Skip to content

Chapter 42

Chapter 42

Zazzafar Kauna Book One Complete Hausa Novels 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

ta6a ganin Ayrah ta fita babu izinin wani a cikin mu? Abban su yau nayi nadama.." "Ya isa haka Ruk'ayyah" Abba ya fad'a yana d'aga mata hannu "Bar ta taje, in dae bijirewa umarnin iyaye ne taje gata ga duniyar, kada muyi mata baki saboda ni uba ne ke kuma uwa ce kada ya kama ta, amma ni kae na yau Ayrah ta wulak'antani a rayuwa.." kallan su kawae Yah Sadeeq yake yi ya kasa cewa komae, ya kasa koda bud'e bakin sa ne ya furta wani abu, dan maganar ta shige shi, bashi da bakin da ze iya k'arya ta wannan maganar ko kuma ya musa, toh idan ya musa d'in mene hujjar sa ta yin hakan? Meze kawo a matsayin hujjar sa? Amma meyasa Ayrah zata yi haka? Meyasa zata za6i d'a namiji akan iyayen su? Iyayen da suka d'auke ta tun ciki har tazo duniya suna d'awaeniya da ita har kawo yanzun basu gaji ba? Duk wani tunanin su akan ta ne, duk wani burin su akan ta, meyasa zata saka musu ta hanyar za6ar wanda ta had'u dashi rana tsaka a rayuwar ta? Ta fifita d'a namiji akan su??. ... Yana cikin motar har lokacin idanun sa na kan gidan yana tunanin yadda zeyi ya shiga cikin gidan, idan ya tuna maza ne har biyu suka d'auki Ayrahn suka shigar da ita cikin gida se yaji wani sabon tuk'uk'i da kuma wani zafi na cigaba da azalzalar sa cikin zuciya, seya bud'e murfin motar a hankali ya zuro k'afar sa dake cikin wani had'ad'd'en takalmi hannun sa akan goshin sa yana d'an murzawa, daga ganin mutanen da suka d'auke ta kasan sanya su akayi, kuma gidan da suka kawo ta babu alamar akwae mutum a ciki, kenan idan haka ne ogan nasu ze zo kuma ze nemi a bud'e masa k'ofar dan shiga gidan "Exactly" ya fad'a yana sake bud'e idanun sa, seda ya fesar da wata zazzafar iska daga bakin sa sannan ya cigaba da zama cikin motar har lokacin gaba d'aya hankalin sa na kan gidan gefe guda kuma yana jiran yaga ta inda wani ze 6ullo. ... Zubewa yayi a gaban me garin yana d'aga hannun sa alamar girmamawa "Allah ya taemake ka yalla6ae" wani matashi da zeyi 25 years ya fad'a kan sa a k'asa, me garin bece komae ba ya cigaba da kallan Mubarak yana jiran jin abinda ze fad'a "Yalla6ae acan gidan Alhaji Mato naga wasu bak'in fuska sun shiga gidan, ban ta6a ganin su ba kuma naga kamar basu da gaskiya" Mubarak ya fad'a har lokacin kan sa na a k'asa, seda me gari ya d'an numfasa sannan yace "Gidan Alhaji Mato?" Me gari ya fad'a, Mubarak ya sake jinjina kae kana yace "K'warae kuwa yalla6ae nima nayi mamaki" d'an shiru Me garin yayi sannan yace "Aje a zo min dasu" ya fad'a a nutse "An gama ranka ya dad'e" Mubarak ya fad'a yana mik'ewa ya bar wajen. ... Suna zaune a tsakar gidan Muttala ya kalli wanda suke tare yace "Kodae mu fito da ita, kada zafi ya mata illah" "A'ah mu k'yale ta, mu dae ba aekin da aka saka mu ba kenan? Ina ruwan mu? Gwara kawae mu jira yazo shi yasan yadda za'ayi da ita" jinjina kae Muttala yayi kana yace "Hakane kuma" babu wanda ya k'ara cewa komae a cikin su har zuwa sanda suka ji ana knocking k'ofar, da mamaki dukan su suka yi shiru suna saurarar knocking d'in sa ake dan tabbatarwa "Wallahi da gaske k'wank'wasawa akeyi, waye kenan?" "Ko dae Alhajin ne ya iso?" mutumin ya tambaya yana kallan Muttala, girgiza kae Muttala yayi kafin yace "No bana tunanin haka gaskiya, idan shine ae akwae mukulli a hannun sa" Muttala yayi maganar yana mik'ewa a hankali ya k'arasa dab da gate d'in sannan yace "Wanene?" Mubarak ne yace "Daga gidan Me gari ne, me gidan yana nan?" se Muttala ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "A'ah be iso ba tukun" "Toh Me gari na neman ku" Mubarak ya sake fad'a, kallan juna Muttala suka yi shida mutumin nan sannan Muttala ya d'aga kafad'a kafin a hankali ya furta "Babu wata matsala fa" jin abinda ya fad'a ne ya sanya mutumin k'arasawa ya bud'e gate d'in sannan suka fara k'ok'arin fitowa daga cikin gidan "Ku kad'ae ne a cikin gidan?" Mubarak ya sake tambaya, mutumin nan na shirin cewa "Ehh" Muttala ya girgiza kae da sauri kana yace "A'ah akwae matar Oga amma bacci take" "A taso ta itama ta fito, Me gari ke neman ku ku duka" had'iye yawu Muttala yayi kana ya koma cikin gidan ya k'arasa ya bud'e motar cikin tunanin yadda za'ayi ta farka saboda abinda suka shak'a mata, cikin sa'a seya hango wani ruwa wanda d'azun ya sha ya ajje ragowar, da sauri ya janyo kana ya bud'e ya fara zuba mata a fuska, seda ya kusa juye mata ruwan sannan ta fara bud'e dara daran idanun ta da suka sake komawa ciki saboda wahala, a hankali ta dinga bud'e su har ta gama ware su tarr cikin motar, idanun ta suka sauka akan Muttala, da sauri ta mik'e ta fara komawa baya tana shirin sakin k'ara Muttala ya girgiza mata kae da sauri yana d'ora hannun sa akan bakin sa sannan yace a hankali ganin yadda ta gama rikicewa gaba d'aya "Kada kice komae, kiyi shiru taemakon ki zan yi" yayi maganar har lokacin yana kallan ta, cigaba da girgiza kae tayi hannun ta d'ore akan bakin ta hawaye se sintiri suke akan fuskar ta "Ki dena kukan taemakon ki zan yi fa" ya sake fad'a ganin kamar bata ji abinda ya fad'a da farko ba "Kiyi shiru kada ki nuna a tsorace kike kin ji, ko me kuma za'a ce miki kada kice komae, komae kika ji an fad'a ke dae ki bisu a haka" ya fad'a a nutse dan gudun kada ta tona musu asiri a gaban jama'a, haka kawae taji tayi na'am da zancen mutumin dan haka seta jinjina kae sannan yace "Fito muje" babu musu ta sanya k'afa ta fito se dae har lokacin k'irjin ta be bar bugawa ba haka zalika tana mamakin ko nan d'in ina ne? Waye ya kawo ta? Yaushe suka zo? Ya akayi suka zo nan d'in? Su waye su? Meyasa suka kawo ta nan d'in? Amma koma dae menene tunda wannan mutumin ze taemaka mata bari ta zubawa sarautar Allah ido, seta sake bud'e idanun ta tana kallan gidan sanda Muttala ke fad'in "Yawwah ga ta" Mubarak ya kalle ta sannan yace "Toh ku wuce muje" babu musu duka suka fito daga gidan sannan suka kulle, tafiya take a hankali kamar wata mara laka tana cigaba da kallan garin da be mata kama da birni ba, ji take kamar ta saka kuka amma idan ta tuna abinda mutumin ya fad'a seta d'an lumshe idanun ta ta had'iye hawayen. Tunda suka fito idanun sa ke kan su, seya saki wata k'atuwar ajiyar sanda ya hange ta ta fito daga cikin gidan tana tafiya cikin k'oshin lafiya "Thank god" ya fad'a yana fitowa daga cikin motar gaba d'aya, seda suka kusa zuwa gidan Me garin yana hango su sannan yabi bayan su cike da tunanin inda zasu je

Table of Contents

Chapters

70 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70