kuma dae_dae lokacin da Ayrah ta saki kuka

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70